Maganin Ulcer Sadidan, na Har Abada, na Musulunci da na Hausa

Da fari dai marabanku da zuwa shafin nan mai albarka na SeeyBlog.

Yau, da yardar mai duka za mu kawo muku nau’ika iri-iri na maganin ulcer, tun daga kan na asibiti, na gargajiya, na musulunci da da sauransu.

Sai dai, zai fi kyau in har ba ka yi wa cutar olsa karatun ta natsu ba, ka fahimceta, ka kuma fahimci alamominta, da kuma abubuwan da ya kamata a kiyaya ba to ka karanta, “Ciwon ulcer, alamomin ciwon ulcer, da hanyoyin magance ciwon” domin kara wa kanka ilimi.

A kula: ba mu muka samar da ko daya daga cikin magungunan da za mu kawo muku ba, illa iyaka dai, muna da yakinin za su amfaneku. Da fatan za su amfaneku kuma za ku yi mana addu’a.

Maganin Ulcer Sadidan

Domin hada wannan maganin da muka fara fara kawo wa, sai ku nemi wadannan mahadan;

  • Garin habbatussauda cokali 10
  • Da garin tafarnuwa cokali 10
  • Sai garin girfa cokali 1
  • Da kuma zuma lita 1 da rabi.

Yadda Ake Hada Shi

Da farko dai bayan kun samu dukkanin garrukan da muka lissafto, sai ku zuba su a mazubi guda walau roba, kwano, ko tasa. 

Sa’annan ku kawo wannan zuman naku ku kela a kan garin maganin nan, sai ku saka yatsanku ko cokali ku cakuda sosai.

Sai ku rinka shan cokali daya da safe kafin ku ci komai, sannan ku sha cokali daya da daddare in za ku kwanta.

Kun ga in aka hada lissafi kullum cokali biyu za ku sha kenan. Za ku yi ta haka har sai kun ji kun samu waraka, ko kuma ku yi na tsawon sati biyu ko wata guda.

Allah ya sa a dace.

Maganin Ulcer na Har Abada

Garin bincike-bincikenmu muka yi karo da wannan maganin na ulcer, kuma ga dukkan alamu zai taimaki duk wanda ke fama da nau’in cutar nan mai tokare kirji.

To, amma akwai abubuwan da ake bukata;

  • Ganyen zogale
  • Zuma

Yadda Ake Hada Shi

A samu ganyen zogalen nan, sai a dafa shi bayan ya tafasa ya tafarfasu, sai a sauke shi, a tace ruwan.

Daga nan sai a debi zuman a zuba a cikin ruwan zogalen (fatan za ku samo zuma mai kyau da yawa) a rinka sha kofi biyu a rana har zuwa kwana bakwai ko abinda ya sauwaka.

Da yardar Allah za a samu waraka.

Maganin Ulcer na Hausa

Mun samo akalla nau’i-nau’in magungunan ulcer sun zarta kala goma. Saboda haka ga su nan a jere.

Maganin Ulcer na Daya

Wannan shi ne maganin ciwon olsa na daya daga cikin wadanda za mu kawo, kuma ‘yan‘uwanku daga sassa daban-daban na kasar Hausa su suka bada magungunan nan, ba kuma rokarsu kudi aka yi ba, sun yi haka ne domin taimakonku.

Ku nemi;

  • ‘Ya‘yan bagaruwa
  • Madara peak ta ruwa

Yadda Ake Hada Shi

Ka samu ‘ya‘yan bagaruwarka sai ka shanyasu su bushe sannan sai ka daka ‘ya‘yan. Bayan sun zama gari sai ka samu madara peak ta ruwa ka zuba a cikin garin ka rinka sha kullum.

Amma fa baya da dadin sha sai kun daure. Ku gwada yin haka har na tsawon sati biyu insha Allahu za ku ga canji.

Maganin Ulcer na Biyu

Shi kansa wannan maganin na ciwon olsa na Hausa wanda za mu bayar, bashi da dadin sha, amma muna fatan zai muku magani.

Ku nemi;

  • Garin kuka
  • Danyen kwai

Yadda Ake Hada Shi

Ka nemi garin kuka sai ka zuba a cikin mazubi sannan ka kawo danyen kwai ka fasa ka zuba ruwan a kansa ka gauraya sai ka sha.

Ka rinka yin haka har zuwa tsayin mako guda zuwa biyu, da yardar Allah za ka ga sauyi za a samu sauki.

Allah shi taimaka.

Maganin Ulcer na Uku

Ga nau’in magani na uku nan na olsa mun kawo muku, shi ma ana bukatar wasu abubuwa ;

  • Garin rumman (wanda a turance ake kiransa Pomegranate)
  • Garin Zolage (wanda a turance ake kiransa Moringa)
  • Zuma

Yadda Ake Hada Shi

Ku samo garin rumman cokali biyar sai garin zogale cokali biyar, daga nan sai ku hada su wuri guda ku gauraya su.

Sai ku debi rabin cokali daga cikin gaurayayyen garin zolage da ruman din nan ku samu ruwa karamin kofi ko pure water daya ku tafasa shi, bayan ya tafasa sai ku sauke shi ku bari ya huce.

Daga nan sai ku samu zumanku kamar babban cokali daya ku zuba a ciki sannan ku gauraya.

Sai ku sha kofi daya da safe bayan an karya, kofi daya bayan an yi cimar dare.

Ku yi haka har na tsawon sati biyu, da yardar Allah za ku ga sauki.

Maganin Ulcer na Hudu

Dan'uwa domin hada maganin nan na ciwon olsa na hudu, sai ku nemi wadannan abubuwan da za mu jero;

  • Kabeji (Cabbage)
  • Zuma
  • Lemon tsami (Lemon)

Yadda Ake Hada Shi

Abu na farko shi ne ka samu kabejin nan naka sai ka yayyanka shi kanana, sannan sai ka yi blending dinsa da ruwa kamar kofi daya sannan ka zuba shi a cikin kofi.

Abu na gaba sai ka zuba lemon tsami cokali daya da zuma cokali daya ka juya sai ka shanye. To, haka za ka rinka yi sau biyu a rana.

Allah ya sa a dace.

Maganin Ulcer na Biyar

Ga kuma karin nau'in maganin ciwon olsa na biyar mun kawo, sai ku nemi abubuwan da zan jero domin gwada shi ko Allah zai sa a dace.

Ku nemi;

  • Zuma
  • Lemon tsami (Lemon)
  • Garin hulba (Fenugreek)

Yadda Ake Hada Shi

To, da farko dai za ku fara da tafasa garin hulbarku da ruwa kofi guda, bayan ya tafasa sai kuma ka saukeshi ya yi sanyi.

Bayan ya yi sanyi sai ka zuba lemon tsami cokali daya da zuma cokali daya ka gauraya ka juya ka sha. Kullum ka rinka yin haka sau biyu tsawon sati biyu ko wata daya.

Da yardar Allah za ka ga canji.

Tambayoyi Masu Alaka

Maganin ulcer, maganin ulcer na hausa, maganin ulcer na islam, maganin ulcer sadidan, maganin ulcer na har abada, maganin ulcer zauren fiqhu, maganin ulcer da ayaba, maganin ulcer da plantain, maganin ulcer da kuka, maganin ulcer a gargajiyance, maganin ulcer na kirji.

Previous News Next News