Yadda Ake Gane Namiji Hariji da Kuma Mace Harija

Namiji Hariji

Mazaje musamman na kasar Hausa dai yawo suke da kutumarsu a cikin wando, kuma saboda tsabagen addini ya bi jini da jijiya, ya ratsa bargon jikinsu hatta al’aurarsu killace ta suke.

Magana ta fisabilillahi, kuma magana ta domin Allah, duk wanda ya san Malam Bahaushe to ya sanshi da alkunya musamman ta fanni irin na nuna tsaraici a fili muraran.

Sai dai yanzu zamani ya zo da wani irin mugun juyin-juya-hali inda Hausawan Kasar Hausa su ka fara sauya alkiblarsa, kai ta kai ta kawo ma hatta riga in suka ga ta yi wa wane kyau to za su areta su yafa su kuma ci magani.

Mai karatu, ina maka lale marhaba da zuwa wannan shafi namu mai albarka na SeeyBlog.

Yau kuma, da yarda hadi da izinin Allah za mu tattauna ne game da harijanci wadda ake ma lakabi da jaraba musamman ta fannin jima’i.

Menene Harijanci

Harijanci na nufin yawan bukatuwa da yin jima’i da kuma rashin saurin gamsuwa da shi, wato dai ya ishi mai yinsa.

Kuma ana samun harijai a jinsin mata da maza, sai dai harijancin mata ya fi fitowa fili, saboda su ne ke matukar uzzurawa matansu har ta kai ga saki in sun kasa dauke bukatar mazajen.

Su kuwa mata wadanda Allah ya halitta da harijanci wasunsu na iya dangana da abinda ya samo, su danne sha’awarsu ko da kuwa abin yana damun su, wasu kuwa bayan mazajensu sai sun kara da na alakoro.

Kai wasu tsabar jaraba har karuwanci mai lasisi suke yi sakamakon jarabar harijancinsu, wato ba ta iya gamsuwa da namiji daya muddin zuwan kan da zai yi bai wuce 3 ba.

Wacece Harija

Harija ita ce mace mai tsananin sha’awa wacce wasu ke yi wa lakabi da jarababbiyar mace.

Ta Yaya Ake Gane Mace Harija

Kamar yadda Allah (S.W.T.) ya haliccemu nau’i, daban-daban kuma duk mu din ‘ya ‘yan Adam ne to haka ya bambanta mata ma musamman ta fannin bukatar namiji.

Sannan akwai shahararru, fitattu kuma sanannun hanyoyin gane nau’ikan mata da yanayin karfin sha’awarsu.

Wannan yasa wasu matan ke yawan sanya safa saboda boye wannan halittar ta su; domin daga lokacin da namiji ya gama karantar nau’ikan kafofin mata ta fannin sha’awarsu to duk wacce ya ga kafafunta zai iya bambance iya karfin bukatarta ga namiji.

Ga hanyoyin gane harijar nan;

  1. Da ka kalli yatsun kafar mace, sai ka lura mabiyin babban ‘dan yatsan kafarta ya fi babban tsayi to hakan na nufin wannan mace tana da karfin sha’awa (harija ce).
  2. In kuma ka kalli yatsun kafar mace, sai ka ga da babban ‘dan yatsan da mabiyinsa duk tsayinsu daya, to hakan na nufin ita wannan macen na da saukin sha’awa.
  3. Sa’annan idan ka ga mace babban ‘dan yatsanta na da tsawo hadi da girma sosai, to hakan na nufin gabanta (gindinta) yana da kofa babba kuma yana da tsayi (gamsar da irinsu sai masu doguwar kutuma).
  4. Har ila yau, idan ka ga babban ‘dan yatsan mace ba babba ba ne, kuma ba shi da tsawo, to hakan na gabanta bai da zurfi sosai kuma yana da matsi.
  5. Idan ko ka ga kafar mace tana da wutsiyar kafa, wato akwai space tsakanin dukkanin yatsunta, to hakan na maka nuni ne da cewa; ita wannan tana da ni’ima da dadin jima’i.
  6. In ko ka ga diddigen mace cike ya ke tab, babu alamun rama a cikinta, to haka na nufin wannan tana da juri’ar jima’i, duk jaraba da kwakwar namiji daidai take da shi, za ta daukeshi.

Wadannan su ne hanyoyi shida da ake gane harijar mace, kuma ba wai su kenan ba, amma abinda ya sawwaka kenan. Ba mu tara sani ga Allah, shi yasa dole mu ce; Allah A’alamu.

Yanzu kam, kuna da cikakken sani game da harijanci, wacece harijar mace da kuma yadda ake gane harijar mace cikin mata. 

Da wannan za mu rufe babin mace, sai mu dunguma zuwa sashin da zai yi bayani game da harijin namiji ko in ce jarababben namiji.

Duk da babu wata specific data da ta tabbatar muka samo bayan dogon nazari da binciken da muka gabatar.

Waye Harijin Namiji

Harijin namiji shi ne namijin da ke da yawan bukatar saduwa da mace, wato dai mai tsananin karfin sha’awa.

Kuma kamar yadda ake iya gane harijar mace, to shi ma namiji ana iya gane shi cikin sauki.

Ta Yaya Ake Gane Harijin Namiji

Gane harijin namiji abu ne mai matukar wuya, saboda in dai ba kebewa kuka yi da shi ba, ya sadu da ke ki ka ga ya kawo kuma yana bukatar ya yi ta yi ba bayan ke kin gamsu to ba kya iya bambance wannan hariji ne ko akasin haka.

Amma kuma, kada kawai daga saduwarki ta farko da namiji ki yi tunanin hariji ne saboda ya yi ya kara, zai kara kuma ya sake karawa.

A’a

Ki bari a dau dogon lokacin in kika ga karfin bukatarsa gareki kullum karuwa ya ke to sai ki yi shiri, domin Allah ya hada ki da mai gamar da ke har ya gundureki.

Shi dai harijin namiji shi ne namijin da ke neman matarsa a kowanne lokaci, burinsa kawai a ci.

Saboda haka duk wacce ke namen hanyoyin sanin harijin namij, don Allah kada ta tayar da hankalinta domin in Allah ya yanka mata kazar auren harijin sai ta aureshi.

Iyakace dai ta koyi wasannin motsa sha’awa da kuma sarrafa namiji yadda ba za ta rinka bari ya na azabatar da ita ba da yawan jima’i.

Na fadi wannan ba wai don tsananin son zuciyata ba ne.

A’a

Akwai aurarraki da dama wadanda suka mutu sakamakon auren harijin namiji da mace ta yi, kuma ita bada ka karfin sha’awa sosai, da an fara sai abin ya isheta, shi kuma ya ce sai ya ci ya gaji.

Shawara ga Harijin Namiji

Ya kai hariji ko in ce jarababben namiji, ba ka da bukatar zama da mace daya muddin ka fahimci ita din ba harija ba ce.

Ka kara aure domin samun biyan bukatarka ta jima’i ba tare da ka uzzurawa matarka ta farko ba.

Daga lokacin da ka fahimci ita fa yawan jima’in nan yana damunta, to, fisabilillahi ka yi kokari ka karo mata kishiya domin ka rage mata nauyi.

A Karshe

Mai rubutun nan bai kasance malami ba, ko wani shehun mai ilimi ba. Mutum ne kamar kowa, kuma na yi wannan rubutu ne bayan dogon bincike da na yi game da harijanci kansa.

Zan so yin amfani da wannan dama wurin yin godiya ga Allah da kuma wanda ya samu damar karanta rubutun nan.

Da fatan ko babu yawa ka dan amfana. 

Allah ya kara wa Annabi Daraja.

Previous News Next News