Mutane Biyar (5) Wadanda Suka Fi Kowa Kudi a Najeriya a 2023

Najeriya kasa ce wadda Allah (S.W.T) ya azurta da nau’ikan abubuwa masu tarin yawa, tun daga kan fitattun mutane, ‘yan kasuwa, malamai, yan wasanni, yan cirani, kai har ma da lalatattu ‘yan damfara.

Haka kuma Najeriya kasa ce da ke dauke da attajirai da dama a cikinta da ma fadin nahiyar Afirka. Wadannan mutane sun tara dukiyoyinsu ta hanyar yin kasuwanci iri daban-daban, kuma har ya zuwa yanzu, suna ci gaba da kasancewa kan gaba a jerin masu hannu da shuni a kasar.

{tocify}  $title={Table of Contents}

Yau, za mu yi bayani cikakken bayani akan waye ya fi kowa kudi a cikin wadannan mutane, kuma duk wadannan bayanai mun tsakurosu ne daga mujallar da ke wallafa manyan masu kudi na duniya wato Forbes.

Alhaji Aliko Dangote – Dala Biliyan 13.6

Alhaji Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote

A yanzu haka, kaf fadin kasar nan tamu Najeriya, babu wani ‘dan kasuwa da ya kai haifaffen dan kasuwar jihar Kanon nan, Alhaji Aliko Dangote kudi. Harkokin kasuwancinsa suna da yawa, daga cikinsu akwai samar da siminti, kayan masarufi, samar da taki, kera motoci da kuma sabon babban matatar man da kaf Afirka babu wanda ya fi shi girma.

Shi ne wanda ya kafa kamfanin samar da siminti mafi girma a Afrika, Dangote Cement. Bugu-da-kari, Dangote ya mallaki kaso 85 na hannun jarin kamfaninsa, hadi da arziki fiye da dala biliyan 13.6.

Karanta: Tarihin Alhaji Aliko Dangote (Salsala, Haihuwa, Ilimi da Kasuwancinsa)

A yanzu haka Alhaji Aliko Dangote ya mallaki motoci na hawa wadanda suka hadar da;

 • Bentley Mulsanne
 • Bugatti Veyron
 • Maybach 57S Knight Luxury
 • Toyota Landcruiser Prado
 • Mercedes-Benz CL65 AMG

Kai a zahirin gaskiya Dangote fa har jirgin sama ne da shi na hawa ya je duk inda yake son zuwa. Saboda duk wanda ya mallaki tarin dukiya irin wannan ai dole ya samu private jet. 

Abdulsamad Rabi’u (Bua) – Dala Biliyan 8.6

Alhaji Abdulsamad Rabi'u BUA
Alhaji Abdulsamad Rabi'u BUA

Babu wani Bahaushe ko ma wanda ba Bahaushe ba da bai san Alhaji Abdulsamad Rabi’u mai kamfanin BUA ba. Sa’annan ba na fatan ka yi mamaki don ka ganshi a jerin masu kudi na Najeriya, musamman ma da ka ganshi a sahu na biyu.

Abdulsamad Rabi’u shi ne attajiri na biyu a Najeriya wanda arzikinsa ya kai dala biliyan 8.6. Bugu-da-kari, shi ne dai wanda ya kafa shahararren kamfanin nan na BUA Group, kamfanin da ke samar da siminti, sukari, gidaje da sauransu.

Dan kasuwar mai shekaru 61, haifaffen jihar Kano, ya fara sana’ar sa ta shigo da tama, karafa, da sinadarai, ya kuma gaji fili daga mahaifinsa, hamshakin dan kasuwa.

Ba za mu wuce ba sai mun kawo muku jerin motocin da Alhaji Abdulsamad Rabi’u BUA ya mallaka.

Kuma shi ma ga dukkan alamu ya mallaki jirgin sama, wanda ya ke hawa yana zaga duniya don kasuwanci.

Motocinsa na hawa sun hadar da;

 • Range Rover Sport
 • Mercedes Benz S-Class
 • Armoured Mercedes Benz G-Wagon
 • Toyota Land Cruiser Prado SUV

Za mu dakata a nan, ba wai don mun so ba, a’a, sai don mu takaita bayanan yadda wasu ma za su samu wuri.

Mike Adenuga – Dala Biliyan 6.1

Mike Adenuga
Mike Adenuga

Oh, kun yi tunanin wani Bahaushen ne zai zo na uku ko? To ai farfajiyar kasuwancin Najeriya ba taku bace ku kadai.

Kuma in ba ku sani ba, Mike Adenuga shi ne mai kamfanin nan na sadarwa na Globacom wato GLO da shahararren kamfanin man fetur din nan, Conoil Producing.

Mike Adenuga shi ne ‘dan kasuwa na uku mafi arziki a Najeriya, kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa, yana da dala biliyan 6.1.

Bugu-da-kari, kamfaninsa na Conoil Producing har fitar da man fetur ya ke yi. Ya kuma mallaki motocin hawa wadanda suka hadar da;

 • Rolls-Royce Phantom
 • Mercedes Maybach S-Class
 • Mercedes-Benz AMG C63
 • Armoured Bentley Mulsanne

Haka kuma Mike Adenuga ya mallaki jiragen hawa guda biyu, wadanda ya ke zaryar kasuwancinsa da yawace-yawace a cikinsu.

Arthur Eze – Dala Biliyan 5.8

Arthur Eze
Arthur Eze

Mashahurin mai kudin nan, Arthur (Asa) Eze shi ne ‘dan kasuwa na hudu a cikin jerin wadanda suka fi kowa kudi a Najeriya.

Dattijon mai shekaru 74, ba karamin hamshakin mai kudi ba ne, amma ‘dan kudancin kasar ne.

Arthur (Asa) shi ne shugaban kamfanin mai na Atlas Oranto Petroleum, daya daga cikin manyan kamfanonin samar da mai na Najeriya.

Sannan a shekarar 1992, ya kafa kamfanin sufuri na jiragen sama na Triax, biyo bayan dage harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya.

Asa ya mallaki motoci wadanda suka hadar da;

 • Royle Royce guda biyar
 • Da Maybacks guda bakwai.

Kuma har zuwa yau, yana nan yana gudanar da kamfanunuwansa biyu, wato Atlas Oranto Petroleum da Triax.

Sai dai, na bincika mujallar nan ta Forbes, amma ban ga sunansa ba, bi ma'ana mujallar ba ta san iya adadin arzikinsa ba, komi kuka ga mun wallafa to bisa kiyasi ne.

Orji Ozu Kalu – Dala Miliyan 330

Na tabbata babu wanda zai yi zaton za a samu ‘dan siyasa a cikin jerin ‘yan kasuwa wadanda suka fi kowa kudi a Najeriya.

Amma dole ne a saka shi, domin ta kama ne a yi hakan. Kada ka ji wani ya darsu cikin zuciyarka, domin shi din asali ‘dan kasuwa ne.

Orji Ozu Kalu shi ne tsohon gwamnan jihar Abia, dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Abia ta arewa, kuma babban mai shigar da kara a majalisar dattawa a tarayyar Najeriya. 

Orji Uzor Kalu cikakken dan kasuwa ne kuma hazikin dan siyasa. Shi ne Shugaba na SLOK Holding, kamfani mai zuba jari a banki, jigilar kaya, masana'antu, cinikin mai, da kuma kafofin watsa labarai.

Wasu daga cikin motocinsa sun hadar da;

 • Mercedes Benz S-Class
 • Range Rover Sports SUV
 • Porsche Panamera

Kammalawa

Dukkan godiya ta tabbata ga Madaukakin Sarki Allah, wanda ya bamu damar kammala wallafa mutane biyar wadanda suka fi kowa kudi a Najeriya a shekarar 2023.

Hakika masu kudi (kazamin kudi) ‘yan kasuwa ba za su kirgu ba a Najeriya, saboda haka muka zakulo na sama-sama su biyar muka kawo muku cikakkun bayanai akansu.

Kada ku manta ku yi sharhi a kansa, sannan ku shiga guruf dinmu na WhatsApp da Telegram.

Previous News Next News