Ciwon Ulcer, Alamomin Ciwon Ulcer, Da Hanyoyin Magance Ciwon

Ciwon Ulcer

Babu wata cuta da Allah Madaukakin Sarki ya saukar ba tare da ya saukar da maganinta ba.

To, ita ma cutar olsa (ulcer) kamar sauran cututtuka ta shigo cikin wannan jerin. Sa’annan, a cikin rubutun nan na yau za mu kawo muku sahihan magungunanta kala-kala domin amfanuwarku.

{tocify} $title={Table of Contents}

Fatanmu dai daya ne; Allah ya sa ku yi nasarar rabuwa da wannan azababbiyar cuta da taimakon abubuwan da muka kawo a shafin nan.

Marabanku da zuwa shafin SeeyBlog.

Kafin mu fara rakarkato muku jawabai, za mu fara yin zuzzurfan bincike game da me ke kawo ita kanta wannan olsa din, da matakan da ya kamata duk mai wannan ciwo ya bi domin wanyewa lafiya.

Me Ke Kawo Ulcer

Babbar alamar ciwon olsa ita ce jin zafi a tsakiyar ciki wajen cibiya ko kirji, kuma hakan na faruwa ne saboda akwai wani ruwan acid da jikin kowanne mutum ke samarwa mai suna hydrochloride acid domin narka abinci.

Sai dai jikin wasu mutanen na samar da hydrochloride acid fiye da kima wanda ke sa shi acid din ya yi wa bangon cikinsu illa sakamakon zafinsa, domin bangon cikin mutum bai da kwari sosai. 

Da zarar acid din ya raunata bangon cikin mutum to olsa za ta iya kama shi.

Sa’annan a wani bangaren kuma olsa na kama mutum ne dalilin kasancewar wadansu kwayoyin cuta na bacteria (helicobacter pylori) wadanda ke haduwa da acid din hydrochloride na narka abinci su kawo rami, rauni, gogewa, kwailewa, ko kuma kwarzanewar bangon ciki (stomach rugae).

To, wannan raunin da suka samar shi ake kira gyambon ciki ko kuma ulcer a turance.

Kuma in har ba a dau mataki na gaggawa ba, wannan kwayar bacteria din ka iya haddasa cutar kansar uwar hanji wacce ake kira da Gastric Cancer. 

Allah ka tsaremu da ita.

Kamar yadda wasu ke ta fadi, wai olsa yunwa ce ke kawo ta. Amma a zahirin gaskiya ba yunwa ke kawota ba, sa rai da cin abinci kuma ba a samu ba ka iya sa jiki ya sako wannan hydrochloride acid din fiye da kima daga nan sai ya haifar da olsa.

Kazalika, kwayoyin cuta ko wani magani da mutum ke sha na ciwon jiki mai suna, “NSAID” to suna haddasa ciwon olsa. Saboda haka in kana shan sa to ahir dinka. 

Shin Ana Warkewa Daga Ciwon Ulcer

Hakikanin gaskiya ana iya warkewa daga wannan cuta ta olsa idan mutum ya je asibiti aka duba shi, aka tabbatar masa da ita din ce. 

Kuma akwai gwaje-gwaje da ake yi domin tabbatar da olsa din ce ko kuma bacteria.

To, ka ga ba za ka san takamaimai me ke damunka ba, har sai ka je an haska cikinka an bambance tsakanin aya da tsakuwa. 

Sannan akwai bukatar likitan da ka je wurinsa ya tsaya ya yi bincike na tsanaki domin ba duk olsa ce ake shan magani iri daya ba.

In aka samu sabanin baka magani, sai ka yi ta sha, gashi da maganin olsa ne, amma kuma sam ba ya yi maka aiki.

In dai za a dora mutum a kan magungunan da suka dace da abin da ya jawo cutar olsa din na tsawon satittika ko watanni, kuma a bashi shawarar ya kiyaye ka’idojinta ya kuma kiyaye din, to babu tantama da yardar Allah zai warke.

Don haka kada ku ji komai, ana warkewa daga cutar ciwon olsa.

Hanyoyin Bi Don Magance Ciwon Ulcer Ko Yawan Tashinsa

  1. Za ku iya cin naman kaji, abincin alkama, taliya ta alkama, biredin alkama, brown rice, kifi, wake, gyada dafaffiya, dafaffen kwai, kai za ma ku iya shan yoghurt musamman irin probiotic din nan.
  2. A daina cin abinci dan kadan kuma a daina take ciki damdam har a rinka gyatsa ana nishi, a dai ci daidai misali (moderate). Saboda cin dan kadan ko take ciki na tada olsa domin kamar ka dauki shirgegen dutse ne ka danne olsa din da shi.
  3. Ku yi kaffa-kaffa da yawan cin nau’in abubuwa masu dandano sosai, irin dai masu kama baki aji zauzau din nan irin su daci, yaji, sugar, gishiri ko flavor.
  4. Ganyayyaki irin su salad, zogale, cabbage ba sa narkewa a kan kari a cikin mutum, hakan ya sa suka zama barazana ga masu ciwon olsa, domin yawan cin su danyu shar kan sa ciwon ya tashi. Duk da suna da matukar alfanu ga jiki, amma dai masu olsa su yi baya-baya da su.
  5. Ku na shan nono, madara (ko-ta-ruwa-ko-ta-gari) lokaci zuwa lokaci domin suna ba da kariya wurin dakile tashin ciwon.
  6. Yana da kyau kullum da sassafe kafin ku ci komai ku fara da shan ruwa domin hakan na har hatsarin ciwon cancer ya ke magancewa.
  7. Ga masu aikin karfi, in dai kana da olsa, kuma ka yi aiki ka gaji, to kada ka dage sai ka dan karasa don ganin ba yawa karashen, domin za ka iya sumewa yayin karasa aikin musamman aikin in ya yi zafi da yawa.
  8. Yawan barci na tada ciwon olsa, kuma yawan barcin dai ka iya haifar da kamuwa da ciwon zuciya, ko cutar paralysis musamman in mutum na dauke da irin su ciwon suga ko hawan jini.

Baki daya dokokin nan da kuka ji na lissafto, to na olsa ne, mu dai mun fi sanin daina shan abu mai yaji da me tsami. Sakamakon rashin bin dokokinta shi yasa mutane ke jimawa suna fama da wannan cuta ta olsa.

Abubuwan Ci Da Sha Da Ke Tayar Da Ciwon Ulcer

  1. Coffee
  2. Chocolate
  3. Danyen Tumati
  4. Cingam
  5. Abu mai zaki
  6. Abu me maiko sosai
  7. Abu mai daci
  8. Abu mai zafi
  9. Lemon tsami
  10. Abu mai tsami (kunun tsamiya kwananne, 7up da sauransu)
  11. Abu mai dandano sosai (maggi, onga, gishiri da sauransu)
  12. Cika ciki dam har a rinka yin gyatsa
  13. Zama da yunwa
  14. Cin abici mai yaji irin sosai din nan
  15. Soyayyen abinci (wainar fulawa, doya, kosai da sauransu)
  16. Aiki ba hutu
  17. Kin cin isashshen abinci (mawadaci)
  18. Shan giya (barasa)
  19. Shan sigari ko shisha da sauransu.

Akwai abubuwa da dama da ka iya tada olsa. In da zama za mu yi mu lissafto su duka lallai da makarancin wannan rubutu bai samu natsuwa ba.

Shi yasa zai fi kyau mutum ya je asibiti a auna shi, a haska cikinsa domin gano me ke damunsa takamaimai. 

Kada a baka maganin wata nau’in olsa din yayin da kai kuma wata iri daban ce ke damunka.

Tambayoyi Masu Alaka

Ciwon ulcer, alamomin ciwon ulcer, maganin ulcer, maganin ulcer sadidan, maganin ulcer a musulunci, maganin ulcer na hausa, maganin peptic ulcer, alamomin ulcer, maganin ulcer mai kyau, hulba na maganin ulcer, maganin ciwon ulcer, alamomin gastric ulcer, ciwon ulcer, maganin ulcer har abada, magani ulcer, menene maganin ulcer, ganyen gwanda maganin ulcer, maganin matsananciyar ulcer.

Previous News Next News