Yadda Ake Karatun Sujjadar Sallah (Bayani Dalla-Dalla)

Sujjadar Sallah

Ba zan fara darsa yatsana domin yin rubutu game da Addinin Musulunci ba face sai na sauke nauyi na sanar da ‘dan‘uwa makaranci cewa; ni ban kasance malamin addini ba face daya daga cikinku ahalussunnah masu bincike.

Saboda haka kusan duk abinda zan rubuta yanzu haka, na zakuloshi ne daga sassa dabam-daban, walau daga odiyo, bidiyo ko rubutun yanar gizo ko littafi.

Da fatan mun fahimta.

Yau da yardar Allah zan yi bayani ne akan karatun sujjadar sallah domin sallah na da muhimmanci kwarai a cikin Addinin Musulunci.

Also Read: Yadda Ake Zaman Tahiya da Karatun Tahiya

Tana daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar, wato kalmar shahada, sallah, azumi, zakka da kuma aikin hajji (amma fa ga wanda Allah ya hore wa).

Bisa wannan dalili, yana da kyau mutum musulmi ya koyi karatun sujjadar sallah da kuma ‘yan addu’o’in da ake yi duk cikin sujjadar.

Kuma zan so yi mana tuni da cewa, babu wani wanda ake yi wa sujjada im ba Allah ba, ko a wanne irin hali kake ka nemi taimakon Allah, zai kawo maka agaji.

Kazalika masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, tambaya mabudin ilimi kuma shi matambayi ba ya bata.

Insha Allahu kai ma ba za ka bata ba.

Karatun Sujjadar Sallah

Yanzu zan kawo muku karatun sujjadar sallah a transliteration dinsa, wato a latin aphabet yadda kowa zai iya karantawa da wanda ya san Arabic da wanda ya san boko.

Yayin da ka kai hannayenka kasa, sai kuma gwuiwoyinka su biyo baya sannan sai goshinka. Amma bai kyautuwa ka rinka sujjada mai kama da zaman rakumi, wato gwuiwoyinka su riga hannunka taba kasa.

Sai ka karanta

Subhana rabbiyal-a'la. ( sau 3) 

Ko

Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi (sau 3)

Sannan sai ka yi ‘yan addu’o’in da suka sauwaka, bi ma’ana wadanda ka sani sannan sai ka hada da sauran bukatunka ka roki mahaliccinmu.

Allah ya kara wa Annabi Daraja.

Previous News Next News