Tarihin Kawu Dan Sarki (Mawakin Wakar Ingallo)

Kawu Dan Sarki

Kamar yadda rana ke bullowa da hantsi haskenta ya karade duniya hadi da zaga kowanne lungu da sakon cikinta, to haka matasan mawakan Hausa ke bulbulowa kowacce shekara.

Shekarar 2022, shekara ce wacce ke cike da abubuwa wadanda za mu jima ba mu taba mantawa da su ba musamman ta fannin nishadi, kalubalalluka da sauran al’amura.

In dai kai masaurarin wakoki ne musamman na nanaye, ina da yakinin cewa ba sai na gabatar ma da Kawu Dan Sarki ba, to, amma sanin tarihin rayuwarsa zai matukar kawatar kwarai da gaske.

Kazalika, duk inda ka zaga a kasar Hausa ka ce, “Wayyo Katara ta Mara ta” to ko tantama ba na yi za a yi ma amshi da, “Ingallo na Ciwo”.

Hakikanin gaskiya na yi zuzzurfan bincike a yanar gizo ko zan samu wata kafa da aka wallafa tarihin wannan mawaki, amma dai har yanzu ban samu ba.

Bisa wannan dalili na ga ya dace na kara kaimi wurin zakulo abinda ya samu daga cikin tarihin Kawu, ina fatan Allah ya shige min gaba.

Waye Kawu Dan Sarki

Muhammad Sule wanda aka fi sani da Kawu Dan Sarki, haifaffen jihar Kano ne, kuma a cikinta ya girma. To, sai dai ba mu samu cikakken bayani a kan shekarar da aka haifeshi ba.

Kawu mawaki ne mai zaman kansa, kuma ya shahara kwarai da gaske a fadin Arewacin Najeriya da ma sauran kasashe irin su Nijar, Kamaru Cadi da sauransu.

Sa’annan Allah ya kawo dalilin daukakarsa ne sakamakon wata wakarsa guda daya wacce ake wa lakabi da, “Ingallo” a shekarar 2022.

Shekarunsa Nawa Yanzu

To, ba na son yin karya game da rayuwar wannan bawan Allah, amma magana ta fisabilillahi, ba mu da cikakken bayani game da shekararsa nawa a raye yanzu haka.

Muna dai fatan cewa, nan gaba kadan zai bayyana asalin yawan shekarunsa domin kowa ya sani.

Su Waye Mahaifansa

Malam Sule dai shi ne mahaifin Muhammad (Kawu Dan Sarki), sannan ya danganci fulatanci. Kai tsaye ma shi kansa kawun na danganta kansa da fulatanci, kuma in ka saurari wakokinsa za ka tabbatar bafulatani ne kawai Hausa ya ji.

Karatunsa

Nan ma ba mu da cikakken bayani game da makarantun da Kawu da halarta, amma dai muna da yakinin cewa ya yi makaranta firamare har zuwa sakandire a nan birnin Kanon Dabo.

Sai dai ba ma da yakini game da zuwansa makaranta gaba da sakadire. 

Iyalinsa

Har yanzu dai saurayi ne, kuma babu wata kafa da ta kawo jita-jita, ko ‘yan kunji-kunji game da relationship status na Kawu Dan Sarki.

Yaushe Ya Fara Waka

Mawaki Kawu Dan Sarki ya fara waka ne a cikin shekarar 2015, kuma kama ya yi wakoki da dama a wannan shekarar har zuwa shekarar 2022.

Sai dai daukaka ba ta riskeshi ba sai a shekarar nan ta 2022 bayan ya saki wata waka mai taken, “Ingallo” wacce ta karade lungu da kewaye na Arewacin Najeriya.

Daga baya kuma ya saki wakar da ta biyo baya Ingallo mai taken, “Kina A Raina” wacce ita ma ta samu karbuwa tsakanin Hausawa.

Wasu daga cikin wakokinsa sun hada daga;

  1. Ingallo
  2. Kina a Raina
  3. Sanadinkine
  4. Gyara
  5. Sai Da Ido
  6. Cikon Burina da sauransu.

Wasanni a Kasashen Ketare

Kawu Dan Sarki ya yi wasanni a kasashen Afrika ta yama wadanda ke dauke da al’ummar Hausawa.

Ya yi wasanninsa a kasashe iri su;

  1. Nijar
  2. Kamaru
  3. Cadi
  4. Cote D’ivore da saurasu.

Previous News Next News