Rashin Lafiya: ‘Yan Kannywood sun ki taimakon Jarumi Mal. Lawan (Dan Gajere)

Kannywood masana’antace wadda ke cike da tarin manyan jarumai da kuma manyan mutane, tun daga kan mawaka, masu shirya finafinai, su kansu ‘yan fim din, da dakaktoci da sauransu.

Sai dai wani abin ban mamaki da sanya takaici shi ne; yadda kaso mafi tsoka daga cikinsu ke kokarin zama taron tsintsiya ba shara.

Dalilin da ya sanya Edita fadin haka shi ne; saboda ga malam dogo (Jarumi Mal. Lawan) nan a cikin matsananciyar rashin lafiya, ya fito da bakinsa ya karya lagonsa ya nemi taimakonsu amma sun yi kememe sun ki taimaka masa.

Malam lawan na fama da matsananciyar rashin lafiya, ya kuma nemi taimako a wurin abokan sana’arsa, amma har yanzu shiru kake ji kamar maye ya ci shirya.

Ku kalli bidiyon da ke kasa;


Yau ina Sarkin Kannywood? Ina su Danja, Su Abbale, Su Lawan Ahmad? Ko duk ba sa nan…

Kamar yadda wata majiya ta tabbatar mana, Jaruma Hadiza Gabon da Adam A. Zango sun taimaka wa Mal. Lawan don maganin jinyar da ke damunsa.

Amma su;

  1. Rarara
  2. Naziru Sarkin Waka
  3. Ahmad Lawan
  4. Sani Danja
  5. Ali Nuhu
  6. Su Saira da sauransu

Duk suna nan sun ki yin komai.

Gaskiya ya kamata su canza rawarsu, a taimaki Mal. Lawan tun kafin lalurar da ke damunsa ta ci karfinsa.

Previous News Next News