Yadda Zaki Yi Dace Auren Namiji Mai Kudi Ko Matsayi

Mata da Miji
Mata da Miji

Kaso 80 na iyaye suna burin ganin ya'yan su mata sun auri mazan da zasu huta. Haka nan kashi 90 na mata, burinsu shine su ga sun auri namiji mai kudi ko mai matsayi.

Sai dai wannan burin da iyayen da 'ya'yan su ke dashi ba duk suk sa'a ya cika ba. Wannan kuwa yana faruwa ne ko dai saboda kaddaran Allah Yayi bazasu auri irin wadannan mazan ba.

{tocify} $title={Table of Contents}

Akwai hanyoyi da dama da mace zata iya dacen aurin namiji mai matsayi ko mai mukami koda kuwa bata taso daga gidan masu arziki ko Matsayi ba.

Ga wasu hanyoyin da muddin mace zata iya binsu, akwai fatan tana iya dacewa da namiji mai abun hannnsa ko kuma mai matsayi.

Ki Zama Mai Kyankywan Hali

Kuskuren da wasu matan keyi idan sun hadu da mazan da suke da wadata ko matsayi shine na son nuna musu suma fa sun waye.

Tabbas duk wani namiji ya son yaga ya auri wayayyiyar mace, sai dai wayewa irin na zamani idan kika nunawa namiji kina dashi dayawa, zai soma shakkar ki.

Nuna masa kinada tarbiya, kina da masu miki fada. Kina kiyaye mutuncin ki fiye da komai. Middin ya fahimci hakan zai soma tunanin aurenki.

Ki Fadada Inda Kike Zuwa 

Akwai matan da kullum suna kunshe a gida, daga makaranta sai gida.

Ba manufarmu shine ki zama mai yawon tsiya ba saboda kina son auren namiji mai kudi ba. Sai dai akwai matan da ake gayytarsu wasu tarurrukan da masu kudi da matsayi suke zuwa amma sai suki halarta.

Akwai bukukuwan kawaye harma da yan uwan da muddin kina halartarsu kina iya cin karo da irin wadannan mazan da su kamu da sonki.

Kafafen Sadarwa Na Zamani

Ba kamar yadda wasu suke tunani ba. Mata da dama sun samu mazan aure da irin wadannan shafukan sada zamunta.

Tabbas babu irin mazan da bazaki iya haduwa dasu ba a a irin wadannan shafukan, sai dai yadda kika maida kanki hakan zasu zo miki.

Also Read: Illar Zama ba Tare da Jima'i ba na Tsawon Lokaci (Ga Budurwa)

Muddin kina son samun mazan aure masu hali da matsayi ta social media, to ki guji yawan saka hotunan ki da yawa a shafuka.

Maza masu matsayi ko kudi basu cika burin auren macen data shahara ba. Kaman yadda mata suke son auren mutumin da yayi suna. 

Don haka yawan baza hotunan ki a shafukan zai sa maza masu niyar aurenki so koma ganin kina talla ta surarki ne maimakon yin haka a wasu lokuta na musamman. 

Don haka idan kina son samun namiji mai kudi ko mai matsayi ta hanyar social media, to ki rage saka hotunan ki idan ma ba zaki Iya dai nawa ba. Ta hakan ne zaki jawo hankalin irin wadannan mazan.

Ki Danne Talaucin Ki

Akwai 'yan matan daga lokacin da namiji ya nuna yana sonki daga wannan lokacin zata maida shi na'uran cire kudi ATM. Sai ta fito da talaucin har na gado ta soma tura bukatunta ga namiji.

Maza masu kudi ko hali, duk da sun fi karfin wadannan bukatun da zata kawo musu, hakan kuma nasa su cire sha'awar auren mace. Daga bisani sai su soma tunanin yadda zasu ci kudin su.

Da zaran kin fahimci tarkonki ya kama irin kifin da kike so, ki daure kada ma kiyi zancen mai kamada kina bukatar wani abu ne bare ma yayi tunanin kina masa roko ne da wayo.

Namiji yana mutunta macen da bata neman komai wajen sa musamman wanda yake da niyar aurenta. Don haka muddin kina son auren namiji mai kudi ko matsayi kada ki taba nuna masa saboda wadannan abubuwan ne ma yasa kike sonsa. Wannan dabi'an na saurin shiga zuciyar namiji yaji yana burin mallakanki koda ba da niyar aure yazo ba.

Kada Ki Bari Ya Rainaki

Akwai maza masu hali da mukami 'yan rainin hankali da a kullum suke neman ganin sun kaskantar da wanda suka fi kudi ko matsayi. Kada  ki bari duk Irin hidima ko son da kike yiwa irin wadannan maza yasa su rika tsinkaki ko kaskantar dake.

Maza masu irin wannan matsayin suna ganin darajar macen da batada hali ko matsayi kuma bata yarda da cin kashi ba.

Wanene namiji mai kudi ko matsayi, ta yaya zaki fahimci wanda kika kamo yanada kudi ko matsayi idan ba sanin sa kika yi ba?

A Darasi Na Gaba zamu amsa wadannan tambayoyin.

Mun dauko rankatakab din wannan bayani daga tsangayar babban malamin nan, Malam Abdul Tonga. Za ku iya bincika Tsangayar Malam Tonga a shafukan sada zumunta domin bibiyarsa ta can.

Previous News Next News