Bayani Akan Sallar Dare (Shafa'i Da Wutiri) Da Yadda Ake Sallar Dare

Sallar Dare

Duniya cike take da ‘yan duniya da kuma salihan bayi wadanda su din baki dayansu bayin Allah ne. Kuma wallahi ba lallai ka shaida su ba in kuka hadu in dai ba ikilasinka ne ya kai makura ba.

Ni dai na san bana daga cikinsu, amma har zuwa gobe ban fidda rai daga kasancewa daya daga cikinsu ba domin ba a cire tsammani daga rahamar Allah.

Mai gudanarwa na gidan nan na SeeyBlog shi ne yau ya kade bujensa ya yi zaman dirshan, ya darsa gilashinsa ya shiga komar ilimin malamai magada Annabawa domin debo muku ilimi ya kawo muku.

{tocify} $title={Table of Contents}

Magana ce akan Sallar dare, wacce ba kowanne taliki ne cikin musulmi ya damu da yinta ba muddin ba wata mai alfarma aka shigo ba wato watan Ramadan.

Kada ka yi min musu, domin ba kowa ne ke yin sallar dare ba, amma fa akwai su su wadannan bayin Allah a cikinmu masu yinta, kuma suna da yawa.

Fatanmu dai Allah ya bamu albarkacin masu albarka kuma ya sanya wa rayuwarmu albarka baki dayanta.

Na tabbata yanzu kun gama gajiya da jin zance daga bakina duk da ba zancen zube ba ne.

To, bari mu tsunduma cikin abinda ya sada mu a wagga wuri (SeeyBlog) fatan za ku amfana.

Sallar Dare (Shafa’i Da Wutiri)

Babu sallar da ke kai bawa (mutum) kusa da ubangiji Allah ciki gaugawa fiye da shafa’i da wutiri wacce muke cewa sallar dare. 

Shin ko kun san cewa, Manzon Allah (S.A.W) da kansa ya ce da abaka baki daya duniya da abinda ke cikinta gara a baka damar sallatar shafa’i da wutiri?

Kwarai hakan na nuna irin muhimmanci da girman wannan salla domin kullum fiyayyen halitta yana yin shafa’i da wutiri, kai ko da a halin tafiya ya ke ba ya rabuwa da yin shafa’i da wutiri.

“Ban yi wannan maganar gaba gadi ba, ku duba hadisi na 425 a cikin talifin Sunantu Tirmizi domin tabbatar da abinda na rubutu a sama.”

Bayani Akan Sallar Shafa’i

Daga fahimtar malamai da dama, sallar shafa’i dai sallah ce mai dauke da raka’o’i biyu babu dadi babu ragi. 

Kuma kamar yadda Nana Aisha (Allah ya kara yarda a gareta) ta ce; Manzon Tsira (S.A.W) yayin da yake gabatar da raka’ar farko ta sallar shafa’i ya kasance yana mai karanta suratul Fatiha da kuma suratul A’ala (sabbi hisma rabbikal a’ala).

Also Read: Kudin Aikin Hajjin Bana na Shekarar 2023

Yayin da ya shiga raka’a ta biyu kuma yana karanta suratul Fatiha da kuma suratul Kafirun (Kul ya Ayyuhal Kafirun). Bayan ya gama, sai kuma ya yi zaman tahiya sannan ya yi sallama.

Ga wanda bai san yadda ake yin karatun tahiya ba, ko kuma wani sashe daga cikinta ya kubce masa sai ya duba yadda ake karatun tahiya daga shafin FreeBlog.

Bayani Akan Sallar Wutiri

Malamai da dama sun fi karkata ga cewa, sallar wutiri raka’a ce. Duk da wadansu sun karkata ga sabanin haka, amma mafi akasarin malamai sun fi karkata ga raka’a daya ce.

To, mu ma, za mu tsaya ne a kan maganar malamai masu rinjaye. Kuma za mu yi bayanin yadda ake yin sallar wutiri ta hanyar koyi da Manzon Allah (S.A.W).

Domin a addinance babu wani abin koyi da ya wuce Manzon Tsira, kazalika duk wanda ya bi tafarkin da ya ke bi sau da kafa ba zai taba sauka daga hanya ba.

Kamar yadda Nana A’isha (Allah ya kara yarda a gareta) ta ce (a hadisin Jabir Bin Abdallah, hadisin Imam Tirmizi wanda Imam Nasa’i ya ruwaito a hadisi na 1,729); “Manzon Allah ya kasance yana karanta suratul Fatiha da kuma suratul Ikhlas (Qul huwallahu ahad) sai ya karasa yayi sallama.”

Bi ma’ana, Manzon Allah yana karanta suratul Fatiha da suratul Ikhlas (Qulhuwallahu ahad) yayin yin sallar wutiri sannan ya yi sallama a karshe kamar yadda ake yin sallamar salla.

Kumamawa, a wani sahihin hadisi da Imam Tirmizi ya ruwaito; “ya ce wani lokacin Manzon Allah (S.A.W) bayan ya karanta suratul Fatiha yana karanta suratul Ikhlas, da Falaqi da Nasi a sallar wutiri, dan haka ya halatta ka karanta iya suratul Ikhlas bayan Fatiha, in kuma kana so ka kara da Falaqi da Nasi.” Allah ne mafi sani.

Akwai karin bayanai masu zurfi akan wannan darasi na nan zuwa.

Previous News Next News