Yanzu Zababben ‘Dan Majalissa Jiha, Dr Nuhu Clerk Ya Rasu a Borno

Dr. Nuhu Clerk

Tsohon kwamishinan yaki da fatara na jihar Borno kuma zababben dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Chibok, Dokta Nuhu Clark, ya rasu a kasar Indiya bayan ya sha fama da rashin lafiya.

A cewar wata majiya daga iyalansa, ya shafe watanni yana kwance a asibiti kafin ya rasu a yammacin ranar Talata a Indiya.

Karanta Kuma: Gwamna Zulum ya Kaddamar da Aikin Gina Gadar Sama ta Biyu a Maiduguri Akan Naira N5.8bn

Tare da cikakken biyayya ga ikon Allah, ina sanar da majalisar jiha rasuwar Hon. Dr. Nuhu Clark, dattijo ga shugabar mu Mrs. Ladi Clark. Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a yau a Indiya, inda yake karbar magani,” inji majiyar.

Har zuwa rasuwarsa, ya taba zama shugaban karamar hukumar Chibok, kuma kwamishina a ma’aikatar yaki da fatara, kuma zababben mamba mai wakiltar mazabar karamar hukumar Chibok, a majalisar dokokin jihar Borno.

Previous News Next News