Koyi Yadda Ake Yin Lallen Gam Da Lallen Du-kafa CIkin Sauki

Lallen Gam

Ina da cikakken yakinin cewa duk wanda ka gani ya ziyarci shafin nan to other janda ne, bi ma’ana mace ce walau budurwa, matar aure ko bazawara.

Saboda haka ina mai yi muku barka da zuwa shafin nan namu mai albarka.

{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}

Kuma zan so sanar da ku cewa a cikin post din nan zan yi cikakken bayani game da yadda ake yin lallen gam, kai  za ma ta iya yiwuwa har da bidiyoyi zan tarkato na kawo muku.

Kai imma ta kama har da hotuna.

To, amma kafin mu koyi yadda ake yin shi wagga lalle, me zai hana mu fara da yin karatu akan ita kanta bishiyar lallen da kuma amfaninta ta sassa daban-dabam.

Menene Lalle

Lalli ko lalle wata bishiya ce wacce matan Hausawa ke yin amfani da ganyayenta musamman ta hanyar dakawa su kwaba su yi kwalliya a lokutan suna, aure, bukukuwa ko dai haka nan.

Mun kawo ma’anar lalle, amma ba muna nufin lallen da ake yin zanenin kafa, hannu da shi ba wato dying. 

Muna nufin lalle na gargajiya irin wanda in aka yi kunshi da shi za ku ga kafa ko hannu sun yi ja din nan.

Lalle ta Fuskar Ado

Yanzu haka mafi akasarin mata sun daina amfani da lallen da na kawo ma’anarsa a sama, wato lalle na gargajiya.

Illa iyaka dai mun sani sun koma amfani da na sayarwa wanda shi completely ma hade-hade ne kuma ana kiranda sa da “dying” a turance.

Also Read: Mecece Shagwaba da Yadda Ake Yin Shagwaba Ga Saurayi Ko Maigida

Har ila yau kamar yadda bincike ya bayyana, an tabbatar da cewa sau tari wannan lallen dying din ka iya illatar da fata sakamakon wasu sinadarai da yake dauke da su, to amma dai ba ka raba mutum da abinda yake so ba.

Inda su kuwa mata wadanda har yanzu ke amfani da asalin lalle na gargaji ‘yammatan zamani ke musu kallo irin tamkar gidadawan nan ne ko kuma kauyawa.

Allah shi kyauta.

Amfanin Lalle Na Gargajiya

Ko-da-ya-ke na ga yanzu haka an samu cigaban da shi asalin lalle na gargajiya mata musamman masu ‘dan hasken fata da ma bakaken na yin amfani da shi wurin yin zanuka masu ‘dan karen kyau a tafukan bayan hannunsu da tafukan hannunsu har ma da kafafunsu.

Amma a zahirin gaskiya kuma a addinance, an ce duk wacce ta juri yin kunshi na lallen gargajiya to mala’ikun rahama na ziyartar gidanta kullum.

Haka kuma bayan haka, lallen gargajiya na taimakawa wurin kare macen da ke yinsa daga miyagun aljannu domin sun matukar tsani ganyen lalle.

Kai in da za ku nemi ciyawar aniya makomiya sai ku daka da ganyen lalle sai a rinka shafawa to zai karya duk wani sihiri da ke jikinku ya ku ‘yan‘uwa mata.

Kuma in baku sani ba, shi fa lallen nan na gargajiya na da matukar amfani wurin magance ciwon fata. Kai lallen fa yana zuke duk cututtukan da ke kafa kai masu ciwon hannu ma na iya yin lalle a hannun kuma cikin ikon Allah ana samun sauki

Sa’annan yana taimakawa wurin tabbatarwa da mace ni’imar da ke jikinta.

Lalle na maganin dattin ciki, in da za ki samu ganyen lallenki ki tafasa shi, ki tace ruwan sai ki rinka sha cokali daya da safe to zai rinka wanko dukkanin dattin da ke cikin cikinki. Amma fa mace mai juna biyu kada ta sha!

Lalle na maganin infection na mata irin kaikayin gaba ko dai makamantasu, in da za ki tafasa ganyen lalle ki rinka zama a cikin ruwan kullum na tsawon sati biyu to ina da yakinin zai magance miki infection din da ke damun al’aurarki.

Lalle na maganin warin kashi. 

Yadda Ake Yin Lallen Gam

Lalle dai ya kasu gida biyu, akwai lallen gam da kuma lallen dayin. Kuma bi’izinillahi ta’alah zan yi muku cikaken bayani akan yadda ake yin lallen gam.

Na samu cikakken bayanin nan daga wurin mahaifiyata wacce na tambaya ta yi min dalla-dallan bayani a kan yadda ake yin lallen gam da na dayin.

Da farko dai ka samu farantin silba da rezarka mai kyau sabuwa sannan ka hada da bakin gam kwallo daya.

Sai ka dayi gam dinku ku nana a bayan farantin, sai ka saka reza ka yayyanka ko kawata irin kunshi da kuke son yi a jikin wannan gam din da ku ka manna a jikin farantin.

Bayan kun yayyaka sai ka rinka dayar gam din, kuna likawa a kafarka domin ya fitar da nau’ink kwalliyar da kuke son yi wa kafarku.

Iya inda kofar yankan adon gam din take, to iya nan kunshin zai kama. 

Bayan kun gama mammanna gam din a tudun kafarku, hannunku da duk inda kuke son kwalliyar kunshin ta fito sai kuma nemo gishirin kunshi da toka ku kwaba.

Bayan kun kwaba sai ku debi kwababbiyar tokar nan ku na bi duk ramin kwalliyar da ke jikin gam din kafarku da hannunku kuna lallabewa har sai kun ga kun kammala.

To sai ku baki ya bushi sannan ku cire ku wanke kafarku.

Shi irin wannan kunshin ya danganta da irin fikira da salon mai yinsa, in dai ke gwana ce wurin iya tsara kwalliyar fulawa to za ki iya yin kunshin gam mai dan karen kyau.

Kamar yadda na samu cikakken bayani, shi irin wannan kunshin ana kiransa da dugwal.

Yadda Ake Yin Lallen Du-kafa

Shi ne lallen da a baya na bayyana muku cewa mata zamani sun daina shi, sun fi yin lallen gam wanda kafa za ta yi baki kuma ta yi ja.

Da farko dai ku samu lallenku ku daka shi sai ku tankade shi da rariya, bayan kun tankade sai ku nemi mazubi ku zuba garin lallen sa’annan ku kawo ruwa ku zuba ku kwaba shi.

Daga nan sai ku nemi ledar sikari wadatacciya wacce za ta daure muku dukkanin kafafunku guda biyu.

Sai ku rinka lakutar lallen nan kuna shafawa a saman tudun kafarku (iya ma’alawanta) har sai kun zageyeshi da kwababben lallen kun rufe kafar ruf.

Sa’annan sai ku kawo ledar nan ku rufe kafarku da ita, sai kuma ku kawo tsumma wanda za ku daure kafar bayan kun sanya ledar. Fata dai tsumman wadatacce ne.

Dalilin sanya tsumma a yi wa kafa tamarkiya shi ne: don kafa kuna tafiya ledar ta fita.

In kuna son lallen naku ya jima bai goge ba, za ku iya yinsa da daddare ya kwana, to in kuka yi haka zai yi sati biyu yana nan garau.

In kuma sharp-sharp kuke so, awanni 3 da daurashi ma zaku iya sincewa, sai ku wanke kafarku za ku ga ta yi ja.

Haka kuma in kuna son wani wurin ya yi baki a kafar taku (ma’ana ba iya ja ba) sai ku siyo gishirin kunshi ku nemi toka mai kyau fara sai ku tankadeta da rariya sannan ku kawo gishirin kunshin nan ku saka a tona.

Daga nan sai ku kawo ruwa ku zuba ku tona, amma kada ya yi ruwa sosai. To bayan kun tabbatar ya kwabu sai ku debi wannan kwababbiyar toka ku yi ado da ita a kafarku.

Duk inda kuke son bakin ya bayyana sai ku reda kwababbiyar tokar nan, ku barta ta bushe sannan sai ku wanke kafar taku.

Wannan shine takaitaccen bayani akan yadda ake yin lallen du-kafa wanda wasu ke kiransa da lallen gargajiya.

Kammalawa

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah bisa nasarar da muka samu wurin kammala bayanin nan akan yadda ake yin lallen gam da kuma lallen du kafa.

Kusan dukkanin bayanin da ya kamata mu yi shi, mun yi iya kokarinmu mun yi shi. 

Fatan zai amfanar da ku.

Allah ya kara wa Annabi Daraja.

Previous News Next News