Sauke Sabuwar Wakar Rarara Jagaba Ya Karbi Kasa Yanzu

Jagaba Ya Karbi kasa

Bayan nasarar bazata da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya yi, fitaccen mawakin nan, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya saki sabuwar waka jiya mai taken, "Jagaba Ya Karbi Kasa".

To, shi dai Rarara yadda ka san tsubbu ya ke wurin canka hadi da fadar wanda zai ci zabe a kasar nan musamman shugaban kasa da gwamnoni.

Magana ta gaskiya, ni ban yarda mutumin nan haka kurum ya ke ba, kai wallahi akwai wata a kasa. Sai dai ba a tara sani ga Allah.

Waye Bola Ahmad Tinubu

Bola Ahmed Tinubu wanda cikakken sunansa shi ne; Bola Adekunle Tinubu haifaffen jihar Lagos ne, kuma tsohon gwamnan jihar daga shekarar 1999 zuwa 2007

An haifeshi ranar 19 ga wata March a shekarar 1952. Cikakken akawunta ne, dan siyasa wanda ya yi nasarar lashe zaben da aka yi a shekarar 2023.

Yanzu haka shi ne sabon angon Najeriya.

Waye Dauda Kahutu Rarara

Aku kenan mai bakin magana, sardaunan mawakan Hausa. Kuma jagaba a fannin wakokin siyasa wanda ya ciri tuta.

Shi ne mawakin da ya yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wakar 2015 da 2019 sannan kuma yanzu yana tafiyar jagaba ne.

Ina ma'abota sauraron wakokinsa?

Sai ku ji wannan waka yanzu haka kai tsaye daga Youtube Channel din Dauda Kahutu Rarara.

LATSA NAN KA SAUKETA

Kammalawa

Yanzu kam za mu yi bankwana da maziyarci wannan shafi, sai mun hadu da kai a cikin wani sabon post din mai zuwa.

Previous News Next News