Gwamnan Kebbi ya kori mai bashi shawara kan matasa sakamakon dora bidiyon batsa a WhatsApp status

Gwamnan Jihar Kebbi, Naisru Idris   Hoto: Rasheed


Wani bidiyon dabdala da mataimakin gwamnan jihar Kebbi ya dora a status dinsa na WhatsApp ya jawo masa rasa aikinsa.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya kori Alhaji Babangida Sarki, mai bashi shawara kan matasa sakamakon wani bidiyon da bai dace ba da ya dora a WhatsApp status dinsa.

Labarin korar tasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin a Birnin Kebbi, wacce ke dauke da sa hannun Ahmed Idris, babban sakataren yada labaran gwamnan.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnan wanda ya fusata da wannan muguwar dabi’ar, ya ce mai taimaka masa ya taka dabi’ar da’a da zamantakewar al’ummar Jihar Kebbi, wanda galibinsu mabiya addinin Musulunci ne.

“Idris ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da ke bata tarbiyya da mutuncin mutanen jihar ba.”

Ahmed Idris, kakakin gwamnan ya ce gwamnan ya gargadi dukkanin ma'aikatan jihar da su guji yada irin wadannan bidiyoyi da ke dauke da tsiraici a shafukansu na sada zumunta da ma duk wani taron jama’a ma yanar gizo.

Previous News Next News