Bukatuwar Gyaran Jiki (Kamshi, Amarya, Gyaran Fata da Fuska)

Gyaran JIki

Daga shekaru dari baya zuwa yau, al’ummar Hausa ta ginu ne kan tsananin yarda da amanna da magungunan gargajiya, daga baya-bayan nan ne ma magungunan musulunci suka fara shura tsakanin wannan al’umma.

Za ta iya yiwuwa mata kadai aka fi sani da yin bincike akan gyaran jiki ko dan su birge mazajensu, amma a zahirin gaskiya su kansu mazan ma suna yin irin wadannan bincike sai dai ba kasafai ba.

Dalilin da yasa ba kasafai maza ke yawan tambayoyi akan gyaran jiki ba, sai don suna yawan siya tare da amfani da sassake da magungunan gargajiya a hanun mutanen da ke yawo kwararo-kwararo, lungu-lungu, sako-sako suna tallansa.

Kuma kun san me? Mafi akasarin magungunan da suka fi bida ba za sa wuce na sanyi da kara karfin maza, basir, shawara, olsa (gyambon ciki), macijin ciki, kaban ciki, amosani da sauransu.

Bugu da kari, a tasu fadar, wai sai hutacce ne kadai ya ke damuwa da matsalar jikinsa, kamar shape, kuzari, girman uwar ciki, teba da sauransu, alhali lamarin a zahirance ba haka ya ke ba.

‘Yar‘uwa, ‘dan‘uwa, kada kuji ba dadi don na kira mutanenmu masu amfani da magungunan gargajiya, domin kafin na fara rubutun talifin nan ni ma sai da na sha wani da nono. Don haka duk kanwar ja ce...

To, amma akwai dalilin da yasa mutane ke bincike ta yanar gizo game da kalmar, “Gyaran Jiki” dalilin kuwa shi ne, “Suna da matsalar da take damunsu game da jikinsu (wadda a turance ake kira body insecurities).”

Bayan na gudanar da zuzzurfan bincike ta Intanit game da dalilin wannan tambaya da kuma irin sakamakon da ke bayyana, sai naga ashe har zuwa yau babu wani sahihin talifi da yake bayani dalla-dalla akan matsalar, kuma ya kawo dukkanin magungunan da mutane ke bukata domin magance matsalar.

Inda za ka/ki san abin ya matukar yin tsamari, a lalace ana yin tambayar, “Gyaran Jiki” sau dama da dubu goma kowanne wata, kunga in muka lissafta dubu goma sau 30, to ya kama 300k searches per year akan wannan tambayar.

Haka ne ya bani kwarin gwuiwar ware wani kaso daga cikin lokacina mafi daraja domin wallafa talifi akan gyaran jiki, wanda ba a kan iya matsalar mata zai tsaya ba, har ma da mazan.

Tun da nake ban taba tunanin zan yi tsallen albarka na tsoma bakina game da matsalar da ta shafi ‘yan‘uwana mata ba (musamman irin personal issues na jiki da gyaransa), domin na yi amanna da maganar da suke fadi; matsalar ‘ya mace ta ‘ya mace ce. 

To, amma duk da haka in wuri ya kure sai a bar wa irinmu (gardawa) su shigo don bada gudunmawarsu wurin kawo wasu cigabobi a cikin al’amuran mata saboda su din iyayenmu ne.

Su kuwa maza, dama mu ne, mun matukar sanin kanmu kamar yadda mata suka san kansu. Duk abinda kuka gani na magani ko hadi, to daga wurin mata aka samo shi. Shi ma na maza, daga wurinsu aka samo shi. Ni Abba Abdullahi Garba (Zugson) ba mai bada magani ba ne! Kuma bada magani ba sana’ata ba ce.

Allah Mai Halitta

Bismillahi, na fara da sunan Allah gagara misali, gwani wurin tsara halitta, mai tsara al’amura yadda ya ke so, kuma su tafi yadda ya so ba tare da an samu wani tasgaro ba.

Allah shi ne mai halitta! Kuma babu wani abu mai rai ko maras rai da ba shi ya halicceshi ba. Mu bayin da ya halitta (‘yantattu wato musulmi) gareshi muke bidar taimako ba wurin kowa.

Halittar ubangiji musamman ta dan Adam aba ce mai matukar kyawu da tsaruwar matakin farko. Ba ma iya ta ‘dan Adam ba, kai duk wani abu mai rai da kaga Allah ya halitta in ka tsaya ka yi masa kallon tsanaki, kallo na hankali, to za ka fahimci wani abu, wannan abun shi ne; halittar Allah ko ta ina mai matuka cikar tsari da daidaito ce.

Abin na da matukar ciwo, da cin zuciya, kaga Allah ya tsara halittarsa mu ko ‘yan Adam muna kusheta, ko muna rainata.

Mu aje babin dabbobi da tsuntsaye da nature baki dayanta, mu daga idanuwanmu mu kalli zubin ‘dan Adam, lallai in muka hankalta to za mu ga ashe babu wani abu na ki a jikinsa.

Duk sharar fagen nan da na ke yi, ina yinta ne domin tattaunawa akan body shaming, wadda na tabbata mata da maza da dama suna fama da wannan matsalar.

Abin ya fi zafi a bangaren mata; domin har ana iya kaiwa matakin da ake uzzura musu wasu su birkice su shiga shaye-shayen magunguna wadanda a zahirance illatar da su za su yi, amma saboda mutane sun sako su a gaba, da haka za su sha wadannan magunguna domin kara kiba, rage kiba, kara girman nono, kara girman mazaunai, bleaching domin fatarsu ta yi haske da sauransu.

Shi yasa a kasashen yammacin duniya ake yawan samun kyasa-kyasan sheke kai duk dalilin cin zarafi, aibanta halitta, da sauran cin fuska wadda baki daya bai dace ba.

In har muka ci gaba da haka, to lallai mun zama ‘yan Adam masu ragaita!

Dan Adam Mai Ragaita

Ragaita kam daidai take da rashin daraja. Wasu da dama daga cikin ‘yan‘uwanmu mutane cikinsu taf yake da ragaita, karin abin ban mamaki shi ne; da dama basu san su din suna yi ragaita ba daukarta suke kamar wasa ce (its a joke!).

Tambayoyi irin wadannan tashe suke a injin nema na duniya, wato bleaching creams, kara girman nono, rage girman nono, kara girman mazaunai, karin kiba, rage kiba, rage tumbi da sauransu.

Shin kun san dalilin da yasa suke tashe?

A’a

Na san ba ku sani ba, amma zan sanar da ku.

Saboda madadin mu rinka bai wa masu fama da irin wadannan matsalolin na jiki shawarwari masu amfanarwa (positive advices), a’a, gwara mu rinka zolayarsu, tsokanarsu, yi musu shagube da sauransu.

Hakan shi ke hana da dama daga cikinsu barci, wasu ma cin abinci. Amma fa mu babu ruwanmu (we just don’t care!).

Previous News Next News