Wurare 7 da suke saurin Motsa sha'war Mace da Magidanta ba su damu da su ba


Daga Tsangayar Malam Tonga

Da wuya kaji ma'aurata suna zancen wadannan wuraren a yayin da suke zancen motsa sha'awa.

Waɗannan wuraren, wurare ne dake motsa wa mata da maza sha'awar su da zaran anyi hakan yadda ya dace. 

Waɗannan wuraren sun hada da;

Kai

Shafa kan juna ga ma'aurata a lokacin wasannin motsa sha'awa abu ne da yake motsawa mutum sha'awar sa nan take.

Shi yasa maza suke son mace mai gashi, baya ga karin kyau da yake yiwa mata, maza suna son suga suna wasa da gashin matansu a lokutan soyayya.

Haka nan mata suna son shafa kan mazansu wanda wannan shafar na motsawa namiji sha'awar sa.

Sai dai abun takaice ba duk ma'aurata bane sukasan hakan kuma suke amfani da hakan ba.

Haba

Nan ma waje ne da muddin za a yi wa namiji ko mace wasa da shi nan take za a motsa masa ko mata sha'awar sa ko sha'awar ta.

Maza masu baiwa saje ko gemu zasu fahimci matansu suna son yi musu wasa da nan. 

Baya ga dadin da su matan suke ji idan suna taba wa, haka shi ma maigida yana jin dadin dake motsa masa sha'awar sa.

Also Read: Abubuwa 10 da ya kamata ki sani kafin a yi miki aure - Tsangayar Malam Tonga

Suma mata sune son ji mazansu na shafamusu habarsu wajen fuskarsu cikin sanyin rai hade da soyayya. Nan take za a ga mace ta soma lumshe idanuwa.

Kirji

Shima wuri ne dake motsa sha'awa amma ma'aurata suna watsi da shi.

Yiwa mijinki wasa da kirjinsa musamman idan mai gashi a kirjinsa ne yana matukar motsa namiji sha'awa.

Tsakiyar kirjin mace tsakanin nonuwanta wajene shima dake motsawa mata sha'awar su.

 Kada ka taba mata nonuwa. Kawai shafa mata nan ka kura mata idanuwa za ka ga halin da ka tsomata.

Hamata

Nan ma lungune da yake da saurin Motsa sha'awa da ma'aurata suke burus da shi.

Hamata mai gashi ko marashi wajene da idan aka yiwa mutum wasa da shi. Ta hanyar shafa wuje ko lasa nan take yake motsawa mutum sha'awa.

Tafukan Hannu

Ma'aurata bama sa daukansa a matsayin wajene dake cikin jerin wuraren da suke motsawa mutum sha'awa.

Yin wasa da tafukan hannu musamman ma idan aka shafawa tafin hannun man shafawa mai kamshi da santsi.

Kasan Cibiya

Duk mutumin da za a taba masa kasar ciniyarsa da manufa na soyayya sai sha'awar sa ta motsa.

Waje ne da yake da saurin aika sakon sha'awa ga wanda ake da niyar motsa masa. Don haka ma'aurata su kasance suna amfani da wannan wurin domin motsawa juna sha'awa.

Kugu

Shima wajen da yake motsawa mutum sha'awa amma sam ma'aurata hankalinsu baya zuwa nan.

A lokacin da ma'aurata suka rungumi juna, su kasa yatsansu a ramin kugun juna musamman babban yatsa suna shafawa wajen kamar ana tausa. Nan take zasu ji sha'awar su ya motsa.

Waɗannan suna cikin jerin wasu abubuwan dake saurin motsawa mutum sha'awar sa da akasarin ma'aurata basu cika amfani dasu ba a lokutan su na soyayya.

Sai dai ba ana nufin kowa aka masa wasa da wadannan wuraren zai ji ya motsu ba. Abunda zai iya motsawa wani sha'awar sa wani kuwa kashe masa sha'awar zai yi. 

Don haka ma'aurata sai suyi la'akari da wanne yake motsasu kamin suyi amfani da shi.

Previous News Next News