Gwamna Zulum ya Kaddamar da Aikin Gina Gadar Sama ta Biyu a Maiduguri Akan Naira N5.8bn

 

Babagana Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya kaddamar da aikin gina sabuwar gadar sama mai tsawon mita 600 a tashar Borno Express a Maiduguri ranar Asabar.

Aikin wanda shi ne irinsa na biyu a Maiduguri zai ci Naira biliyan 5.8.

Gwamnan ya ce gadar za ta kara rage cunkoson ababen hawa a yankin tare da kara samar da ababen more rayuwa a babban birnin jihar.

“Gwamnati za ta tabbatar da fitar da kudaden aikin cikin gaggawa.

"Muna umurtar dan kwangilar da ya tabbatar da kyakkyawan aiki yayin da muka kuduri aniyar samar da karin ribar dimokuradiyya ga mutanen Borno a wa'adin mu na biyu," in ji Mista Zulum.

Borno ta ba da kwangilar gina gadar ga wani kamfanin kasar Sin wanda ake sa ran kammala aikin kafin karshen shekarar 2023.

Previous News Next News