Yadda Ake Shawarma (bayani dalla-dalla)

 

Shawarma
Shawarma

Koyon girki abune wanda ya zama wajibi ga dukkaninmu, rajilu da nisa’u.

Wannan dalili ya sa yau na ga ya dace na yi cikakken bayani akan yadda ake hada daddadar abar nan mai suna “Shawarma.”

Sai dai zai kyautu gareni, in har na yi mana ‘dan bayani akan shawarmar kanta.

Mecece Shawarma

To, shawarma dai wata irin cima ce mai ‘dan karen dadi wacce mafi akasari a gidajen masu hannu da shuni da manyan wurare sayar da abinci ake yinta.

Kuma ko a otel-otel ma wani sa’ilin ana iya samun ita wannan shawarma.

Also Read: Yadda Ake Gurasa (Gurasar Tanderu, Tukunyar Karfe, da ta Kwai)

Wadansu na rade-radin cewa ita wagga shawarma da gurasa ake yinta, ni kaina na yarda, amma fa ba karabatin gurasa ba.

Kayan Hadin Shawarma

Domin hada shawarma da kanka ko da kanki, kuna da bukatar abubuwa kamar haka

  • Cream salad
  • Koren tattasai
  • Cucumber
  • Maggi
  • Nikakken nama
  • Labanese bread
  • Curry
  • Mai
  • Da gishiri

Bayan kin tanadi abubuwa taran nan da na jero, sai kuma ki yi duba zuwa kasa domin koyon yadda ake hada ta.

Yadda Ake Yin Shawarma

Da farko dai ki fara da soya namanki da curry da magi, ki tabbatar naman ya soyu daidai misali yadda zai yi saukin nikawa amma fa ba ya kandare ba.

Bayan kin tabbatar da cewa kin soye namanki, sai ki sauke shi.

Ki samu koran tattasai da cucumber ki yanka su ‘yan guri-guri (daidai ci).

Ki dauko gurasa ‘yar Labanese ko kuma ‘yar gida mai taushi (wacce kika yi ranar) sai ki farkata yadda za ki samu damar zuba kayan hadin a ciki. Ki ajeta a kan faranti.

Sai ki bude cikin gurasar nan ki zuba da nikakken namanki, ki kawo tattasai da cucumber ki zuba a ciki, sannan ki yaryada cream salad dinki a kai da 'dan gishiri, sai ki nadeta a tsaye.

Bayan kin gama, sai ki saka nadaddiyar gurasar nan a cikin oven, sannan ki gasata zuwa mintuna 10 har sai ta gasu.

Sai ki sauketa.

Shi kenan kin hada shawarma. Ita ce wacce Jikan Malam ke mata kirari da shawarma-shawarma.

Cin Shawarma

Kowanne lokaci za ku iya cin shawarmarku, domin tana da ‘dan karen dadi, sannan za ku iya ci da safe, ko rana ko dare.

Zabi dai yana gareku.

Previous News Next News