Tarihin Alhaji Aliko Dangote (Salsala, Haihuwa, Ilimi da Kasuwancinsa)

Alhaji Aliko Dangote

Yau dauke muke da tarihin sanannen dan kasuwar nan na jihar Kano wanda kaf Afirika yanzu haka babu wani dan kasuwa da ya kai shi arziki a shekarar nan ta 2023.

Kafin kuma na fara baku tarihin wannan bawan Allah wanda fitaccen marubucin nan, Maje Ahmad Gwangwazo, ya yi da ‘dan uwansa Alhaji Umaru Muhammad Dangote a shekarar 2007.

Sannan mun kara da sabbin bayanai musamman na kasuwancinsa da kuma na iyalansa.

{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}

Da fatan za ku amfana ta hanyar karanta fitaccen dan kasuwar nan na Najeriya, zan kuma so ku yi wa Malam Maje Ahmad Gwangwazo addu’ar neman rahamar ubangiji.

Salsala

Alhaji Aliko dan Muhammadu dan Gote dan Aliyu dukkaninsu Fulanin Kura ne.

Garin Kura yanzu haka shi ne hedikwatar Karamar Hukumar Kura ta jihar Kano, Najeriya.

Iyalinsa

Alhaji Aliko Dangote yanzu haka ba shi da aure, amma a baya ya yi aurarraki. Kuma yana da ‘ya‘ya mata uku kamar haka

  • Hajiya Mariya
  • Hajiya Fatima
  • Hajiya Halima.

Ilimi

Kakansa ne na wajen Uwa Alhaji Sunusi Dantata, ya yaye shi, da ya dauko shi sai ya dankawa Hajiya Ammani shakikiyar Mahaifiyarsa ita ta reneshi sai da ya girma sannan ya san cewa Hajiya Mariya ce ta haife shi.

Da ya isa zuwa makaranta Alhaji Sunusi ya sa shi a makaranta Islamiyya, ta Ulumuddeen Islamiyya, inda ya yi karatun AlKur’ani hade da na fikihu, an sa shi yana dan shekara biyar da haihuwa a duniya.

Daga nan aka sa shi a makarantar Boko mai suna “Dantata Memorial Primary School” ta gidan Alhaji Amadu Dantata, bayan nan ya yi Kuka Primary School.

Daga nan ya zana jarrabawar tafiya gaba da Firamare inda ya samu nasarar cin jarrabawarsa ya tafi “Government College Birnin Kudu.”

Kafin ya kammala wannan makaranta ta Birnin Kudu, sai Kakansa Alhaji Sunusi Dantata ya cire shi shi da dan’uwansa mai suna Alhaji Nasiru Sunusi Dantata, wanda yake dan Alhaji Sunusi ne.

Kasuwanci

Alhaji Aliko Dangote ya fara harkar kasuwanci da gidan bulo, inda ya cire su daga wannan makaranta sai Alhaji Sunusi ya bude musu wannan gidan bulo a Kurnar Asabe, suka ci gaba da harkokinsu na buga bulosu sayar har suka kai matsayin da suka tara jari mai dan kauri.

Wannan ita ce sana’ar Alhaji Aliko Dangote ta farko. Amma fa a zuciyaraa ya fi son ya yi karatu, kasancewar hakan sai Alhaji Aliko ya je ya samu dan’uwansa, yayansa mai suna Alhaji Umar Gote, ya shaida masa abinda yake ciki cewa ya fi so ya yi karatu.

Nan Alhaji Umaru Gote ya je ya samu kakan Aliko Dangote na wajen uwa Alhaji Sunusi, ya shaida masa cewa ya ji abinda ya faru, saboda haka me zai hana a bar shi ya karasa karatunsa, nan take Alhaji Sunusi kakan Alhaji Aliko Dangote ya ba shi amsa da cewa “Da Kasuwanci muka budi ido”.

Alhaji Aliko suka ci gaba da kasuwancinsu na gidan bulo, shi da Alhaji Nasiru, wanda daga baya suka kara da mota tifa tasu ta kansu, wadda ke yi musu jigilar daukar yashi, idan sun dauko yashi suna kawo wa gidan bulonsu su zuba, ragowar kuwa ana sayarwa da masu bukata.

Bayan nan sai Alhaji Aliko Dangote ya fadada harkar kasuwancinsa da kwangilar gini, inda ya fara da gina makarantar Primary a garin Takai, Karamar Hukumar Dawakin Kudu.

Bayan nan sai ya gina makarantun firamare na (U.P.E) a Karamar Hukumar Birnin Kudu.

Daga nan sai ya samu kwangilar gina wani bangare na gidajen gajiyayyu na Mariri.

Da kammala wannan gine-gine a wajen shekara ta 1972 Miladiyya, sai ya koma Lega inda ya shiga harkar kasuwancin sai da siminti a karkashin kawunsa mai suna Alhaji Usman Dantata wanda aka fi sani da suna “A Makkah”.

Yana zamansa a Legas ya rika odar manyan motoci daga kasar Amurka, inda ya samu wani dan lokaci mai tsawo yana kan wannan harka ta shigo da motoci.

Bayan nan sai Alhaji Aliko Dangote, a shekara ta 1983 Miladiyya, ya koma shigo da kayayyaki irin su; Sukari da shinkafa da fulawa da kifi da tayoyi da batira, bayan shigo da kayayyaki kuma yana fitar da kayayyaki kamar su; Koko da Karo da Kashu.

Kuma ya shiga gina masana’antu inda ya gina masakar M.T.N a Ikeja, ya sayi hannun jari mafi rinjaye a wannan kamfani na jihohin kasar yarabawa.

Daga nan sai ya sayi wani hannun jari a kamfanin gishiri na tarayyar Najeriya a Ogun State (Ota), wanda yanzu wannan kamfani ya zama mallakarsa.

Sannan tarihi ya bayyana mana cewa Alhaji Aliko Dangote ya kafa bankin kasuwanci mai suna “Liberty Merchant Bank” wanda daga baya ya sai da shi.

Daga nan ya sayi hannun jari mafi yawa a Bankin Gamji Bank na tsohuwar Jihar Sakkwato, wanda yanzu ita ce Jihar Zamfara da Birnin Kebbi.

Sannan ya bude kamfaninsa na kansa na Siminti a Fatakwal da Legas mai suna “Dangote Cement”.

Sannan ya kafa kamfanonin fulawa a Kano da Kalaba (Calabar) wanda ake kira “Dangote Flour”.

Bayan nan sai ya kafa Kamfanin Taliya da yin Buhunhuna a Legas kuma duk suna nan suna aiki.

Sai bangaren sufuri, wanda a yanzu a kalla za a samu Tireloli guda dubu biyu a shekarar 2007, amma yanzu haka a shekarar 2023 akalla Dangote na da Tireloli sama da dubu goma sha  biyu (12,000).

Kuma Alhaji Aliko Dangote ya mallaki jirgin ruwa ruwa wanda ke harkokin zirga-zirga kasashe.

Bayan nan Alhaji Aliko ya kafa babban kamfanin hako siminti a Abijanta Jihar Kogi, wanda suke nika shi su sa shi a buhu wato “Packaging”.

A takaice Alhaji Aliko Dangote yana da abubuwan kasuwanci da dama wadanda ba za su lissafu ba, sai dai idan tarihinsa za a yi cikakke.

Kuma wannan baiwa da Allah (S.W.T) ya yi wa Alhaji Aliko Dangote, ta zama alkhairi da alfahari ga mutan jihar Kano da kasa da Afirka da ma duniya baki daya, domin duk inda ka sani iya iliminka a Najeriya duk dan kasa yana amfana da kayan kamfanin “DANGOTE” imma ta abinci ko ta sha ko na girki ko bangaren gini, ba shakka wannan ludufi ne ga al’umma.

Kuma ko ba komai ya zamewa duk wani dan Arewa katanga ga al’ummar kudu.

Hadimai

Ba lallai bane mutanen da za mu lissafo sunayen har yanzu suna cikin hadiman Alhaji Aliko Dangote, amma dai har yanzu wasu suna nan suna yi masa hidima duk da cewa, tafiya ta riga da ta lula.

Alhaji Aliko Dangote yana da masu taimaka masa wajen tafi da harkokin kasuwancinsa, wadanda suka hada da kannensa wato Alhaji Sani Dangote (Vice President) da Marigayi Alhaji Bello Dangote (wanda har gobe Dangote yana jin rasuwarsa) da ‘ya‘yan shakikiyar mahaifiyarsa, Alhaji Abdu Dantata da Alhaji Abdumannanu.

Haka akwai jigajigai irin su Mr. Olakunle Alake da Alhaji Abdulkadir Musa Sidi da Mr. Haman Obel da Alhaji Ahmed Shehu Yakasai da Mr. Essang da Alhaji Aminu Dikko da Mr. Taiye T. Ajiyen da Alhaji Shehu Bello da Mr. Tunde Mbagunje da Alhaji Abdu Ibrahim da Alhaji Salisu A. Calabar da Alhaji Abdullahi Direba da Alhaji Abdu Yaro da Mr. Smith da Mr. Knut O. Da Mr. Suleiman Olarinde da Alh. Yahaya Fufure da Alhaji Maitama Yusuf da sauransu duk su ne suke dauke da amanar kamfanonisa a wanca lokaci (2007).

Wasu suna tare, wasu kuma ba sa tare.

Abokai

Kuma yana da abokai wadanda ko da yaushe za ka gan su tare, su ne kamar su; Alhaji Bala da Mr. Benga da Mr. Sam Uwajokwu da Alhaji Malam Dala da Marigayi Alhaji Waziri Muhammad da sauransu.

Za ta iya yiwuwa wasu daga cikin wadannan abokai nasa sakamakon juyin-juya halin rasuwa sun rasu ko kuma abotar ta yi baya.

Biyayyar Iyaye

Alhaji Aliko Dangote ya kasance mutum ne mai biyayya kwarai da gaske musamman ga mahaifiyarsa duk abin da zai yi sai da yardar mahaifiyarsa, don haka kullum cikin sa masa albarka take.

Yana bin mahaifiyarsa sau da kafa, sakamakon wannan biyayya shi ma ya samu masu binsa sau da kafa wato kannensa Alhaji Sani Dangote da Alhaji Bello Dangote dukkaninsu masu kasaitaccen arziki ne amma ba sa jin wani abu sai abin da Alhaji Aliko Dangote ya sa. Suna matukar biyayya a gare shi.

Kuma yana biyayya ga ‘yan’uwan iyayensa baki daya, yana kuma girmama yayyensa da abokan yayyensa baki daya.

Hajiya Mariya mahaifiyar Alhaji Aliko Dangote, ta kasance mai yawan hidima ga gajiyayyu, mai yawan hidima ga al’umma, mai taimakon Musulmi da Addinin Musulunci.

Yawan wadannan ayyukan alkhairi nata ya sa gabas da yamma, kudu da arewa cikin birnin Kano da kewayenta da ma kauyukanta an san Hajiya Mariya a kan taimako, musamman marasa lafiya da ke kwance a asibitoci, da ci da marayu da ci da makarantun Alkur’ani sun hada da wadanda mutane ke gani da ma wadanda ba’a gani, ba kuma wanda zai san ta yi.

To duk wadannan ayyukan alkhairi da Hajiya ke yi, tana sa Alhaji Aliko Dangote ya dauki nauyinsu, don zaburar da shi da kara dora shi bisa al’amuran alkhairi.

Hadiman da aka dora akan wadannan manyan al’amura basa gajiya, bacci ne kawai ke raba su da mikawa.

Haka duk wadannan ayyukan alkhairi don Allah take yinsu, domin abin da mutum ya ke yi don Allah shi ya ke dorewa, sabaninsa kuwa baya dorewa, kuma dan adam kadai ke yabawa, amma na Allah kuwa, ubangijin sammai da kassai na madallah da su.

Kuma tarihi ya bayyana mana cewa Alhaji Aliko Dangote yana rike da ‘yan‘uwa wadanda su ke li’abbai da dukkan wadanda suka hada iyaye da kakanni daya na bangaren uba ko bangaren uwa duk ya rike su yana kulawa da su.

Haka zalika yayyensa duk ya rike tamkar shi ya haife su.

Previous News Next News