Yadda Ake Kunun Alkama (bayani dalla-dalla)

Kunun Alkama


Kunu kam ya kasu gida-gida, su kunun tsamiya, kanwa, gyada, alkama, aya da sauransu.

Yau, zan koyar da yadda ake yin kunun alkama, bayan na yi cikakken bayani akan shi wannan kunu da kuma fa’idar shan sa.

In ba ku sani ba, na tabbata in har ku ka ji abinda ke tattare da kunun nan na alkama to za su daure ku ga kun yi shi, kun kuma sha.

A binciken da wadansu masana harkar iyali suka gudanar, sun gano cewa shi kunun alkama na matukar kara ni’ima ga mata.

Also Read: Yadda Ake Kunun Aya (bayani dalla-dalla)

Na san mata da dama na matukar son su ji maigidansu ya ce musu suna da ni’ima, hakan ya sa dole mu koyar da kunun nan.

Kunun Alkama na Karin Ni’ima

Shi wannan kunun shi ne wanda ake hada shi da;

  • Alkama
  • Aya
  • Sikari
  • Madara

Yadda Ake Hada Shi

Da farko dai, ki samu alkamarki tsaba, sai ki gyarata, ki surfata, bayan kin surfa sai ki wanketa, sannan ki shanyata.

Abu na gaba, sai ki samo ayarki, ita ma ki gyarata, ki surfa, ki wanke sannan ki shanyata.

Abu na gaba, bayan kin gama surfe da gyaran alkama da ayarki, sai ki samu mazubi ki zubasu ki aika a niko miki, nikan laushi.

Bayan an niko sai ki tangade, ki aje garinki wuri guda.

Abu na gaba, sai ki debi garin nan ki dama shi da ruwan sanyi a roba ko kwarya, sannan ki dora tukunya a wuta ki tafasa ruwa ya tafasu daidai damun kunu.

Bayan ya tafasu, sai ki debo ruwan ki zafinki ki kwara a kan damun ruwan sanyin nan, ki dama kununki kamar yadda za ki yi wa na tsamiya.

Abu na karshe, za ki iya zuba sikari da madara, ko sikari kadai ki sha kununki, kai in ma kina so za ki iya saka lemon tsami a ciki.

Fa’idar Kunun Alkama

Kunun alkamar nan na karin ni’ima na da matukar amfani da matar gida da magidancinta. 

Domin zai kara mata ni’ima, shi ma kuma mijin zai iya kara masa yawan maniyyi.

Yanzu, za mu tsallaka zuwa sashen asalin kunun alkama wanda ba na karin ni’ima ba ne.

Kayan Hadin Kunun Alkama

  • Nono
  • Sikari
  • Alkama
  • Gyada malkadaddiya
  • Kayan kamshi

Yadda Ake Yin Kunun Alkama

Da farko za ki kawo garin alkama da wanda ba’a nika ba sai ki wanke alkamarki ki sa a tukunya ki dora a wuta.

Sai ki dauko gyadarki ki dama ki tace ki ajiye a gefe, sai ki duba idan ya yi sai ki sauke ki juye. Sannan ki dora ruwan gyada a wuta.

Idan ya tafasa sai ki dauko dafeffen alkamarki ki zuba ki barshi ya kara nuna.

Sai ki dama garin alkamarki kadan ki sa kayan kamshi.

 Idan ya yi sai ki sauke ki zuba damammen garinki ki juya sosai.

Idan ya yi sai ki zuba suga da nono ki juya sosai ki sawa mai gida da yara.

Kammalawa

A cikin rubutun nan na yau, mun koyar da yadda za ku hada kunun alkama wanda ke karin ni’ima da kuma normal kunun alkama wanda kowa ya sani.

Za ku iya yin sharhi.

Previous News Next News