Fusatattun Matasa Sun Binne Wani Tsoho da Ransa Saboda Maita a Jihar Benue

SP Catherine Anene
SP Catherine Anene

An birne wani dattijo da rai bisa zargin maita da wasu matasa suka yi masa a unguwar Ikyve da ke karamar hukumar Konshisha a jihar Binuwai.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne a karshen mako a unguwar Ikyve da ke Diiv-Ikyurave, wani yanki na karkara da ke iyaka da jihar Cross River.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa matsala ta fara ne ga tsoho da aka bayyana sunansa da Ihwakaa lokacin da tsawar damina ta kashe dansa Henry tare da matarsa da jaririyarsu.

Mazauna yankin ya ci gaba da cewa wasu matasa a yankin sun yi zargin cewa aikin Ihwakaa ne, wanda a kullum suke zargin yana suna amfani da ruwan damina wajen cinye mutanen yankin.

“Saboda haka, suka kama shi kuma suka binne shi a wani kabari mara zurfi," in ji mazaunin.

Wani mazaunin unguwar, Engr. Baba Agan, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa ya samu labarin a ranar Lahadin da ta gabata cewa, tsawa ta kashe mutane uku a unguwarsu.

Agan ya ci gaba da cewa, ya kara samun labarin cewa ana zargin wani dattijo ne da laifin kitsa kashe mutanen uku, lamarin da ya kai ga wasu gungun fusatattun mutane suka binne shi da rai.

Ya ce guguwar tsawa ta zama ruwan dare gama gari a yankin kuma ta yiwu ta yi sanadiyyar mutuwar mijin da matar da jaririnsu dan wata biyu.

Agan, wani dattijo a yankin, ya ce abin takaici ne kafin ‘yan sanda su isa wurin domin ceto rayuwar wanda aka binne din ya mutu kuma a karshe aka tono gawarsa.

“Ban ji dadi ba. Kada mutane su dauki doka a hannunsu. Idan ba a kula da wannan al'amari yadda ya kamata ba, zai iya haifar da Ζ™arin rikici a cikin iyali da al'umma. A matsayina na dattijo, zan bi sahun sauran shugabannin al’umma don ganin an warware wannan batu cikin ruwan sanyi,” in ji Agan.

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta kara da cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargi.

“An binne wani dattijo da rai saboda ana zargin wani matashi da matarsa da yaronsa dan watanni biyu sun mutu sakamakon walkiya. An yi zargin cewa maita dattijon ne ya kawo walkiyar. Suka je suka binne shi da rai ya mutu. 'Yan sanda suna bincike; mun riga mun kama mutane biyu,” in ji Anene.

Previous News Next News