Ciwon Sanyi, Illolinsa, Alamominsa, da Maganin Ciwon Sanyi na Maza da na Mata Sadidan

Ciwon Sanyi

Babu wata cuta (wadda ka sani da wadda ba ka sani ba) da Allah Madaukakin Sarki ya saukar ba tare da magani ba.

Sai dai in har ni/ke/kai ne ba mu san maganin nata ba.

Amma dai tabbas, muddin aka tsawwala binciken maganin to za a samo shi, kuma za a waraka.

{tocify} $title={Table of Contents}

Ni ba likita ba ne, ban kuma karanci likitanci ba, saboda haka ban san adadin cututtukan da suke kama ‘dan Adam ba.

Illa iyaka dai na san wadansu daga ciki.

Kuma yau kamar yadda na saba, zan yi binciken kwakwaf domin zakulo muku maganin sanyi na gargajiya da ma na bature.

Ina da yakinin duk abin da za ku karanta a cikin wallafaffen rubutun nan mai inganci ne kuma sahihi domin bincike na gudanar na zakulo muku su.

Ciwon Sanyi

“Za ta iya yiwuwa kai cutar sanyi iri daya kawai ka sani, amma cutar sanyi ta kasu gida goma sha takwas a jikin ‘dan Adam.”

Saboda haka in har ka ce sanyi ne ya kama ka, to gaskiya kai tsaye ba general maganin sanyi za ka nema ba.

A’a

Kana da bukatar ka san takamaiman wanne irin ciwon sanyi ne ya kama ka, za ta iya yiwuwa sanyin mara ne, sanyin mata ne, sanyin kashi ne da sauransu.

Rashin neman sanin ainihin cutar da ke damun mutanenmu hakan ne ke sanya su yi ta shan magani iri-iri amma cuta ta ki ta warke.

Za ta iya yiwuwa magani daban cuta daban kawai su ke yi.

Recommended Reading: Maganin Ulcer Sadidan, na Har Abada, na Musulunci da na Hausa

Ina guje maka fadawa cikin makahon tarkon shan maganin cuta daban, ciwo daban.

Don haka muddin ka tabbatar da sanyi ke damunta, to ka gwada zuwa a gwadaka a asibiti, a tabbatar da wanne irin nau’in sanyi ke damunka, in ya so sai ka zabi irin maganin da ka ke ganin shine mafita a gareka.

In har ka fi gane wa maganin gargajiya, you are good to go, in ko ka fi gani na Bature to kai tsaye likitocin da suka gwada ka za su dora ka a kan maganin da ya fi dacewa da ciwon da ka ke fama da shi.

Illolin Ciwon Sanyi

Kamar yadda na fada a baya, ciwon sanyi ya kasu gida sha takwas. Za mu dauki ciwon sanyi na mara da ciwon sanyi na mata domin yi muku bayani a kansu.

Babu wata cuta wacce bata da illa, sanyin mara da sanyin mata an fi daukar na biyun (sanyin mata) ta hanyar jima’i, yayin da sanyin mara shi ma layinsa ya ke bi, ko da kuwa mutum ba ya yin jima’in.

Sanyi (na mara da mata) cuta ce wacce ba kasafai ta ke nuna tsauraran alamomi ba wadanda za su tayarwa da mutum hankali.

Daga cikin illolin ciwon sanyin mara da na mata akwai;

  • Haifar da raunin ‘da namiji (mazakuta)
  • Lahani ga jaririn da ake raino a ciki (wanda ba a haifa ba)
  • Haifar da karin hadarin rashin haihuwa
  • Yana haifar da wasu nau’ikan cututtukan ciwon daji (Allah ka tsare mu)
  • Yana kuma hana gamsar da abokin jima’i cikin sauki
  • Yana kuma disashar da sha’awar ‘da namiji kai har ma macen.

Ba mu kawo jerin illolin ciwon sanyi domin mu tayar maka da hankali ba, a’a, mun yi haka ne domin sanar da kai irin illolin da cutar sanyi ta ke tattare da.

In har ka yi amanna da cewa, kana dauke da cutar sanyin mara ko na mata, to zan so kai tsaye ka san alamomin ciwon sanyi domin tabbatar da zarginka.

Alamomin Ciwon Sanyi

Tabbas alamomin ciwon sanyi suna da yawa, kuma zan yi iya kokarina domin kawo muku su a takaice.

Ga su nan kamar haka;

  1. Zafin fitsari ko canza launins
  2. Fitar ruwa daga al’aura haka kurum (mai kauri ko wari)
  3. Rikicewar jinin al’ada
  4. Jin zafi yayin saduwa (jima’i)
  5. Jin motsi a cikin farji (kamar wani abu na tafiya
  6. Fitar wani abu kamar dusa-dusa daga farji
  7. Kurajen gaba
  8. Kumburin gaba
  9. Daurewar mara (ga mata) akai-akai ba lokacin jinin al’ada ba
  10. Gaba ya rinka kaikayi

Wadannan alamomi ciwon sanyi guda goma  su ne wadanda muka samo bayan mun gudanar da bincike.

Game da na dayan nan, zafin fitsari, mafi akasarin lokuta rana ce ke sanya zafin fitsari ba sanyi ba.

Sai dai shi kansa sanyin zai iya haifar da hakan.

Maganin Ciwon Sanyi na Maza

Hadin maganin sanyin da za mu kawo na gargajiya ne, kayan hadi ake nema ake hada shi.

Amma kamar yadda muka tabbatar, yana maganin sanyi na maza da na mata kai har ma da na gonoria yana yi.

Ku nemi:

  1. Ku samu namijin goro guda 5
  2. Ku samu citta mai yatsu (ashar) guda 4 ko 5
  3. Ku samu tafarnuwa guda 3 ko 4 
  4. Sai ku samu lemon tsami guda 5
  5. Sannan ku nemi zumanku mai kyau

Bayan kun samu wadannan kayan hadin, abu na gaba sai ku koyi yadda ake hada wannan hadin maganin sanyin.

Yadda Ake Hada Shi

A samu namijin goron nan, da cittar nan, da tafarnuwar nan, sai a yayyankasu kananu sannan a jajjagasu.

Bayan kun gama jajjagasu, sai ku samu lemon tsamin nan ku yayyanka shi har da bawonsa, ku matseshi a cikin tukunya, sai ku zuba har bawon nasa a cikin tukunyar.

Daga nan sai ku kawo jajjagen nan ku zuba a kai, ku zuba ruwa ku tafasashi ya tafasu.

Sai a saukeshi a barshi ya yi sanyi.

Sai a rinka tsiyaya kofi daya da safe, da rana da daddare ana sha.

Amma kafin a sha, a kawo zuma a zuba a ciki saboda ya kashe baurin maganin domin ba lallai ya yi dadi ba.

A shawarce; ku cigaba da sha sau uku a rana har tsawon makonni biyu, Insha Allahu za a samu waraka da yardar Allah.

Maganin Ciwon Sanyi na Mata

Mata iyayenmu, mata ko iyayen gida. Ina tsaka da bincike na ci karo da muhimmin hadin maganin ciwon sanyi na mata wanda musamman domin su aka samar da shi.

Ganin hakan ya sa na ce, kai ba zan tsallake na barshi ba, gwara na kawo musu shi na tabbata zai matukar amfanarsu.

Abubuwan da za ku nema;

  1. ‘Ya‘yan habba (ina ga habbatussauda ake nufi)
  2. Sai ganyen magarya
  3. Miski
  4. Tafarnuwa
  5. Da ‘ya‘yan bagaruwa

Bayan kin tabbatar da kin tanadi wadannan abubuwan sai kuma ki koyi yadda ake hada wannan hadin na maganin ciwon sanyi na mata sadidan.

Yadda Ake Hada Shi

Kafin ki fara da komai, zan so ki wanke tukunyarki, ki zuba ruwa a ciki, sannan ki azata bisa wuta.

Daga nan sai ki kawo wannan tafarnuwar, da ‘ya‘yan bagaruwar, da ‘ya‘yan habbar, da ganyen magaryan nan ki zuba a cikin tunkunyar ki yi ta izata.

Bayan ya tafaso, sai ki kawo miskin nan naki ki zuba a ciki ki barshi ya tafarfasu sosai da sosai. 

Sai ki saukeshi, sannan ki barshi ya 'dan huce ya yi ramai-ramai yadda in har kika diba kika shiga bandaki da shi to za ki iya zama cikin ruwan.

Ba a son ya yi sanyi kalau, ki tabbatar da 'dan zafi-zafinsa kika diba.

Kina diba sai ki zuba a cikin bahon wanka ki kai bandaki, ki zauna a cikin ruwan har sai ya yi sanyi, daga nan sai ki yi wanka da abinki.

Kuma kada ki sake ki yi masa gauraye da ruwan sanyi kafin ki yi wankan.

Insha Allahu muddin ki ka jure yin wannan hadi tare da wanka da shi bayan kin zauna a cikinsa za ki yi bankwana da ciwon sanyi.

Kammalawa

Allah shine abin godiya. Allah mun gode maka. Kuma nan gaba kadan za mu kawo muku nau'ikan wadansu magungunan sanyin na gargajiya wadanda za ku iya hada su da kanku.

Za ku iya yin sharhi a karkashin rubutun nan.

Previous News Next News