Yadda Ake Gurasa (Gurasar Tanderu, Tukunyar Karfe, da ta Kwai)

Gurasa
Gurasa

Yau, cikin hikimar ubangiji za mu yi bayani dalla-dalla akan yadda ake yin gurasa.

Misali irin ta tanderu, ta tukunyar karfe, gurasar da ake yi da kwai, gurasar shawarma da sauransu.

Shi girki ya kasance muhimmin abu ga rayuwar mata da maza, wadansu na ikirarin cewa mata kadai aka sani da girki, amma fa a zahirin gaskiya mazan ma akwai magirka na gaske.

{tocify} $title{Table of Contents}

A kaf Arewacin Najeriya, babu inda za ka zo ka ci gurasa ka koshi, ka yi mata cin kaca sai ka zo Jihar Kano (ta dambo ci gari!).

In ko masa ce, to kai tsaye ka wuce Bauchi.

Mecece Gurasa

“Gurasa dai nau’in abinci ce wacce ake hadata da fulawa, sikari, gishiri, ridi, kwai, da yis. Wadansu na cinta da kuli-kuli, wasu da miya, wasu ma hakanta da sauransu.”

Ina ne Garin Gurasa

Eh to, garin da ya ke kan gaba wurin samar da gurasa da kasuwancinta shi ne Jihar Kano.

Domin in har ka shigo kwaryar birnin Kano, ka zagaya har ka fice ba ka hadu da mai tallan gurasa ba, to gaskiya ba Kanon ka zo ba.

Saboda haka duk wanda ya tambayeka ko ya tambayeki ina ne garin gurasa, kawai ka/ki ce, “Kano.”

Yadda Ake Gurasar Tanderu

A kasar Hausa, mafi yawancin lokuta an fi yin gurasar tanderu. Daidaikun mutane ne ke yin wata nau’in gurasar.

Yanzu, za mu koyar da yadda ake yin gurasar tanderu, amma kafin haka sai kun nemi;

Kayan Hadi

 • Fulawa
 • Sikari
 • Gishiri
 • Yis
 • Ridi/Kantu

Yadda Ake Yin Ta

Ki samu fulawarki ki zuba ta a cikin mazubi, sai ki zuba mata yis daidai gwagwado, ki kawo ruwa ki zuba shi ma madaidaici.

Bayan kin zuba sai ki kwaba ta, amma fa kada ki kwabata ta yi ruwa, ki kwaba ta yi ‘dan tauri.

Ya danganta da irin gurasa da za ki yi, in mai zaki za ki yi sai ki zuba suga a cikin fulawar, in mai gishiri ce sai ki zuba gishiri kadai.

In har lokacin zafi ne, to sai ta fi saurin tashi, in ko lokacin sanyi ne, za ta ‘dan jima ba ta tashi ba.

In har kin tabbatar kwabinki ya tashi, abu na gaba sai ki zuba karare a cikin tanderunki ki kunna wuta saboda ya yi zafi.

Da zarar kin tabbatar tanderun ya yi kuna rau, kuma karan da kika kunna ya cinye murus, sai ki yayyafa ruwan kanwa a cikin sannan ki sanya tsintsiya ki share tokar da ke ciki.

Daga nan sai ki jawo kwabinki, ki fara yagar kwababbiyar fulawar nan kina likawa a cikin tanderun bayan kin tala ta a hannunki.

Iya dai yadda kike son fadinta ya kasance, kuma girmanta ma haka, to haka za ki na gutsura kina likawa a jikin tanderun.

Bayan kin kammala cika tanderuin sai ki kawo murfi ki rufe tanderun, bayan mintuna kamar 15 zuwa 20 ki bude shi, ki bare gurasarki domin zuwa lokacin ta yi.

A kula: dole sai kin yi a hankali kada ki je ki kone garin lika fulawar nan a jikin tanderunki domin yana da matukar kuna.

Yadda Ake Gurasar Tukunyar Karfe

Dazu mun koyar da yadda ake yin gurasar tanderu, yanzu kuma za mu yi waiwaye ne zuwa tukunyar karfe.

Shin ta yaya ake yin gurasar tukunyar karfe?

Kafin ki yi komai, sai kin fara da neman...

Kayan Hadi

 • Fulawa
 • Sukari
 • Gishiri
 • Yis
 • Ridi/Kantu

Yadda Ake Yin Ta

Da fari, ku samu fulawarku sai ku debo yis ku zuba mata, daga nan sai ku kawo ruwa ku zuba ku kwaba.

Son samu kada ku yi mata kwabin da za ta yi ruwa, ku kwabata ta yi ‘dan tauri-tauri.

In mai sikari ku ke so, sai ku zuba sikari yayin da kuke kwabin fulawar taku.

In mai gishiri ce, sai ku zuba gishiri.

Abu na gaba, sai ku samu tukunyarku ta karfe ku aza bisa murhu, ku kunna wutar itace a karkashinta, in ta yi zafi sosai ta yi garwarshi, sai ku zare itacen ku bar garwashin da ke kasan tukunyar.

Dalilin cire itacen shi ne; don kada gurasar ta kone.

Abu na karshe, sai ku cura gurasarku ku fadada ta, ku saka a cikin tukunyar.

A kula: Yayin sakawa, ku yi a sannu, kada ku kone.

Bayan kun gama, sai ku kawo murfi ku rufe. In ta gasu za ku fara jin ta fara kamshi.

Sai ku bude murfin, ku bambare gasashshiyar gurasarku.

Idan an gama, sai a kawo murfi a rufe. Idan ta yi, za a ji ta fara ƙamshi.

Yadda Ake Gurasa da Kwai

Gurasa da kwai na da ‘dan karen dadi.

A baya mun koyar da yadda ake yin gurasa kala uku, wato gurasar tanderu, da gurasar tukunyar karfe wacce daidai take da ta oven domin hanyar iri daya ce.

Domin yin gurasa da kwai, sai ku nemi…

Kayan Hadi

 • Gurasa ‘yar Hausa
 • Kwai
 • Mai
 • Gishiri
 • Albasa
 • Tumatir

Yadda Ake Yin Ta

Ku samu kwai sai ku fasa shi a mazubi, ku debo gishiri madaidaici ku zuba a ciki sai ku sa cokali ku kada shi.

Daga nan sai ku yayyanka albasarku da tumaturinku ku debo madaidaici ku zuba a cikin danyen kwanku, ku kada su.

Bayan kun yi abin da ke biye da wannan sai ku samu gurasarku ku yi mata irin yanda da kuke so, daidai yadda za ta shiga baki, sannan ku aje ta gefe.

Abu na gaba, sai ku zuba manku a karko ku dora a kan wuta, in ya yi zafi sai ku matso da kwanon gurasarku da kwanon kadadden kwanku kusa da ku.

Sai ku rinka diban gurasar kuna zubawa a cikin danyen kwan nan kuna tsoma ta, sai ku tsame ku saka a cikin kankon man da ke kan wutar.

Bayan kun zuba watacciya, sai ku barta ta soyu daidai-wadaida, sannan ku tsame ku saka a kwando.

Kuna kammala tuyarku, sai ku zubata a cikin flask.

In ci za a yi, sai a yi harama.

A kula: Ko da wasa, kada wacce ta yi wada da tafasashshen man da ke cikin kason nan, kuma kada ku bar yaranku su yi wada da shi domin zai kona su.

Previous News Next News