Abin ya Zama Gasa: Shi ma Gwamnan Taraba, Ishaku ya Roki Yafiyar Mutanen Jiharsa

Gov Darius Ishaku
Gov Darius Ishaku

Gwamna Darius Dickson Ishaku ya nemi afuwar mutanen Taraba wadanda watakila ya cizgunawa a gwamnatinsa ta shekaru takwas.

Ishaku ya ba da uzurin nasa ne a yayin taron godiya da kungiyar kiristoci ta kasa reshen jihar Taraba ta shirya a sakatariyar CAN da ke Jalingo.

Gwamnan ya ce ya yi farin ciki da yadda littafinsa na “Give Me Peace and I will Give You Development” ya samu gindin zama a zukatan ’yan Taraba inda ya bukaci jama’a da su bar ruhanayyar zaman lafiya da soyayya da gafara ya jagoranci halayensu da ayyukansu da kuma dangantaka da ƴan uwansu.

Ishaku dai ya taba yin hidimar godiya ta musamman ta Easter a Cocin Anglican Mayo Dasa da ke Jalingo inda ya durkusa a gaban jama’a tare da neman gafarar duk wani laifi da ya aikata a tsawon shekaru takwas da ya yi yana gwamnan jihar.

“A matsayina na shugaban da ya shafe kusan shekaru takwas yana jan ragamar jihar nan, mai yiyuwa ne na yi wa mutane da dama laifi ko dai da sanina ko kuma cikin rashin sani a dalilin gudanar da ayyuka na a matsayina na mai zartarwa” inji shi.

Ishaku ya bayyana cewa Littafi Mai Tsarki ya ce ya fito fili ya nemi gafara tare da neman afuwa ga wadanda watakila ya yi wa laifi.

“A cikin Littafi Mai Tsarki, an koya mana mu gafarta wa waɗanda suka yi mana laifi. A wannan yanayin, ina roƙon waɗanda na yi wa laifi su gafarta mini. Na yi haka ne a dakin Allah, idan kuma ba su yafe min ba, tsakanin su da Allah ne,” inji shi.

Gwamnan mai barin gado ya yi godiya ga Allah da ya ba shi hikimar yi wa al’ummar jihar hidima yadda ya kamata duk da kalubalen da gwamnatinsa ta fuskanta.

Sai dai ya bukaci al’ummar jihar da su bai wa magajinsa Laftanar Kanar Kefas Agbu (Rtd) goyon baya da hadin kai domin samun nasara.

Wannan dai shi ne karo na biyu da gwamnan zai je gaban wata jama’a domin neman gafarar ‘yan siyasa da al’ummar Taraba a bainar jama’a kan batutuwa da wuraren da zai iya bata musu rai.

A makon da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma roki ‘yan Najeriya da watakila ya yi wa laifi su yafe masa.

Mako guda kafin Buhari ya nemi jama’a, Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ya kuma nemi jama’a su gafarta masa.

Previous News Next News