Mtsew: Gwamna Ben Ayede na Kuros Riba ya yi Alfahari saboda biyan Albashin Ma’aikata da ya yi

Ben Ayede
Gov. Ben Ayede

Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya bayyana biyan albashin ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a matsayin kyakkyawan abin da gwamnatin sa ta yi.

Ayade, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba ya bayyana kansa a matsayin "babban jarumi," ya kara da cewa mazauna garin na murnarsa da nasarorin da ya samu.

A cewarsa, biyan albashin ma’aikatan gwamnati da na fansho ya fi kowane aiki muhimmanci.

Ayade ya kuma yi ikirarin cewa kudaden da Cross River ke samu daga kudaden da gwamnatin tarayya ke samu bai kai na albashin da gwamnati ke biya ba, inda ya ce ya cancanci a yaba masa bisa cike gibin da aka samu.

Ya ce, “’yan kasar nan abin ya fi daukar hankali fiye da kokarin nuna cewa mu kasa ce mai tasowa alhalin ku talakawa ne. Zan iya gaya muku Kuros Riba a matsayi na daya ta fuskar sadaukar da albashi da fansho duk da haka mune na 36 a bangaren rabon tarayya.

“Abashi da fansho da biyan hakkokin mutane hakki ne kuma bai kamata ya zama nasara ba. Sai dai ya zama nasara saboda tazarar da ke tsakanin abin da nake samu da abin da ya kamata in biya a matsayin albashi kadai ya nuna akwai gibi.

“Ina da dabara. Idan ka zo jihar Kuros Riba a yau, ni jarumi ne. Zan iya gaya muku cewa na yi murna da kaina kuma mazauna Kuros Riba suna yi mani murna.”

Previous News Next News