Maganin Karin Kiba na Bature da na Gargajiya

Maganin Karin Kiba

Shi da ma ‘dan Adam ba a iya masa, domin Allah (S.W.T.) da ya halicceshi, ya daidaitashi daidaiton da babu wata daidaitacciyar halitta kamarsa ma bai fa iya masa ba, ballanta mu maraina wayonsa ‘yan Adam.

Tsokaci a kan lafiya (uwar jiki) ga mutumin da ba dalibi ko malamin likitanci ba gaskiya ba karamin gagarumin aiki ba ne, amma duk da haka zan yi kokari na tsakuro daga abinda ya sawwaka daga bayan masana daban-daban domin amfanin maziyarcin wannan shafi.

Yau, da yardar Allah za mu yi bayani ne a kan kiba, maganin karin kiba na gargajiya, na bature, alfanu da illarsa, da kuma ba da shawara ga mai son karin kiba ko kuma rage ta.

Mecece Kiba

Kafin mu fara ba da bayani a game da kiba, ya kamata mu fara fahimtar cewa kowanne jiki tsatson (offspring) da ya fito daban ya ke, haka su kansu kwayoyin halittar mutane akwai inda wasu daga ciki su ka bambanta.

Wani abin ban mamaki ma shi ne; ita fa kibar nan da mu ke magana a kanta, wasu ma gadonta suke yi, wasu kuwa na yinta ne sakamakon wasu dalilai.

Kiba na nufin karuwar nama a jiki sakamakon rashin motsa jiki, ko kumburashi ta hanyar magunguna da allurori, ko kuma ta dalilin yawan motsa jiki ko daga karfe kullum.

Ko-da-ya-ke matanmu na Hausa/Fulani Allah ya jarabcesu da son yin kiba, ba sa jin kunyarta, su a nasu tunanin ma yin kiba alama ce ta jin dadi, kuma in jikinsu cike ya ke da nama hakan zai kara musu kwarjini.

A karin bincike da karance-karance da na yi, wannan baragurbin tunanin ba ga iya matan Hausa/Fulani ya tsaya ba, kusan duk matan Afrika ma haka abin ya ke, kai wani lokaci ma fa har ado ake yi da kibar sannan a gorantawa wacce ba ta da ita.

Kaji sakarci!

Karin wani abun takaici shi ne; tun ana yin kibar ta marmari har kuma a zo a zama heavy, wato kibar ta wuce minsharrin, abin kuma ya zo ya dami mutum (walau mace ko namiji).

Sai dai ya kamata mu sani cewa kasusuwan mu (bones) da muke gani iya nauyin da kashin mutum ke dashi da kuma adadin jinin dake jikinsa baya bukatar tsoka fiye da yadda Allah ya tsarosu tare. 

A zahirance tsoka ita ce ke support na kashi in babu iya ko kuma ta yi wa kashin nauyi to tafiya ba za ta yiwu ba koda kuwa kafar sak take a mike.

Shin Maganin Karin Kiba Na Da Illa Ga Lafiya

Tambaya ce wannan da ya kamata mu nutsu domin yi mata wayayyiyar fahimta, shi shan maganin karin kiba na da illa ga lafiya? Kuma me ka iya zuwa ya dawo sakamakon shan maganin?

Amsar ita ce, shan maganin karin kiba ka iya haifar da hatsarin ciwon zuciya, koda ko hanta. Haka kuma yana sa jiki ya yi ta ciwo sakamkon lafta wa kasusuwa tsoka mai nauyi fiye da yadda za su iya dauka.

Saboda haka, a takaice, kuma a warware, shan maganin karin kiba ba lallai a karshe ya haifar da ‘da mai ido ba.

Hanyoyin Kara Kiba Naturally

Ga duk mace ko namijin da ke son ya kara kiba ta gaskiya-da-gaskiya, to, akwai hanyoyin da ake bi wurin kara ta.

Sai dai su wadannan hanyoyin ba sa bukatar shan wani maganin gargajiya ko na malam bature.

In dai;

  • Za a ci mai kyau
  • A sha mai kyau
  • A yi wanka
  • A yi wanki
  • A cire dukkanin damuwa (tension da stress)
  • Ga 'yan mata, samari da zawarawa (karshe a yi aure)

To tabbas mace ko namiji za su ga suna yin kiba naturally ba tare da diddikar wani magani ba. Muddin hankali ya kwanta to fa za a yi kumari.

In ya so sai a kara da shan maganin tsusar ciki ko dattin ciki duk bayan wata 2, 3 ko 6 to ba wata matsala.

Maganin ya danganta da irin wanda ku ke so; na bature dai sai a sha Albendazole kwaya 2 rak, na gargajiya kuma sai a nemi su baban jijiya. Kada kuma a manta; a rinka ‘dan motsa jiki akai-akai, ko da yin dogon tattaki ne da dan zazzagayawa bayan an ci abinci.

Yanzu kuma, za mu tattauna ne a kan maganin kara kiba na bature, mu kuma kawo muku sunan ingataccen halastaccen magani wanda 

Maganin Karin Kiba na Bature

A yanzu haka babu wani halastaccen maganin karin kiba da hukumar NAFDAC ta aminta da shi sama da, “MultiVamin”. Domin tabbatar da abinda na fada, sai ku shawarci likitocin da ke kusa da ku.

In kuma na karin cin abinci ki ke so, wanda za ki ci ki tatul in an jima ki kara, to babu sama da, “Multivite”. Duk da haka kada ku sha shi ba tare da tuntubar likitoci ba kun nemi shawararsu a kai.

Sannan akwai magungunan karin kiba da ake siyarwa wadanda ba su samu izini daga hukumar NAFDAC ba, ku kula sannan ku ankare da su, kada ku je ku siyo wa kanku wahala da kudinku

Allah shi ne mafi sani, likitoci kuma masana magungunan bature.

Maganin Karin Kiba na Gargajiya

Da dai ban so yin bayani game da irin wannan maganin ba, duk da a bincikena na samo da dama daga cikinsu.

Dalilina shi ne; ni ko wani wanda na sani bai taba gwadawa ba, kuma ana yawan samun sabani a magungunan gargajiya, mutum ya sha su su zame masa wahala.

Amma duk da haka, babu masanin gaibu sai Allah.

Maganin Karin Kiba na Daya

Ga abubuwan da ake bukata a tanada nan, kuma mun yi bayanin yadda ake hada maganin a kasan abubuwan da ake son ka nema kafin ka yi komai.

  • Waken soya cokali 2
  • Ridi cokali 2
  • Dabino cokali 1
  • Hulba cokali 1
  • Gyada dai dai misali
  • Madarar garin cokali 5

Yadda Za a Hada Maganin

Abu na farko: Ku samu waken suya sai ku gyarashi sosai ku fitar da tsakuwar cikinsa, sannan sai ku soya shi har sai kun ji ya fara kamshi sa’annan ku saukeshi. 

To, bayan soyayyen waken suyar ya yi sanyi, sai ku daka shi sosai har sai ya zama gari.

Na biyu: Ku ridi mai kyau ku gyarashi ku bece shi ya zama babu wani datti a ciki, shi ma sai ku soya shi yadda ya kamata, sannan ku sauke shi.

Daga nan sai ku daka shi ya zama gari kamar yadda ku ka yi wa waken suyar ku a baya.

Na uku: Ku samu dabino busasshe, shi ma sai ku daka shi ya zama gari kamar yadda ku ka yi wa waken suya da ridinku.

Na hudu: Sai ku samu gyara, ku yi kunun gyada da ita daidai wanda za ku iya sha a wannan rana.

To, bayan kun gama kunun gyadar sai ku rinka diban abubuwan da muka lissafta da farko (cokali-cokali din nan) kuna sa wa cikin kunun gyadar kuna sha kullum har tsawon sati biyu zuwa uku.

Da yardar Allah za ku ga kibar jikinku ta sauya.

Sai dai duk da haka ba mu da wani tabbas game da wannan hadin maganin karin kiba na farko, amma Allah ya bada sa’a, nisan kwana sai da gwaji.

Maganin Karin Kiba na Biyu

Kamar yadda wadanda su ka bayar da wannan maganin su ka ce, sun ce; duk wacce ta ke so ta ga fatarta ta yi kyau, jikinta ya rinka cikowa to ta gwada wannan maganin karin kiba na gargajiya.

Ga jerin abubuwan da ake da bukata nan;

  • Lemon zaki guda daya
  • Lemon tsami guda daya
  • Kwanduwar kwai guda daya
  • Zuma mai kyau

Yadda ake hada maganin shi ne; ku matse ruwan lemon tsaminku da lemon zakinku a wuri daya, sannan sai a fasa kwai daya a yi amfani da kwanduwarsa.

Sai a sanya kwanduwar cikin ruwan lemon, a zuba zuma babban cokali uku a cikin ruwan a juya a rinka sha kullum da safe kafin a ci komai.

A cigaba da sha har tsawon sati biyu zuwa uku. Da yardar Allah za a ga canji a fatar jiki da kuma kiba.

Sai dai, duk da haka bamu da wani tabbas game da wannan magani, amma kuma ba za mu hana ku gwada wa ba, domin daga ingantattun majiyoyi muka samo wadannan magunguna kuma nisan kwana sai da gwaji.

Wasu Hanyoyin Karin Kiba

  1. Kana gama cin abinci ka kwanta ba tare da ka mike tsaye kun tattaka hadi da dan zazzagayawa ba ko da kuwa taku 20 ne
  2. Shan damammiyar fura da safe da nono mai kauri kafin a ci komai (ban aminta da wannan ba saboda nono low carbon ne, in kuna son rage kiba ma maida nono abinciku ku sha mamaki)
  3. Yawan shan alewar chocolate
  4. Shan kayan cocoa a shayi akai-akai
  5. Cin nama mai kitse akai-akai
  6. Cin Kwai akai-akai (eggs) (duk da shi kansa kwai na taimakawa wajen rage kiba in ana cinsa, don haka ban aminta da wannan ba shi ma)
  7. Yawan cin farar kaza
  8. Yawan shan lemon kwalba ko na kwali ko na gwangwani
  9. Rashin motsa jiki

Shin Akwai Mutanen Da Ba Sa Lukutancewa

Akwai kyaukyau din mutanen da su haka Allah ya haliccesu, ko uwarsu za su ci ba za su yi irin wannan mahaukaciyar kibar nan da ake tunani ba, sai dai a ga sun dan ciko sun yi dumurmur.

In har kin san ko ka san kana cikin jerin wadannan mutanen, don Allah kada ma ku wahalar da kanku. Ku yi wa Allah godiya da yadda ya yi ku.

Domin masu karamin jiki, ba sa bukatar shan maganin karin kiba, abu daya suke da bukata, wato baki, duk wanda ya aibata halittar jikinka ka bashi wuta yadda ya kamata sannan ka nuna masa bacin ranka a fili yadda gaba ba kai kadai ba, wani ma ba zai kara yi wa ba.

Shawarata Game da Karin Kiba

Wasu mutanen na kukan kiba na damunsu, wasu kuwa na mararin ta zo musu har su lukutance su yi kumatu luhu-luhu.

Amma dai a kasashen da aka ci gaba, maza da mata har zuwa gidajen motsa jiki suke yi domin jikinsu ya dawo moderate. Kada ka bari mutane su yaudareka ko su yaudareki cewa kiba ita ce abu mafi al'ala, a’a, zama da kosasshiyar lafiya ya fi komai dadi.

Kai hatta ciwon suga, mafi yawancin lokuta rashin motsa jiki ke kawo shi, saboda haka kowa ya fita ya motsa jiki domin ya kasance fit.

Ni fa abinda ke bani mamaki da matanmu na Hausa/Fulani shi ne; ba sa motsa jiki domin maintaining din hourglass figure (kirar coca-colar) da Allah ya yi musu, sai su ci su yi tatul kuma su kwanta barci.

Nan da nan za ka ga sun lukutance, ka ga mace da tumbi.

Saboda haka don Allah ku rinka motsa jiki domin hatta mama sakamakon motsa jiki yana jimawa bai gama zubewa ba, haka su kansu hips ana kara girmansu su zama curvy duk ta dalilin motsa jiki.

Ku daina bari ana yaudararku da wadannan magungunan, ku motsa jiki domin kasancewa cikin koshin lafiya kowanne lokaci.

Allah ya kara wa Annabi Daraja.

Previous News Next News