Mawakiya Ayra Starr ta Soke Wasannin da za ta yi a Amurka Kan Rashin Lafiya

Ayra Starr

Shahararriyar mawakiyar wakar nan ta kudancin Najeriya wacce ta yi fitattun wakoki irin su, “Sability” da “Rush”, Oyinkansola Sarah Aderibigbe, wacce aka fi sani da Ayra Starr, ta soke dukkan shirye-shiryenta wasanninta da za ta gabatar a Amurka saboda rashin lafiya.

Har ila yau, an sahale wa mawaƙiyar don ta yi wasa a ' Something In The Water Concert’ a Birnin Virginia tare da ASAP Rocky, Busta Rhymes, da ɗimbin sauran manyan taurari.

Da take bayyana hakan a daren Lahadi a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Instagram, Ayra Starr ta bayyana cewa likitanta ne ya kwantar da ita a kan gadon gaggawa.

Yayin da ta ke ba ta hakuri kan rashin halartar shirin da ta ke jira, ta yi wa masoyanta alkawarin dawowa ta musamman.

Ta rubuta: “DC, VA da Houston yarinyarku tana cikin kalubale. Likitana ya shawarce ni da in rage gudu, don haka ina kan hutawa na gaggawa.

“Don haka kuyi hakuri na kasa haduwa da kowannenku kamar yadda aka tsara. Har ila yau, ina mai baku hakuri don na san za ku ji babu dadi amma na yi alkawari zan dawo gare ku ta hanya ta musamman lokacin da za mu sami lokacin cashewa. Ina godiya da addu'o'inku da fatan alheri."

Previous News Next News