Yadda Zaka Sace Zuciyar Budurwa da Yadda Zaki Sace Zuciyar Namiji

Sace Zuciyar Budurwa

Soyayya ruwan zuma ce, wai aka ce in ka sha ka ba masoyi. Ga dukkan alamu yau karatun namu ta kan masoya ya biyo saboda haka sai ku gyara zama ku saurari me ke tafe da mu.

Kafin mu fara da komai muna yi muku maraba da zuwa shafin SeeyBlog.

Kuma yau za mu tattauna ne a kan yadda za ka sace zuciyar budurwaka hadi da baku wasu shawarwari game da hakan.

Mai karatu zan so ka sani cewa; ita da budurwa in ka tsaya jin kunya, tsoro, ko noke-noken yi mata magana to fa haka za ka yi ta ganinta tana wucewa ba tare da ka yi nasarar furta abinda ke kunshe cikin zuciyarka ba.

Shi yasa in dai soyayya kake son farawa to ka tattaro dukkanin karfin halinka, da confidence dinka domin tunkarar abar kaunarka.

Wadansu mutanen na tunanin iya wanka, kudi ko tsantsara lafazi ke sa mace ta so su.

Amma ni a tunanina gaskiya masu irin wannan tunanin to sun saba lamba.

Idan Kana So Budurwa Ta So Ka So Na Gani Kasheni

 1. Kada ka zama mai noke-noke, yawan kunya ko kauyanci a gabanta. Alaji kawai ka saki jikinka ka maganceta cikin confidence da tabbatar mata da eh kai fa namiji ne ba watta shakkarta da kake. Domin mata da yawa na bala’in son namiji mai matukar karfin hali da isa da izza da nuna ko shi wanene a gaban ko wanene. Kuma duk budurwar da ka nuna mata kai fa kunyar yin magana kake da ita kake, ko magana da itan ma wahala ya ke baka, ko kana yi bakinka na rawa, to daga nan za ta raina maka wayo ne maimakon taji tana sonka.
 2. Duk saurayin da ke bai wa macen da ya ke so damar furta abinda ke zuciyarta kuma ya saurara ba tare da katse mata hanzari ba, to wannan cikin sauki zai kame zuciyar budurwar tasa.Saboda haka kada ka zama a cikin sahun mazajen nan da mace sai dai ka yi ta zuba tana binka eh eh eh. Gaskiya mata na tsoron auren irin wadannan mazajen.
 3. Idan budurwarka ta yi abun kwarai, malam yaba mata. In ko ta yi abinda ya ke kuskure, to ana son ka gyara mata kuskurenta cikin mutuntawa, nasiha, hikima da girmamawa.
 4. In ko budurwarka ta cancara tare da dandasa kwalliya da ado kada ka tsaya wata-wata, kawai ka yaba. Hakan zai sa ta ji ta kara sonka da kaunarka.
 5. In ka fahimci babynka na cikin damuwa, ko cikin wani yanayi na rashin jin dadi, kada ka ji komai. Ka lallemta ta fada ma damuwar, ka kuma bata amintacciyar shawara, hakan zai kara mata sonka.
 6. Kuma a matsayinka na dan soyayya, zai fi kyau, ka rinka kiran babynka da sabon suna irin my heart, sweety, one love, ko kuma ka kawata sunan nata in Zainab ake kiranta to ka na kiranta da Zeey Baby.
 7. Kada ka je mata da karya in har da gaske sonta kake, kuma aurenta za ka yi. Ka fito mata a mutum, ka kuma saki jiki da ita ka sakar mata fuska a yi wasa da dariya.
 8. In ko ta yi wani abu da ya sosa maka rai matuka. Kawai ka kirata ka fada mata. Ka kuma bayyana mata kai ya wuce a wurinka, ka marairaice irin please baby ki gyara nan gaba.

Wasu Abubuwa Goma Da Zaki Mallake Zuciyar Masoyinki Dasu

To, mun juyo bangaren sistoci wato mata iyayen gida kuma iyayen biki har ila yau baya goya al’umma.

Soyayya na iya yin farat daya ta shiga cikin zuciyar mutum walau mace ko namiji, amma fa samun damar mallake zuciyar wanda aka kamu da so sai an yi da gaske hadi da wasu aiyuka.

Yadda Zaka Sace Zuciyar Namiji

arat daya soyayya zai iya shiga mutum. Amma kuma samun damar mallakar wannan zuciyar da ake so sai an hada da wasu aiyukan.

 1. Matakin farko na mamaye zuciyar masoyi ita ce; kada ki kira sunan masoyinka garan-gatsan. Saboda maza na son su ji babynsu ta sanya musu wani suna don hakan na sanya su alfahari da ita. Bisa wannan dalili ina mai shawartarki da ki samu suna mai dadi ki saka wa masoyinki.
 2. Duk rashin darajarki da rashin mutunci ki faka su a gefe, a duk lokacin da za ki hadi da mai sonki da aure kada ki kunce kullin faggon rashin mutuncinki.
 3. Kada ki yi shagar banda har mai sonki da aure ya gani. Mu maza muna da kishin abinda za mu aura matuka.
 4. Girmamawa na da matukar tasiri wajen kara narkar da zuciyar masoyinki. Ki rinka girmama shi. Domin namiji mai hankali bai burin auren macen da ba ta ganin girmansa.
 5. In ya bukaci ku yi shawarwari akan wasu abubuwan kafin ku yi aure, ki natsu ku shawarta abubuwa ki bada naki gudummarwar kuma irin positive din nan daidai da tunanki.
 6. Dakikiyar budurwace kadai ba ta yi wa saurayinta kyauta ko babu yawa. Kamar yadda kike son namiji ya kyautata miki to shi ma haka yake so, amma fa ban ce ki bashi kyautar durinki ya taushe tun kafin aure ba. Kada ki sheke aya ki ce a shafin SeeyBlog kika gani.
 7. Kada ki cika bani-bani, domin ba kowanne namiji ke son auren mace mai bani-bani ba tun tana budurwa. In ya fahimci kin cika bani-bani to abinda zai kawo a ransa shi ne; ko da bayan aure ma haka za ki cigaba da uzzura masa da bani babu. Daga nan sai ki ga ya fece dare daya.
 8. Duk munin saurayinki in har ya yi kwalliya yana so ko ba yawa ki yaba masa ita. Ki irin zuga shi din nan, ki koda shi yadda ya kamata. Idan kina yi wa namiji haka to ina da tabbacin zai matukar kware miki.
 9. Ba fa iya maza ba, shi kansa Allah (S.W.T) na son a gode masa, sai ya kara wa mutum. Duk kankantar kyautar da masoyinki ya yi miki, kada ki ji komai ki gode masa. Gobe in mai yawa ta samu da gudunsa zai zo ya kawo miki.
 10. A karshe kuma zan horeki da sakin fuska hadi da yin raha a duk lokacin da kuke tare da namijin da zai aureki.

Tambayoyi Masu Alaka

Yadda zaka sace zuciyar budurwa, yadda zaka sace zuciyar mace, yadda zaka sace zuciyar budurwarka, yadda zaka sace zuciyar namiji, yadda zaka sace zuciyar karamar yarinya, yadda zaka sace zuciyar budurwa a haduwar farko, yadda zaka sace zuciyar saurayim yadda zaka sace zuciyar yarinya, yadda zaka sace zuciyar budurwa cikin sauki.

Previous News Next News