Kalli wasan Sallar Hamisu Breaker da Rakiya Mousa a Nijar bayan kace-nacen kwanakin baya

Watanni kamar biyar da suka gabata yanar gizo ta rude da labarin da Rakiya Mousa da bayar yayin tattaunawarta da Jaruma Hadiza Gabon wacce ke shirya shirin Gabon Talk Show.

A cikin tattaunawar, Rakiya ta bayyana irin tsananin son da ta ke yi wa wani jarumi amma shi ko kadan ya ki amincewa da soyayyarta.

Kai har wadansu 'yan hawayen takaici ne suka kubuce mata yayin tattaunawar.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan lamarin, inda da dama daga cikinsu suka yi zargin Mawaki Hamisu Breaker da cin amanar jarumar ta hanyar kin karbar soyayyarta.

Sai dai watanni kadan bayan aukuwar lamarin, muka yi kacibus da wani faifan bidiyon wasan Sallar Hamisu Breaker da Safiya Mousa a kasar Nijar.

Kamar yadda shafin HausaMini ya wallafa, jaruman tare da wadansu jaruman Kannywood da dama sun matukar nishadantar da masu kallo a wasan Sallar da suka gabatar.

Mutane da dama sun matukar cika da mamaki ganin jaruman suna gwangwajewa a wurin wasan tare.
Ku kalli faifan biyion a YouTube.

Previous News Next News