Cikakken Tarihin Ado Gwanja (Mawaki kuma Jarumin Finafinan Hausa)

Ado Gwanja

Duk inda ka zaga a Arewacin Najeriya ka ce waye Ado Gwanja, to ina da yakinin za a baka amsar shi waye. 

Da zarar an yi maganar mawakin mata to Ado Gwanja ake nufi, haka kuma in ka je gidan biki ka ga mata suna rawa takun bai yi ma ba, lallai ‘yan gidan su Gwanja ne ba su iso ba.

Shin ko menene cikakken tarihin wannan shararren mawakin Hausa kuma mawakin mata?

Samun cikakkiya kuma gamsashshiyar amsa na cikin wannan rubutun namu na yau wanda  ke dauke da cikakken tarihin Ado Gwanja.

Waye Ado Gwanja

Ado Isah Gwanja wanda aka fi sani da Ado Gwanja haifaffen unguwar Birget ne da ke cikin birnin Kano ranar 22 ga watan Janairu a shekara ta 1990.

Mawaki ne mai zaman kansa kuma jarumi a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood wacce ke da reshe a jihar Kano, Arewacin Najeriya.

Gwanja mawaki ne wanda ya shahara kwarai da gaske, haka kuma wakokinsa ma sun shahara tsakanin mata da kuma mata a Arewacin Najeriya.

Shekarunsa Nawa Yanzu

Kamar yadda mu ka bayyana a baya, an haifi Ado Isah Gwanja a shekarar 1990, don haka yanzu yana da shekaru 33 cif a duniya.

Su Waye Mahaifansa

Mahaifin Ado Gwanja dai wato Isah Bahaushe ne dan asali kuma mazaunin jihar Kano. Mahaifiyarsa kuwa asalinta yar kabilar shuwa arab ce da ke zaune a jihar Borno.

Sai dai ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 2020 Allah ya yi wa mahaifiyarsa rasuwa.

Karatunsa

Gwanja ya yi makarantar firamare da sakandire a unguwar Birget. Sai dai kawo zuwa yanzu babu wata majiya  da ta kawo sahihin labari a kan cewa ya cigaba da karatun jami’a.

Iyalin Ado Gwanja

Gwanja na da mata daya mai suna Maimuna, sai dai a shekarar da ta gabata ya saketa. Kamar yadda rade-radi ke yawo, an ce saki uku ya yi mata.

Sai dai daga baya Maimuna ta fito fili ta karyata labaran bogin inda ta ce ita mijinta bai yi mata saki uku ba.

Yaushe Ya Fara Fim

Kamar sahihan majiyoyi su ka tabatar, Gwanja ya fara fitowa a finafinai ne tun shekarar 2009, kuma role din da ya ke shi ne na ‘dan daudu. Sakamakon yadda ya kware wurin yin salon ‘yan daudu a cikin fim, hakan ya sa tauraruwarsa ta fara haskawa.

Daga cikin irin finafinan da ya taba fitowa a matsayin jarumi akwai;

 1. Kicimulli
 2. Dan Yau
 3. Dan Yau a Birni
 4. Dankuka
 5. Dankuka a Birni da sauransu.

Haka kuma kwanan nan ya fito a wani shiri mai dogon zango, Gidan Badamasi, wanda shahararriyar tashar nan ta Arewa24 ke haskawa.

Yaushe Ya Fara Waka

Daukaka dai ta Allah ce, amma Gwanja ya fara waka ne ba da jimawa ba bayan ya fara fitowa a finafinai, wakarsa ta Kujerar Tsakar Gida wacce ya yi a shekarar 2014 ita ce daga baya ta zamo silar daukakarsa.

Ya kuma kware kwarai da gaske a fannin wakokin mata, ana kuma gayyatarsa zuwa wurin bukukuwa da wasanni inda ya ke rera wakokinsa.

Ya nada Aminu Mai Dawayya, tsohon mawakin Hausa a matsayin jagoransa.

Daga cikin fitattu kuma shahararrun wakokinsa akwai;

 1. Kujerar Tsakar Gida 
 2. Mamar-mamar
 3. Asha Rawa-rawa
 4. Dakin Bakuwa
 5. Kilu ta ja Bau
 6. Indosa
 7. Kidan Mata da sauransu.

Mawaki Ado Gwanja ya samu nasarar lashe kyaututtuka wadanda kungiyoyi da kuma daidaikun mutane su ka yi masa. Daga ciki akwai wacce uwargidan Shugaban Kasar Najeriya, Aisha Buhari ta bashi da kuma wasu kamar irin su;

 • 2019 - Samun lambar yabo ta Kano
 • 2018 - Sani Abacha Youth Center Award
 • 2018 - Ƙungiyar Dalibai ta ƙasa (NANS)
 • 2019 - RS Fans Entertainment
 • 2018 - Fitattun Mawakan Hausa

Dakatarwa

Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin ta kasa, NBC, ta hana sanya wakarsa ta “Warr” a gidajen rediyo da talabijin na kasar. A sanarwar hukumar, Warr na dauke da kalaman da basu dace ba kuma ta bayyana rashin tarbiyya.

Hukumar ta kuma yi zargin cewa a wakar an nuna yadda ake tangadi bayan kwankwadar barasa kuma an yi zagi kai tsaye a cikinta.

Haka kuma a baya-bayan nan hukumar tace finafinai da jihar Kano ta nemi mawakin ya amsa kira bayan sakin wakarsa ta, “Chass” wacce ta matukar tada hazo a yanar gizo.

Wasanni a Kasashen Ketare

Ado Gwanja shi ne mawakin nanaye na farko da ya yi wasa a kasar Amurka a shekarar 2022.

Kuma ya shahara sosai a kasashen Afirka ta yamma musamman wadanda ke kunshe da al’ummar Hausawa.

Irin su:

 • Nijar
 • Kamaru
 • Cadi  da sauransu

Previous News Next News