Yadda Ake Zaman Tahiya da Karatun Tahiya

Zaman Tahiya

Duk da kasancewata ba wani malami ba, amma yau cikin yardar Allah zan yi dogo kuma zuzzurfan bincike game da zaman tahira kuma na yi mana bayaninsa a saukake, kana na kawo karatun da ake yi yayinsa.

Abu ne mai kyau mutum Musulmi ya sani kuma ya koyi karatun zaman tahiya domin yinsa yayin da yake gabatar da bauta.

Karatun Tahiya

Attahiyaatu lillahi

Alzaakiyaatu lillahi

Addayyibaatu salawaatu lillahi

Assalamu alaika

Ayyuhan nabiyu

Wa rahmatul laahi

Wa barakatuhu

Assalaamu alainaa

Wa alaa ibaadillahii saalihina

Ash’hadu an la’ilaha illallahu

Wahdahu laa sharika lahu

Wa ash’hadu anna muhamman abduhu wa rasuluhu.

Kaji iyakar karatun da ake yi yayin zaman tahiya. Yanzu kuma za mu ‘dan kara nutsawa can ciki domin kara yi muku warwarare zare da abawa akan zaman tahiya.

Bayani Akan Karatun Tahiya a Sallah

Ga duk wanda Allah (S.W.T) ya bai wa damar bin jam’i hadi da samun cikakkiyar sallah, to tabbas ya sani sallah na kunshe da nau’in zaman tahiya har guda biyu.

Also Read: Yadda Ake Karatun Sujjadar Sallah (Bayani Dalla-Dalla)

Bugu da kari, zaman tahira da kuma karatunta sunnah ne (shi ko in aka ce sunnah to ya bambanta da farilla kuma amfaninsa ba karami ba ne a sallah).

Tahiya ta Farko

Ita ce tahiyar da mutum zai yi bayan kammala raka’a biyun farko na sallah Azahar, La’asar, Magriba, da Isha’i.

Ita ko Sallar Asubahi zaman tahiya daya ake yi mata sakamakon raka’o’i biyu gareta, haka ma sallar Juma’a (babbar rana).

To, a tahiya ta farko ana son masallaci ya takaita karance-karancen da yake son yi zuwa karatun tahiya kawai.

Ma’ana; yayin da liman ya yi zaman farko, kawai ka karanta lafazin tahiya da muka wallafa a saman rubutun nan, shi kadai ma ya wadatar da yardar Allah.

Tahiya ta Biyu

Ita ce tahiyar da ake gabatarwa ta karshe a sallah, daga ita da sauran salatuttuka da addu’o’i sai kuma a yi sallama.

Zan so mai karatu ya yi sani cewa a zaman tahiya na biyu, zai iya yin karatun tahiyarsa, sai ya yi wa Annabi (S.A.W) salati da shi da alayensa da kuma addu’o’in neman tsari da Dajjal, wuta ga wanda Allah ya bai wa ikon haddacesu.

Imam Maliki ya tafi akan cewa in ka yi wa Annab (S.A.W) salati bayan karatun tahiyarsa to hakan ma ya wadatar ko da kuwa baka hado da alayensa ba.

Shi ko Imam Shafi’i ya tafi akan cewa, wajibi ne yayin zaman tahiya ta biyu, bayan ka yi karatun tahiya ka yi wa Annabi (S.A.W) salati da shi da alayensa.

Ko ma dai wanne ka yi, walau Annabi (S.A.W) kadai ka yi wa salati ko kumaka hada da alayensa duka daidai ne domin Allah ne masanin daidai.

Sallama Farali Ne

Ina da yakinin duk wani cikakken musulmi ya san farali ko in ce FARILLA, wato abinda ya ke wajibi, in ko babu shi to lallai aiki zai baci.

Ina son mai karatu ya yi sani cewa, sallama a sallah farali (farilla) ne, haka kuma zaman da za ka yi na gwargwadon fitar lafazin sallamar (assalamu alaikum) shi ma farilla ne.

Kaga kuwa in ko haka ne, baya kyautuwa da liman ya ce Assalamu Alaikum kawai mutum ya mike ya kade bujensa ya fice daga masallaci.

Son samu mutum ya zauna daidai gwargwado har lafazin sallamar ya fita.

Allah dai shi ne masani.

Kammalawa

Hakika babu abin bautawa da gaskiya face Sarki Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata abisa shugabanmu, jagabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W). Ina tawassali da kyawawan tsarkakan sunayen Allah 99 wurin miko muku wannan 'dan tatsitsin aiki wanda ina fatan zai taimaki mabukata.

Previous News Next News