Yadda Ake Alkubus (bayani dalla-dalla)

Alkubus
Alkubus


Yau, da yardar Allah za mu yi bayani dalla-dalla akan yadda ake yin alkubus cikin sauki, ya yi kyau, ya yi dadi.

Da saninku dai cewa babu wani abu na ci ko na sha wanda ake yinsa ba tare da kayan hadi ba.

Saboda haka, ku nemi

  • Fulawa
  • Alkama
  • Yis 
  • Sikari 
  • Mai
  • Gishiri

Yadda Ake Hada Alkubus

Bayan ka tabbata ka nemi kayan hadin da na ambata guda shiga a sama, sai ka biyo ni domin koyon hada alkubus.

Da farko dai ku nemi garin fulawa da garin alkama, sai ku tankade na alkamar ku gaurayashi da fulawarku, sannan ku kawo sikari, yis da gishiri ku zuba sannan ku kwaba shi, amma fa ya fi na fanke tauri

Abu na gaba, sai ku kawo marufi ku rufe shi, ku daukeshi ku kai shi rana, idan ya tashi sai ku kawo mai ku zuba kadan ku 'dan kara buga shi.

Also Read: Yadda Ake Shawarma (bayani dalla-dalla)

Abu na gaba, sai ku samu leda ko gwangwani ku rinka shafa mata mai kuna diban kwabin nan kuna sawa a ciki. 

Za ku iya yi masa yadda ku ke so, ko dai ku yi shi kamar alala ko kulele.

Abu na karshe, sai ku turarashi. Ku ci da miya kowacce iri ranku ya biya muku.

Bidiyon Yadda Ake Alkubus

Domin mu hutar da ku, hakan ya sanya muka garzaya YouTube domin kawo muku bidiyon yadda ake alkubus, kai tsaye za ku iya kallonsa ta shafin nan.

Kammalawa

Wannan shi ne yadda alkubus cikin sauki, a saukakakken bayani dalla-dalla. Kada ku manta, ku biyo ta Tuwita.

Previous News Next News