Mawaki Ado Gwanja ya Saki Sabuwar Wakarsa Mai Taken, “Iye”

Ado Gwanja

Bayan jira na dogon lokaci da masoya wakokin Ado Gwanja suka yi suna jiran ya sakar musu sabuwar wakar da ya alkawurta musu.

To, yanzu haka ya saketa, za kuma ku iya sauraronta kai tsaye daga Youtube Channel dinsa, ko a AudioMack, Apple Music, Spotify, BoomPlay da sauransu.

Waiwaye

A shekarar 2022 ne dai Ado Gwanja (mawakin mata) ya saki wadansu jerin wakoki wadanda suka yi matukar tayar da kura a yanar gizo.

Wakokin nasa wadanda suka da irin su, “Warr”, da kuma “Chass”.

Haka kuma a farkon sabuwar shekarar nan ta 2023 nan ma ya saki wakarsa mai taken, “Luwai”.

Sai dai ban da wakar, “Warr” babu wata daga cikin wadannan fitattun wakoki nasa da ya yi wa bidiyo.

Mostly, dai audio kawai ya ke saki domin a yi rawa a cashe kuma a yi challenge a Tiktok.

Wakar Iye

Domin na samu damar baku labarin yadda ya kamata sai da na fara garzayawa Youtube dinsa na kallota wakar tukunna.

Aradun Allah wakar nan ta yi matukar dadi, ba za ku tabbatar da hakan ba sai kun ware lokaci kun saurareta tukunna.

Ina masoyan Ado Gwanja, to, sai gareku.

Previous News Next News