Shafuka Labaran Cin Gindi (Batsa ko Dabdala) da Mawallafansu

Al’ummar Hausawa, al’umma ce wacce aka santa da sanin ya kamata, al’ada, daraja da kuma kima duk a hade wuri guda.

Sai dai sakamakon bayyanar yanar gizo an samu sauye-sauye wanda in aka fada wa wanda bai sani ba sai ra rantse da ajalinsa ba haka abin yake ba.

Alhali kuwa yau, lalacewar wasu da dama daga cikinmu ta kai makurar da har sun fara romance novels wanda in banda tsantsar dabdala babu abinda suke rubutawa a ciki.

{tocify} $title={Table of Contents}

To, amma wa ya isa ya yi musu magana ya ja musu kunne, ya kuma tsawatar musu? Ga dukkan alamu babu domin masu gudanar da irin wadannan rubututtuka abin nasu kam sai dai a’uziya.

Babu wani ‘dan Adam da yake shedancewa ba tare da ya samu masu goya masa baya ba akan wannan turbar shedanci da yake yi.

Recommended Reading: Top 5 Best Free Hausa Novels Blogs in 2023

Abin haka ya ke a duniyar labaran dabdala, finafinai, kai har ma da litattafai.

Mutane na bukatar wadannan irin contents, shi yasa su kuma wadanda suka ga ko da ba daidai bane gwara su basu.

Allah ka shirya mu ba don halinmu ba.

Mai karatu ina yi maka barka da zuwa shafin nan mai albarka na SeeyBlog, shafin da ke kawo muku abubuwa mabambanta, har ma da wanda ba kwa so.

Yau za mu yi binciken kwakwaf a intanit domin kawo muku mashahuran shafukan rubutun dabdala na Arewacin Najeriya da kuma bayanan wadanda suke gudanar da su.

Asalin Labaran Dabdala ta Yanar Gizo a Kasar Hausa

Samun damar binciko tushen bayyanuwar barna irin wannan ba karamin aiki ba ne, amma za mu yi amfani da bayanan da muke da su na shekaru 8 zuwa tara domin yi muku saukakken bayani.

A zahirin gaskiya, wanda ya fara kawo rubutun dabdala a Hausa shi ne Musa Ajayi (za ta iya yiwuwa wasu sun san shi), kuma shi din ma bai samu nasarar watsa wagga muguwar dabi’a ba sai da taimakon mutane (masu neman wannan abu).

Domin ya fara rubutun labarun batsa tun wajen shekarar 2013, kun ga tafiyar da nisa, wajen shekaru 10 fa kenan.

Ya kuma wallafa litattafan batsa da dama, kamar irin su Yar Gata 1, 2, da 3. Abun Mamaki, Cin Duri a Waya da sauransu

Wanne Mataki Ake Yanzu

Yayin da duk duniya ta farga da abubuwan alkhairi da cigaban da kimiyya da fasaha ta ke kawo wa, su kuwa Hausawa a wannan lokacin suke dada cigaba wurin yin tambayoyin dabdala a shafukan sada zumunta, google da sauransu.

Hakan ya sa muke da Youtubers masu wallafa tarkace batsa kuma su samu kudi duk da a dokokin YouTube babu barin irin wadannan contents din.

Haka kuma suke wallafe-wallafe a shafukan intanit suna siyar da litattafai na batsa suna samun kudi, duk da hakan a zahirance ba daidai bane.

Gaskiya batsa a yanar gizon Hausa ta matukar gawurtar da ko tambaya ka yi ta “yadda ake” babu wani sakamako da zai fara zuwar maka in ba na batsa ba.

Kuma shi yake dominating na wannan sashen, kazalika, a binciken da na yi kalmar, “Cin Gindi” ana tambayarta sama da sau 12,000 duk wata.

Saboda haka, mun baci da yawa. Sai dai Allah ya shiryamu.

Cin Gindi

Shi ne saduwa tsakanin mace da namiji, kuma mu dai yadda muka sani ya fi aukuwa tsakanin mata da miji.

Sadda, sadda zamani ya lalace, samari basu da aiki sai dai lalata da ‘yammata, don tsabar rashin kunyarsu azumi na wucewa za su fara jigilarzuwa kyamis domin sayen kwaroron roba.

Allah shi sawwaka.

Jerin Shafukan Gasu Nan

Ku yi mana uzuri saboda jan harshen rubutun nan zuwa dogon layi, saboda haka za mu dakile bayanai haka mu kawo muku fitattun shafukan labaran rashin daraja guda biyar da muke da su a Arewa.

Cin Duri da Ilimin Jima'i

Cin Duri
Cin Duri

Mafi dadewa a cikin duk shafukan labarun batsa na Arewacin Najeriya, domin kamar yadda muka bincika an fara wallafe-wallafe akansa tun shekarar 2015.

Sanannen matashin nan, Musa Ajayi (Malamin Gindi) shi ne mamallaki kuma mawallafin shafin na.

A yanzu haka, shafin ana samun kudade da shi daga Wordpress.com Monetization. Bugu-da-kari, yana maziyarta daga Najeriya sama da 25,000 a kowanne wata.

Musa Alayi dai an haifeshi a 1999 a garin Azare, Awe LGC, jihar Nasarawa. Manomi ne kuma dan kasuwa  wanda ya ke da matukar sha’awar bada labarai.

Shi ne mutum na farko daga Arewacin Najeriya wanda ya samu fiye da Naira Miliyan Daya sakamakon rubutun romance novels, wadda muke cewa labaran dabdala.

Littafinsa na farko shi ne Malamin Cin Gindi, Yar Gata, Fatima yar Baba, Sanadi da sauransu.

In har ana neman pioneer na wannan lamari ta yanar gizo, to gaskiya ba zan bayar sunansa kai tsaye.

Karin wani abin mamaki shi ne; gaba daya Musa Ajayi bai cika wallafe-wallafe akai-akai ba, amma duk da haka har yau shafinsa ne a kan gaba wurin samun mabiya masu ziyartarsa duk wata.

Labarun Batsa

Labarun Batsa
Labarun Batsa

Na tabbata in har na fada maka mawallafin wannan shafin shi ma ba wani mamaki za ka yi ba.

Malamin Gindi / Musa Ajayi, shi ne wanda ya mallawallafin shafin yanar gizon nan na biyu da za mu kawo muku.

Sannan yana samun maziyarta daga Najeriya sama da 16,000 a kowanne wata. Ya kuma kirkiri shafin a shekarar 2015 wato daidai lokacin da ya kirkiri shafin ‘cin duri’.

Bugu-da-kari, tun shekarar 2019 bai sake wallafa komai a kan shafin nan nasa ba, ya barsi ne ra’as sai tsoffin posts din da ya wallafa a baya.

Za ku iya ziyartar shafin domin ganewa idanunku abinda ya kunsa.

Karin bayani; shi wannan shafin ba ya samun kudi da shi sakamakon gudanar da tallan wordpress.com, illa dai kawai shafi ne a yanar gizo da bai kawo taro.

Hausa Love Stories / NectarBoyBlog

Hausa Love Stories
Hausa Love Stories

Akwai muhimman dalilan da suka sa ban dora shafin nan na Abdul Nectar Boy a matakin farko ba.

Dalili kuwa shi ne; tuban muzuru ya yi, in har ba zan manta ba wajejen 2019 Nectar Boy ya rufe rubuce-rubucen dabdala a yanar gizo, har ya ke cewa shi fa ya tuba.

Amma sai gashi daga baya ya dawo ya cigaba da wallafa labaran dabdala ba ji ba gani.

Kuma mafi akasarin labaran da ya ke wa kwaskwarima yana kara wallafasu, ya jima da wallafasu tun wajen 2016.

Za ku iya duba shafin nan nasa.

Kammalawa

Na matukar jin dadi sakamakon yadda aka samu cigaba wadansu matasan da dama suka daina wallafe-wallafen dabdala a yanar gizo, suka koma sashen fasaha.

Sai dai ban ji dadi ba saboda mata marubutu novels sun kwace wannan alkalami sun tsundumashi a rubututtukansu, duk da mafi akasarin rubututtukan na da matukar amfani in aka yi duba a garesu da idon gyara zamantakewar aure musamman sashen kwanciya da gamsar da iyali.

Ni ban kasance wani tsarkakakke ba a cikin wadanda suke samar da shafukan yanar gizo, amma dai ina iya kokarina wurin canza labarin, ta hanyar bayyana wa mutane komai da kuma shawartarsu a kan me-zai-je-ya-dawo.

Allah ya shiryamu.

Previous News Next News