Jerin Mutume 5 Wadanda Suka fi Kowa Kudi a Duniya (2023)

Dukiya dai kam gashin hanci ne, haka kuma umarnin mai ita kawai take ji.

Yau, za mu kawo muku jerin wadansu fitattun masu kudi guda goma wadanda duk duniya an yi ittifakin babu wanda ya kai su kudi (in aka ce kudi ba wai ana nufin tsurar takardun Nairori ba, ana nufin kadara (gidaje, kamfanunuwa, hannun jari dss) da kuma kudin kansa).

{tocify} $title={Table of Contents}

Magana ta gaskiya wadansu sun yi wa wannan irin jerin baragurbiyar fahimta, gani suke yi in aka ce wane ya fi kowa kudi, tunani suke tsurar kudin ya aje.

Alhali a zahiri ba duk tsurar kudin ba ne da shi, akwai kadarorinsa da ake hadawa da su yayin lissafin masu arziki, ba wai nairori ba.

Lissafin Networth (Arziki)

In aka ce networth, ana nufin kiyasin adadin dukkanin duniyar da mutum ya mallaka a duniya.

Daga lokacin da aka ambaci dukiya, sai ka saka komai-da-komai na mutum a cikin lissafi, kamar su hannun jari, kudaden asusu, filaye, shaguna, kamfanunuwa, gidaje, motoci da sauransu.

To, masana harkokin kudi na lissafta networth ne na mutum idan suka kirga duk wadannan abubuwan kuma suka ga darajarsu baki daya za ta kai kaza.

Shi yasa da dama daga cikin mutanenmu basu san su masu kudi bane, kaga mutum da karar da ta haura miliyan 50, amma bai san yadda zai juya kadarar ya mayar da ita kudin da zai rinka kawo masa kudi ba.

Allah shi kyauta.

Waye Yafi Kowa Kudi a Duniya

Za ta iya yiwuwa ku ji tambayar nan ta zo muku a wani bambarakwai, amma ya zama dole ne na yi ta a haka domin amsa muku ita nake son yi.

Bismillah.

Bernard Arnault & family – Dala Biliyan 211

Bernard Arnault
Bernard Arnault

Mutanen Faransa sun matukar rike wuta wurin samar da kudade da masu kudi na ban mamaki.

Bernard Jean Étienne Arnault babban dan kasuwan Faransa ne, mai saka hannun jari, kuma mai aje zanannuka.

Shi ne wanda ya kafa LVMH Moët Hennessy Louis Vuitton, babban kamfanin kayayyakin alatu na duniya, sannan yanzu haka shi ne shugabansa.

Bugu-da-kari, Bernard ne babban jami'in gudanarwa na LVMH Moët Hennessy Louis Vuitton. Kazalika, a shekarar nan ta 2023, yana da shekaru 74 a duniya.

Recommended Reading: Mutane Biyar (5) Wadanda Suka Fi Kowa Kudi a Najeriya a 2023

Kamar yadda mujallar kiddige masu kudi ta duniya, Forbes, ta kiyasta hadi da walllafawa, Bernard shi ne wanda ya fi kowa kudi a duniya yanzu haka.

Yana da arzikin kudi da kara na sama da dala biliyan 211. Kuma ‘ya‘yansa biyar.

Elon Musk – Dala Biliyan 180

Elon Musk
Elon Musk

Elon Reeve Musk FRS hamshakin dan kasuwa ne kuma mai saka jari. Shi ne wanda ya kafa kamfanin SpaceX, haka kuma shi ne shugabansa, kana babban injiniyansa. Shi ne mai saka hannun jari kuma shuganan samar da kirkirarrun kirorin kamfanin Tesla, inc. 

Bugu-da-kari, shi ne shugaba kuma mamallakin Twitter, kazalika shi ne wanda ya samar da kamfanin Boring. Kai yana daga cikin wadanda suka samar da kamfanin Neuralink (wanda duk duniya babu kamfanin da ke samar da ingantaccen internet connection kamar sa) da kuma kamfanin sakakon yanar gizo mai fikira (OpenAI/ChatGPT).

Baya ga haka Musk ne shugaban gidauniyar Musk Foundation. 

A yanzu haka Musk yana da shekaru 51 da haihuwa a duniya. 

Kamar yadda mujallar da ke wallafa jerin masu kudi na duniya da ma kasashe ta wallafa, shi ne wanda ya zo na biyu a sahun wadanda suka fi kowa kudi a duniya.

Domin ya mallaki kudi da kadara na sama da Dala Biliyan 180 a shekarar 2023.

Jeff Bezo – Dala Biliyan 114

Jeff Bezos
Jeff Bezos

Jeffrey Preston Bezos dai dan kasuwan ba’amurke ne, mai gidajen watsa labarai, mai saka jari, kuma dan kasuwar zuwa duniyoyi (kamar su Mars da kewaya sararin samaniya) a dawo.

Shi ne wanda ya kafa Amazon, babban kamfanin saye-da-sayarwa na yanar gizo (e-commerce) da kuma babban kamfanin ma’adanar bayanai a samaniya (Cloud Computing) wanda duk duniya babu sama da shi.

Yanzu haka shi ne shugaban zartarwa na kamfanin Amazon, kuma tsohon shugaba na Amazon.

Kamar yadda mullar Forbes ta ruwaito, Jeffry shi ne na biyu a cikin sahun mutanen da suka fi kowa kudi a duniya a shekarar 2023.

Sannan yanzu haka yana da shekaru 59 a duniya. A shekarar 2024 zai cika shekaru 60 a duniya.

Yana da arziki (kudi, kadara da hannun jari) na sama da dala biliyan 114.

Larry Ellison – Dala Biliyan 107

Larry Ellison
Larry Ellison

A yau, kusan duk wadanda suka yi fintinkua a fannin kudi a duniya masana na’ura mai kwakwalwa ne.

Lawrence Joseph Ellison hamshakin dan kasuwan Amurka ne kuma mai saka jari. 

Shi ne shugaban zartarwa, babban jami’in fasaha kuma wanda ya kafa kamfanin fasahar kwamfuta na Amura, Oracle Corporation.

Yanzu haka shi tsohon jami’in gudanarwa ne na kamfanin Oracle. Shekarunsa 78 a duniya a shekarar 2023. 

In har sabuwar shekarar 2024 ta shiga, to zai cika shekaru 79 a duniya. Bugu-da-kari, arzikinsa na kudi da dukiya sun kai na dala biliyan 107 a shekarar nan da muke ciki.

Warren Buffett – Dala Biliyan 106

Warren Buffett
Warren Buffett

Tsoho kenan mai ran karfe, kudi gareku tsurarsu ba ‘yan kudi ba. Kana hango dari sulallanka na zarta dari.

Warren Edward Buffett babban ɗan kasuwan Amurka ne, mai saka jari, kuma mai ba da taimako. 

A halin yanzu shi ne shugaba kuma mai jan ragamar a kamfanin Berkshire Hathaway.

Bugu-da-kari, shi ne wanda aka fi sani da "Oracle of Omaha," Warren Buffett yana ɗaya daga cikin masu saka hannun jari mafi nasara a tarihin duniya.

Sannan yanzu haka shekarunsa 92 a duniya, yana kuma da ‘ya‘ya uku wadanda ya haifa.

Kamar yadda mullar Forbes ta wallafa, a banan nan yana da kudi da arziki na sama da dala biliyan 106.

In har rai ya kaimu, a shekara mai zuwa zai cika shekaru 93 a duniya.

Kammalawa

A yadda na kudurta, da dai jerin mutane goma wadanda suka fi kowa kudi a duniya zan kawo muku. Sai kuma na yi tunani, na ga ai babu wani da za su karemu da shi in ma muka kawo su yanzu haka sai dai nan gaba in har za mu kara gyara wallafawar nan.

Saboda haka ga jerin masu kudin duniya nan guda biyar na shekarar 2023. Ina fatan kun amfana da wannan rubutu namu.

Previous News Next News