Ainihin Kudin Aikin Hajjin Bana (Shekarar 2023)

Kudin Aikin Hajji

Babu wani maniyyacin aikin hajji na fadin Najeriya da kewayenta da ba zai so sanin ainihin takamaiman kudin kujerar jirgi da sauran dawainiya zuwa kasa mai tsarki ba.

Muna yi muku barka da zuwa wannan shafi namu na SeeyBlog, shafin da ke kawo muku muhimman abubuwa da suka danganci rayuwarku ta yau da kullum ta fuskar, addinin, al’ada, labarai da abinda ba za a rasa ba.

{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}

Hakikanin gaskiya an samu kari hadi da hauhawar kudin aikin hajji fiye da yadda aka sani shekaru tara (9) da suka wuce.

A shekarar 2013 kudin karamar kujerar aikin hajji ya kai naira dubu dari shida, yayin da babbar kujera kuma ta kai naira dubu dari bakwai.

Har ila yau, a shekarar 2015 gwamnatin Najeriya karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ta kara kudin aikin hajjin na karamar kujera ya koma dubu dari bakwai da sittin da shida, matsakaiciya dubu dari takwas, babbar kuma dari tara da biyar.

To, haka farashin zuwa aikin hajji ya yi ta hauhawa yana karuwa a mulkin nan na Buhari har zuwa shekarar 2022 inda ya kai akalla naira miliyan biyu da rabi.

Kuma a shekarar nan maniyyata da dama sun koka kan tsadar kudin aikin hajjin da gwamnati ta kara alhali makar nan ba nisa ta kara ba.

In ko haka ne, sai mu yi duba na tsanaki ga lamarin nan na biyan kudin aikin hajin nan, mu ga nawa ya kamata ko muke da yakinin wadannan mutane za su karba a hajjin bana.

Kudin Aikin Hajjin 2023 a Kano

Hukumar jin dadin alhazan jihar Kano ta fara karbar kudin aikin hajji na bana, kuma yana farawa ne da naira miliyan daya da rabi (1.5m) na karamar kujera.

Kujerun nan dai mun sani rukunai ne da su har uku, akwai karama, akwai matsakaiciya sai kuma babbar kujera.

To, ku kuma ayuhannasi, masu karamar kujera sai ku tanadi irin 1.6m din nan domin yin komai cikin sauki har ma a samu rara.

Kudin Aikin Hajjin 2023 a Sauran Jihohi

Ga duk wani maniyyaci da ke da niyyar yin aikin hajjin bana kuma daga sauran jihohin Arewa ya fito to shi ma kudin da jiharsa ke caja ba su wuce miliyan daya da dubu dari biyar ba.

Kammalawa

Mu kam ba wasu shafaffu da mai bane da za mu yanke kudin aikin hajjin bana ba gaba-gadi ba tare da yin wani dogon bincike ba. 

Kafin mu wallafa wadannan bayanan mun yi bidiyen kakaf a yanar gizo sannan muka samo muku wannan sahihin labarin.

Sabida haka komai kuka gani a shafin nan legit ne, kuma za mu so yin amfani da wannan damar wurin yi wa dukkanin wadanda suka samu damar halartar hajjin bana fatan alkhairi.

Previous News Next News