Yadda Ake Shan Nonon Mace Da Kuma Yadda Ake Gyaran Nono Kyauta

Nonuwan Mace

Yau fa a kan babban darasi za mu tattauna, kuma za mu yi karatun yau ne ga manyan dalibai (‘yan kutumar uba) wadanda ke yin tambayar batsa a kafar Google Search Engine.

Insha Allahu yau zan yi muku bayani a kan yadda ake shan nono da nonuwan mace ta ji dadi, kuma ko wacce irin macece walau budurwa, ko bazawara ko kuma matar aure.

{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}

Sai dai kafin mu tsunduma cikin darasin nan, zan so yin amfani da wannan dama wurin gargadar makarancin post din nan a kan ya ji tsoron Allah ya rage tambayoyin batsa in dai ba mata ce da shi ba ko wata kwarkwara.

In har ka yi tambayar nan sannan ka ziyarci shafin nan domin ka koyi abinda za mu koyar yau ka je ka lalata wata, to kai tsaye zan iya cewa kai da Allahnka.

Bai kuma kamata mu fara koyar da ku yadda za ku sarrafa nonon mace ba ba tare da mun yi cikakken bayani a kan wannan halittar ubangiji ba.

Menene Nonuwan Mace

Mama, nono ko nonuwa, wadansu kulatai ne kwara biyu da su kan tsiro daga kirjin mace da zarar ta fara balaga. Fitowarsu na daga cikin alamomin balagar mace.

Halittace ta ubangiji wadda ya ke yinta ga mata kadai ko kuma wadanda halittarsu ta samu tangarda wato mata-maza. 

Har ila yau, nono ya kasance abin da ke bambanta jinsin mace da namiji. 

Kazalika duk wata mace wadda ta haura minzalin balaga kuma aka ga babu nono a kirjinta to alamu ne na matsala, amma fa a zamanin yanzu.

A zamanin da, sai mace ta kai shekaru 20 ma babu nono, babu kuma alamar ya taba fitowa a kirjinta. Amma fa ban da wannan zamanin da muke ciki da ‘yar shekaru 13 za ku ganta da nono a kirji tana yawo da shi.

Kuma a banciken da aka gudanar an gano cewa, nonon mace na dama ya fi na hagu tsayi, amma wacce ke da tantama sai ta auna da kanta ta gani.

Kirjin mace shi ne abu na farko da maza ke fara yin tozali da shi da zarar sun hadu da ita. 

Domin shi ne abin da ke bayyana kyawun diya mace da zarar sun fara tsirowa har suka kai minzalin girmansu.

Baya ga haka, Allah ya halicci nonuwan mace domin ya zamto wurin adan abincin jinjiri bayan ta haihu. Yadda zai mai da shi abinci na ‘dan lokaci mai tsawo kafin ya fara cin abinci mai nauyi.

Nonon Mace a Bangaren Jima’i

A bangaren saduwar aure kuma, nonon mace na dauke da akalla ko fiye da kaso 35 wurin samar da dadin saduwar aure.

Irin ana yi ana wasa da shi din nan.

Saboda in da za ku kasa mata zuwa kaso 100, to kaso 70 daga cikinsu sha’awarsu na saurin motsawa ne da zarar an yi musu wasa da shi nonon nan nasu.

Bisa wannan dalili ya zame wa dukkanin mata wajibi su tsaya tsayin daka wurin ganin sun gyara, tattala, kulawa tare da alkinta nononsu.

Ko-da-ya-ke mun ce mace ta kula da nonuwanta, amma ba hakan ke nufin ta bi wadansu batagarin hanyoyi ba wurin kulawar da shi, misali irin su; sajari wato tiyata a sauya mata da silikon.

Hanyoyin Kula Da Gyaran Nono

Masana sun yi iya kokarinsu wurin gano hanyoyin da ake bi (naturally) wurin gyaran nono ba tare da hankali ya tashi ba.

Su wadannan hanyoyi da za ki iya bin su sun hadar da;

Cin Abinci Mai Kyau

Gareku mata, duk wacce ke samun abinci mai rai da lafiya kuma mai gina jiki tana ci to za ta iya gyara nonuwanta har ta tsufa da su a kirjinta.

Saboda duk tsufanki in har kina samun abinci mai kyau ki gyatse, a koshe ki ke, kuma lafiyarki kalau, to za ki iya tsufa da nonuwanki a kirjinki.

Son samu mata ku rinka samun kayan marmari kuna ci irin su kifi, nama, madara, lemo, ayaba, abarba da sauransu.

Kula Da Girman Jiki (Body Balance)

Duk wata mace wadda ke bukatar tsufa da nonuwanta a kirjinta to son samu ta rinka kula da girman jikinta, wato dai kada ka bari ta zama sukumbiya (asurkubi babbar kaya).

Kada kuma ta bari ta rame ta kanjame in dai ba rashin lafiya ce ta kamata ba, ta rinka motsa jiki akai-akai ko a gida ne.

Akwai dalilin da ya sa muka fadi abinda mu ka ce a baya, shi yawan kiba kan sa fatarki ta yi rabebe, wanda hakan zai iya kawo zubewar nononki.

Ita ko rama in har ta yi yawa to za ta sanya jikinki ya kasa samun isasshiyar fata da za ta rike nonon naki har ya tsaya a tsaye.

Sanya Rigar Nono

Ya zama wajibi, kuma dolen-dole mata su na la’akari da irin rigar maman da suke amfani da ita. Kada su na amfani da rigar nonon da za ta matse nonon nasu (ta yi musu kadan) kada kuma su na amfani da wacce ta yi musu kadan.

Su nemi moderate su rinka sawa, kowacce mace akwai irin cup dinta na nono, akwai masu c, e, ee, d, da sauransu.

Fatan an fahimta.

Ku Rinka Motsa Jiki

Na sani, al’ummar kasar Hausa ba ta damu da wani abu wai shi motsa jiki ba, an fi son a ga mutum ya burkuce, ya zama dan lukuti, to wai hakan shi ne alamu na jin dadi.

Amma fa a gaskiyar lamari abin ba haka ya ke ba.

Yin wasannin motsa jiki na kara wa jikin mutum lafiya, sannan yana sa nonon su zamto masu kyaun gani.

Saboda duk lokacin da kike motsa jiki to jini na samun damar kewayawa zuwa dukkanin sassan jikinki.

Ki rinka fita jogging a kewayayyen fili ko na cikin gidanki ne, ki rinka ‘yan tsalle-tsalle domin rage nauyi, sannan ki daidaita cin abincinki domin ci ba na misali ba kan sa kiba.

Kuma a ci a kwanta ma kan sanya kiba.

Ki Kiyaye Wanka Da Ruwan Zafi

Yin wanka da ruwan zafi na kawo raguwar karfin fatar mace, wadda hakan na sa nonuwanta su zube cikin kankanin lokaci.

Amma ba mu da masaniya game da wankan jego da ake yi har yanzu a karkara.

Ko ma dai menene, duk wacce ke fatan tsufa da nonuwanta a tsaitsaye bisa kirjinta, to ya kamata ta rage wanka da tafasasshen ruwa.

Kwanciya Ruf-da-Ciki

Bai da wani amfani mace ta rike sarar kwanciya ruf-da-ciki, wato bayanta bisa kirjinta, ta rinka danne nonuwanta.

Domin matsala ta farko dai ba za ta sake ta shaki numfashi ba yadda take so yayin barcin nan nata.

In kina kwantawa a kan nonuwanki to hakan na da illar da zai iya sanya wa nonuwan su zube ba tare da sun yi dogwaye shekaru ba a kan kirjinki.

Yadda Ake Shan Nonon Mace

Nonuwan mace dai suna da matukar saurin dauka da kai sako kwakwalwa sakamakon jijiyoyin aike da sako da suke da su. 

Kuma kamar yadda mata ke son a yaba nononsu, to haka ma maza ke son tsotsar nonon mace.

Saboda haka kafin ka fara tarawa da matarka son samu ka murjeta ka tayar mata da sha’awa yadda ya kamata, ka sha ta ka tsotseta kamar alewa har sai ka fahimci ta bukatu da kai.

Kada ka ji kunyar komai yayin da ka zo tarawa da iyalinka, ka saki jikinka ka sha mamanta yadda ya kamata, ka yi wasa da kayuwansa sosai yadda za ta ji dadi.

In ko shayarwa ta ke yi, kada ka ji komai ka kafa bakinka ka sha kai ma, domin babu wata illa da ruwan nonon mace ke yi wa namiji babba.

Hasalima yana kara wa namiji babba kuzari kamar yadda ya ke kara wa jarirai, sai dai, ban fada ma haka domin ka hana diyanka samun maman sha ba.

Tsotsar nonon mace na taimakawa wurin daidaita tsarin gudanar jikin jikinta.

Kuma yayin da ka zage ka ke tsotsarshi, za ka ga numfashi ma da-sauri-da-sauri za ka ga tana yi.

To, bugun zuciyarta ne ke karuwa zuwa sau 110 a duk minti guda, kuma wannan saurin bugun yana zame mata kamar motsa jiki ne.

Kammalawa

Da wannan na ke son rufe wannan dan takaitaccen rubutu nawa, fatana dai Allah ya shige mana gaba, ya kuma rufa mana asiri duniya da lahira.

Kuma ban yi bincike hadi da zakulo wadannan bayanai domin ka debesu ka gwada a kan diyar mutane ba (wato zina) na yi shi ne domin mazaje masu aure.

Ba na goyon bayan cin gindi ba tare da aure ba, fatan Allah ya shirya mu ya shiryi dukkanin zuriyarmu da zuciyarmu bisa tafarki madaidaici ameen.

Previous News Next News