Ciwon Basir (Hemorrhoids), Maganin Ciwon Basir, Alamominsa da Hanyoyin Kawar da shi

Maganin Basir
Maganin Basir

Lalurar basir, lalura ce babba wacce tana da bukatar magani sahihi domin a samu sauki ko kuma waraka daga gareta.

Hakikanin gaskiya babu wata cuta wacce ba ta magani, sai dai in har ni / ke ko kai ne ba ka san maganin ba.

Amma muddin aka matsa da bincike, to la shakka, za a samo maganinta wanda in aka gwada cikin sa’a, to za a dace, a kuma samu waraka.

{tocify} $title={Table of Contents}

Kafin na ci gaba da yin bayani, zan fara da yi maka barka da zuwa shafin nan mai albarka.

Yau, zan yi cikakken bayani akan lalurar basir (ciwon basir), da alamominta. 

Kana, zan wallafa magungunanta kala-kala kamo daga kan na gargajiya, na musulunci da kuma na bature.

Ka sani: duk bayanai, magunguna da alamomi (symptoms) na lalurar basir da zan kawo maka a cikin article din nan, zan kawo su ne bayan yin dogon nazari da binciken kwakwaf.

Menene Ciwon Basir (Hemorrhoids)

In aka ce basir, to, ana nufin ciwon kananun jijiyoyi na dubura wadanda suke a bango-da-bangon dubura inda jijijoyiyin ke samar wa da dubura jini don hana ta lalacewa ko bushewa.

Recommended Reading: Ciwon Ulcer, Alamomin Ciwon Ulcer, Da Hanyoyin Magance Ciwon

To, su wadannan kananan jijiyoyin jini suna kumbura ne (kamar an hura balan-balan) sakamakon matsin da suka samu, bayan nan sai su rinka zugi.

Shi kuma zugin shi ne ke sawa ana jin ciwo.

A takaice dai, “Ciwon basir na nufin ciwon kananun jijiyoyin bango-da-bango na dubura wadanda suke samar mata da jini don kar ta lalace ko bushe, dalilin ciwon sai su kumbura su rinka zogi ana jin ciwo.

Yanzu kam ina da yakini a kan cewa mun gama sanin menene ciwon basir (hemorrhoids), to, ya kamata mu san abinda ke kawo shi domin mu kiyaye ko ba yawa.

Shin Me Ke Kawo Ciwon Basir

Kamar yadda matashin likita, mai bincike akan cututtuka da magungunansu, Ibrahim Y. Yusuf ya wallafa, abubuwan da ke kawo ciwon basir sun hadar da;

 1. Zama wuri daya na lokaci mai tsayi (ga direbobi, teloli da sauransu)
 2. Attini (constipation) / ko yawan yin bayan gida mai tauri 
 3. Juna biyu ga mace saboda nauyin da ciki ya yi, in ta je bayi jijiyoyin duburarta na talewa
 4. Kiba sosai na janyo basir
 5. Mutum ya yi yinkurin kasaye duk abin da ke cikinsa, ko kuma ya rinka yin gaggawa yayin da ya je tsuguno
 6. Yawan zawo (gudawa) shi ma na kawo basir
 7. Halayyar kin tashi ayi kashi sanda ake jinsa har kashin ya koma yai concentrating aciki ya zamto mutum yama dena jin alamun zai kashin.
 8. Nannauyar teba ta mazaunai / duwawu
 9. Nakuda
 10. Saduwa ta dubura (walau ga mace ko namiji)

Ba fa iya su kenan ba! Akwai karin wadansu abubuwan da dama da suke kawo ciwon basir. Kuma lallai in har da hali, to, ya kamata a kiyayesu ko a rage yin su.

Kai tsaye za mu gangara kan alamomin ciwon basir, za mu kawo muku su domin in mutum na fama da daya daga cikin wadannan ya nemi magani.

Alamomin Ciwon Basir

Daga cikin alamomin da ke nuna mutum ya kamu da lalurar ciwon basir akwai;

 1. Kumburar dubura
 2. Ko kuma fitar jini (ba tare da an ji zafi ba)
 3. Jiki ya rinka ciwo, ko kuma rashin sake wa
 4. Kaikayin dubura ko bacin rai
 5. Fitan curi ko dunkule (sakamakon kumburara jiyiyoyin jini na dubura) da sauransu.

Ba fa iya su kenan ba! Alamomin ciwon basir na da yawa. Fatanmu dai Allah ya ba wa masu lalurar nan sauki.

Matakan Cutar Ciwon Basir (A likitance)

Lalurar ciwon basir na da tsages dai-dai har hudu kamar yadda Ibrahim Y. Yusuf ya bayyana, kuma in har ya faro daga stage 1 ba a dau mataki ba har ya kai stage 4, to da matsala.

Ga matakan nan;

 • Stage 1: Shine basir din da ake jin zafi ta dubura kuma in an yi kashi akan ga jini ya dan biyo bayan kashin, ko da an shafo duburar ba za a ji komi ba.
 • Stage 2: Shine bayan angama bayan gida akasa hannu za'aji jijiyar ta zazzago ana tabata amma bayan mutum ya wanke kashin da kanta mutum zai ji ta koma.
 • Stage 3: Idan mutum ya gama tsuguno zaiji ta zazzago, kuma koda ya wanke duburar basir din bazai koma ba sai mutum yasa yatsa ya turasa da kansa. Idan ya mayar zaiji shikenan ya bace.
 • Stage 4: Shine mai zazzagowa baya komawa, kuma inkazo maidashi ga zaba, kuma hakanan da kansa zai qara zazzagowa, wato koka mayar sai ya qara saukowa.

Magungunan Rage Zogin Basir na Bature

A likitance, akwai wadansu magunguna a ake siyar wa a kyamis-kyamis wadanda su kan taimaka wurin rage radadin basir.

Akwai irin su;

 1. Hemorrhoidal cream
 2. Topical anesthetic
 3. Anusol da sauransu

Gargadi: kafin ka sayi kowanne irin maganin basir son samu ka tuntubi likitanka ya fada maka wanda zai yi daidai da irin basir din da ke damunka. Kada ka yarda ka rinka abubuwa gaba-gadi.

Kafin mu kawo magungunan basir na gargajiya, na Hausa da na Musulunci, za mu fara da kawo wadansu hanyoyi 

Hanyoyin Warkar da Ciwon Basir (Ba tare da magani ba)

Na san wasu za su cika da mamaki sakamakon jin na ambaci wadansu hanyoyi da ake bi wurin warkar da basir amma kuma ba tare da an sha magani ba.

Sai dai zan so su sani cewa, ba wani abin yin mamaki a cikin wannan lamarin domin abu ne wanda ya ke mai yiwuwa.

Ba zan yi muku dogon surutu ba domin so nake ku matukar amfana da rubutun nan nawa na yau.

Abinci Mai Gina Jiki

Shin ko kun san cewa yawan cin abinci mai gina jiki (irin su ganyayyaki, kayan hatsi, kayan marmari) na matukar taimakawa wurin magance ciwon basir? To in ba ku sani ba, suna taimakawa wurin nika abinci kuma suna wanke ciki.

Bugu da kari, irin wadannan nau’ikan abinci suna matukar taimakawa wurin rage wahalar yin bayan gida.

Haka kuma yawan cin abinci mai maiko, da jan nama na kawo basir. Don haka in da son samu ne ku rage yawan cin su.

Motsa Jiki

Ina daga cikin mutanen da in dai zan yi rubutu game da kiwon lafiya na ke shawartar mutanenmu da su rinka motsa jiki.

Yana da kyau ku rinka motsa jiki kullum, ku kuma rage yawan zama wuri daya ba tare da kun ‘dan mike kun zazzagaya ba.

A zahirance, duk wanda ke motsa jiki kullum to hakan zai kareshi daga cutar basir. In ma yana da ita zai samu sauki da yardar Allah.

Yin Wanka da Ruwan Dumi

Na tabbata da dama daga cikin mazauna birane ba sa iya fita kasuwa ba tare da sun yi wanka da ruwan dumi ba.

To, ina son ku yi sani cewa wannan abin da kuke yi yana da matukar tasiri ga lafiyarku kwarai da gaske.

Duk wanda ya ke yawan yin wanka da ruwan dumi to zai kawar da kaikayin jiki, ciwon jiki da alamun basir.

Hakan zai kasance win-win ne gareshi.

Shan Ruwa Mai Kyau

Za ku ji abin wani bambarakwai, amma magana ta gaskiya yawan shan ruwa mai kyau yana da matukar amfani a jikin ‘dan Adam.

Da farko dai yana wanke hanjin ciki, kana yana taimakawa wurin nika abinci yayin da aka ci shi.

Ga wanda ke son raba hanya da lalurar ciwon basir to a shawarce ya juri shan ruwa mai kyau.

Ka Rinka Ta’ammali da Vitamin C

Da na ce ka rinka ta’ammali da Vitamin C ba wai ina nufin ka rinka samun kwayarsa kana sha ba.

A’a, ina nufin ka na ci da shan duk wadansu nau’ikan kayan abinci na da sha masu dauke da sinadarin.

Kamar su tumatir, lemon tsami, tuffa (Apple), lemon bawo, lettuce, kankana, lemon grass, kabeji, abarba, na'a-na'a da sauransu.

Fa’idar ta’ammali da su shi ne, saboda shi Vitamin C din yana kara wa jijiyoyi lafiya da karko kuma yana taimakawa wurin magance ciwon basir.

Maganin Basir Mai Tsiro

Yayin da nake tsaka da bincike na ci karo da wani maganin basir mai tsiro wanda wani bawan Allah ya bayar da shi.

Ko-da-ya-ke ban san mutumin ba a zahiri, amma duba da yadda mutane ke ta yi masa godiya da sa albarka hakan ya bani kwarin gwuiwar kawo muku shi.

Ku nemi;

 • Danyen sassaken dinya

Yadda Ake Hada Shi

Ku samu sassaken dinya danye, sa’annan ku nemi tukunya ku aza a kan murhu, ku kunna wuta.

Sai ku kawo sassaken nan ku zuba a ciki ku barshi ya tafasa, bayan ya tafasa sai ku debi ruwan maganin ku kawo farin ruwa ku sirka shi daidai misali yadda za ku iya zama a ciki.

Kana ku juye a bahon ku rinka zama ciki na ko da mintuna 30 ne kullum.

Hakika wannan magani yana kone basir mai tsiro cikin gaggawa. Muna fatan Allah ya shige mana gaba.

Maganin Basir na Mata

Wohoho! Masu iyali wadada suke zargin basir ne silar rashin kwazonsu yayin kwanciyar aure, to, sai gareku.

In dai basir ne ya ke rike ma jijiyoyin azzakari, ya rage musu karfi har ta-kai-ta-kawo ba ka iya gamsar da iyalinka, to, sai gareka.

Ka nemi;

 1. Sassaken dinya (mai ‘dan yawa fiye da sauran)
 2. Saiwar sabara
 3. Da saiwar tsada

Yadda Ake Hada Shi

Bayan ka tanadi saiwar sabara, tsada da sassaken dinya busassu, sai ka hada su wuri guda ka dake, sannan ka tankade garin.

Kullum sai ka rinka diban cokali guda na garin maganin ka zuba a cikin ‘dan karamin kofin silba ko tasar silba, sannan ka kawo ruwa kofi daya ka zuba ka dafa.

Bayan ka dafa, sai ka tace ka sha bayan ya yi sanyi. Ka cigaba da yin haka har na tsawon sati biyu.

Da yardar Allah in dai fannin jima’i ne, azzakarinka na baka matsala saboda basir ya yi maka katutu, to, za ka samu sauki.

Maganin Basir Garanti (Na Musulunci)

A lamarin magani babu garanti, sai dai yardar Allah. In Madaukakin Sarki ya lamunce to kowanne irin magani zai iya yi maka ya ki yi wa wani.

Yanzu haka muna da nau’ikan maganin basir na musulunci har guda biyu. Kuma yanzu za mu kawo muku su.

Ku nemi;

 1. Garin habbatus sauda
 2. Garin citta
 3. Garin sassaken dinya

Yadda Ake Hada Shi

Bayan ka tanadi garikan da na lissafo a sama, sai ka fara da diban garin habbatus sauda cokali uku ka zuba a cikin kofi, ka debi kagin sassaken dinyar nan cokali daya shi ma ka zuba a ciki, sai garin citta cokali daya.

Ka zuba ruwa ka gauraya, sai ka rinka shan sa cokali biyu da safe, yamma da daddare.

Ka yi haka na tsawon sati biyu, Insha Allahu za ka ji sauki bangaren basir.

Maganin Basir Kowanne Iri

Kusan kowa na son yin amfani da magani wanda ya ke dakile kowanne bigire na cuta.

Kamar sauran cututtuka, ita ma cutar ciwon basir tana da maganinta wanda ya ke shakundum.

Domin hada wannan magani sai ku nemi;

 1. Lemon tsami guda 3
 2. Tsohuwar tsamiya guda 3
 3. Sai jan gauta guda 3
 4. Barkono guda 5
 5. Sabulun sha kamar girman lemon tsami

Yadda Ake Hada Shi

Bayan ka tanadi wadannan abubuwa biyar da na lissafo, sai ka hadesu wuri guda a cikin mazubi ka jikasu su kwana.

To, kullum ka rinka tsiyayan rabin kofi kana sha, kana kara ruwa a ciki har sai ka ji ya yi salam.

Daga nan sai ka sake jiko.

Amma da yardar Allah in dai ka gwada wannan hadin za ka yi bankwana da basir na dogon lokaci.

Allah ya sa mu dace.

Kammalawa

A cikin dan dogon rubutun nan na yau da na gabatar, na yi bayani dalla-dalla akan lalurar ciwon basir, abinda ke kawo ciwon, alamomi, matakai, hanyoyin kawar da shi da ma maganinsa iri-uri.

Da fatan kun amfana, kada ku manta ku yi share domin sauran al'umma su amfana.

Madogara

Previous News Next News