Mecece Private Number, Yadda Ake Kira da Ita Da Cire Private Number

Private Number

Yau kuma za mu yi cikakken fahimtaccen bayani game da private number, yadda ake kira da ita da kuma yadda ake cire private number da yadda ake gano boyayyiyar number da aka kiraka ta private number cikin sauki ba tare da an sha wahala ba.

Mutane da dama na da sarar kiran lambobi ta hanyar sakaya tasu lambar (privatizing their number) sai dai mutum yaga an kirashi amma babu asalin lambar da aka kira shi.

{tocify} $=title{Abubuwan Dake Ciki}

An matukar cigaba a fasahance yadda har ta kai ta kawo kai tsaye za ka iya fito da lambar wanda ya kiraka da private number kafin ka daga kiran ko ma manhaja (application) ya nuna maka ainihin lambar take.

Wasu na sanya wayoyinsu ne a tsarin private number ba tare da saninsu ba, walau yayin shige-shigen inda basu sani ba ko kuma sun bai wa wasu sun shigar musu ba tare da saninsu ba.

Yayin da ‘yan damfara da masu ci-da-gumin-wasu da kuma kiriminals ke amfani da ita (private number) wurin yin aika-aika.

Labari Labari (Story Story)

Domin in ba zan manta ba, akwai wani bawan Allah da cikin dare ya ga an kirashi ta private number, yana dagawa aka zungura masa ashar, aka kuma yi ikirarin sai an kashe shi.

Bawan Allahn nan ya kasa tsugun, ya ci alwashin ko nawa zai salwantar sai ya tabbatar da an gano wanda ya kira shi ya yi masa barazanar kisan nan.

Ilemun-ilemun kuwa sai gashi a police station, ya cike korafi, aka hada shi da jami’i sai kamfanin MTN Nigeria, ma’aikata suka binciko wanda ya kirashi, aka basu asalin lambar.

Bugawar da za su yi kuwa sai aka daga, to, a lokacin wanda ya daga wayar ba tashi ba ce a wurin mai ita ya karba, bai san ciki ba ya bada adireshin inda yake, sai ga jami’ai sun zo gareshi su ka yi ram da shi.

Also Read: Latest NCC-approved MTN, Airtel, Glo, and 9mobile 2023 USSD Codes

Da jin abinda ya auku, sai yace shi Allanfir waya ta wane ce, dazu ya karbeta, aka yi wa wancan kofar rago aka kame shi. 

In dai takaice maka labari, wanda ya yi barazanar sai da ya yi asarar sama da 100k sakamakon wannan barazanar kisa da ya yi wa mutumin nan kuma sai da ya yi kwanan bayan kanta.

Karin wani abin al’ajabi shi ne; mutumin fa na kauye ne!

Saboda muhimmancin lamarin nan da izinin Allah Madaukakin Sarki abinda za mu tattauna akansa a cikin wannan rubutun blog din.

Mecece Private Number

Lambar boye wani tsarin saiti ne da ake saitawa a cikin waya bangaren saitin layi wanda ke bai wa mutum damar kiran wata lambar ba tare da an ga asalin lambarsa ba, madadin haka sai dai a ga “hidden number”.

Lokuta da dama in dai mutum ya san waya ya kuma jina yana rike da ita, ya san cikinta to ba ya da bukatar shiga cikin settings domin boye lambarsa.

Kawai wasu lambobi zai latsa da farko kafin ya kira lambarka take za ka ga kira ta boyayyiyar lama.

Yadda Ake Kira ta Private Number

Akwai hanyoyi akalla biyu da ake bi wurin yin kira ta lambar boye, su kuwa wadannan hanyoyi sun hadar da:

Kira Private Number da USSD Code

Ta hanyar amfani da USSD code za ku iya kiran duk lambar da kuke so ta private ba tare da wanda ku ka kira ya ga lambarku ba.

Domin yin hakan sai ku latsa #31# sannan ku rubuta lambar mutum ta biyo bayan #31# din kana ku kira.

Ga dai yadda abin yake a aikace.

 • Bude phone app din wayarka
 • Ka latsa #31# sai lambar wanda kake son kira ta biyo baya
 • Misali #31#091482xxx sai ka kira
 • Kiran yana shiga wanda ka kira din kai tsaye zai ga kira ya shigo masa ta private number.

Zan so ka kula, ka kuma sani cewa da yiwuwar asirin lambarka ya tonu kai har ma da sunanka muddin mutum yana amfani da manhajar truecaller ko ya latsa wadansu USSD Codes kafin ya daga wayar taka.

Kira ta  Private Number ta Phone App

Hanya ta biyu wacce za ka bi domin mayar da lambarka private ta cikin settings a wayoyin keypad ko kuma android ga ta za mu kawo ta.

 • A wayarka ‘yan dangwale, ka shiga “Phone” app, inda kake saka kati ko kuma kake saka lambar mutum ka yi kira
 • Sai ka duba inda aka saka “More” ko kuma wasu digo uku a tsaye “” ka latsa
 • Daga nan sai ka shiga “Settings
 • Zai baka zabin call settings options, to ka bude “Call Settings
 • A shafi na gaba sai ka zabi layinka ka latsa akan sunansa (MTN-NG ko AIRTEL-NG)
 • Ka bude “Additional Settings
 • Sai ka duba inda aka saka “Caller ID” sannan ka cike zabin “Hide number” domin boye lambarka kai tsaye.

Kira ta Private Number ta Waya Keypad

Ka biyo wadannan matakan domin ka mai da lambarka private ko kuma ka cire ta daga private number ta cikin karamar wayarka.

 • Kunna wayarka sannan ka shiga cikin “Menu
 • Daga nan ka duba “Settings” ka shiga ciki
 • A cikin settings sai ka bude “Call Settings
 • Ka duba sosai za ka ga inda aka saka “Hide ID” to ka shiga ciki
 • In kana son mai da lambarka private kai tsaye, sai ka cike zabin “Hide ID” sannan ka yi save.
 • In kuma tana cikin private number ne kana son cireta sai ka cike zabin “Display ID by Network” ko “Display own ID”.

Yadda Ake Cire Number Daga Private Number

Babu wata sahihiyar hanyar cire waya daga cikin private ko hidden number sama da wacce za mu kawo.

In har kana fama da irin wannan matsala to ka kwantar da hankalinka domin yanzu haka kakarka ta yanke saka.

Sai ka koya:

 • A wayarka ka shiga “Phone” app
 • Sai ka duba inda aka saka “More” ko kuma wasu digo uku a tsaye “:” ka latsa
 • Daga nan sai ka shiga “Settings
 • Zai baka zabin call settings options, to ka bude “Call Settings
 • A shafi na gaba sai ka zabi layinka ka latsa akan sunansa (MTN-NG ko AIRTEL-NG)
 • Ka bude “Additional Settings
 • Sai ka duba inda aka saka “Caller ID” sannan ka cike zabin “Show number” ko “Network Default” domin bayyanar da lambarka.

In kuma da karamar waya ka ke amfani sai ka yi haka:

 • Kai tsaye ka bude menu sannan ka shiga “Settings
 • Ka bude “Call settings
 • Daga nan ka bude “Hide ID
 • Sai ka cike “Display own ID” ko kuma “Display ID by network”.

Shi kenan an gama, ka cire lambarka daga private number.

Yadda Zaka Gano Boyayyar Number ko Hidden Number

Duk mai amfani da manajar “Truecaller” to ba ya da bukatar bata lokaci domin koyon yadda zai gano boyayyiyar lambar da aka kira shi da ita.

To, amma ai ance shi ilimi kogi ne, kuma shi kogi ba zai ki dadi ba don haka babu laifi in an kara ilimi kan ilimi.

Truecaller yana bayyana bayanan duk wanda ya kira ka da boyayyiyar numba, to ka ga ba stress kenan.

Amma ga wadanda ba sa amfani da truecaller, sai ku biyo wadannan matakan domin gano wanda ya kika ku da private number.

 • Ana kiranka da private number kawai ka daga.
 • Kana dagawa sai ka latsa alamar keypad wato wurin da ke da alamar gidan lambobi
 • Yana budewa sai ka latsa *#*#0686#*#*
 • Kana kammala latsawa zai dawo da kai fuskar kiran, kuma take za ka ga sunan mutumin da ya kiraka ta private in akwai lambarsa a jerin contacts dinka, in babu kuma za ka ga lambar.
 • In kana so, sai ka yi screenshot daga baya ka kira shi, ka ji me ke tafe da shi.

Madallah, yanzu kam ina da yakinin in dai wasu sirrika kake bukatar sani game da private number to kana kammala bibiyar rubutun blog din nan za ka san komai.

Kammalawa

Yau, na yi muku bayani gamsasshe akan private number, yadda ake kira da ita, da yadda ake cire lamba daga private kai har ma da yadda ake gano lambar da ta kira ta private number.

Ina fatan Allah ya shige mana gaba, ya kuma sa ku amfani duk abinda ke cikin wannan rubutun blog.

A karshe, Allah ya kara wa Annabi (S.A.W) daraja.

Previous News Next News