Yanzu haka ana garkuwa da mutane akan kudin da bai kai ₦30,000 ba a mazabata – Dan majalisa

Amobi Ogar


Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Isuikwuato da Umunneochi da ke jihar Abia, kudu maso gabashin Najeriya, Amobi Ogar, ya ce yanzu hakan ana garkuwa da mutane akan kudin da bai kai 30,000 ba a mazabarsa.

Mista Ogar ya yi tir da yadda ake samun yawaitar laifuka na garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami a kananan hukumomin da ya ke wakilta a tarayya, inda ya kara da cewa ana zuwa har gidan mutane ana daukesu don neman kudin fansar da bai kai N30,000 ba.

Kamar yadda DailyTrust ta ruwaito, dan majalissar na jam’iyyar Labour Party, a ranar Alhamis bayan gabatar da kudirin kawo dauki ga yankin nasa a zauren majalisar, ya ce babbar manufar gwamnati ita ce kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa. 

Also Read: Katsina: ‘Yan ta’adda biyu sun gamu da ajalinsu a hannun ‘yan Sanda, an kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su

“A yau, na gabatar da kudiri kan hare-haren da ake kai wa jama’ata (a mazabarmu). Satar mutane ya zama tamkar sana’ar sayar da kosai (akara) a mazaba ta.

“Kusan kowace rana ana garkuwa da mutane. Ba daya, biyu ko uku ba. Har ya zuwa yanzu su (masu garkuwa da mutane) suna zuwa gidajen mutane don daukar su a matsayin kudin fansa N50,000, N30,000.

“Yanzu babban lamari ne a gare ni in motsa shi a kasan gidan domin ‘yan Najeriya su ji. Kamar yadda nake magana, da yawa daga cikin mutanen kauyen sun gudu daga gidajensu, har ma iyayenmu mata ba sa zuwa gonaki,” inji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa, Majalisar Wakilai a lokacin da ta amince da kudirin Ogar, ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya umarci dukkan jami’an tsaro da su tabbatar da tsaro a kewayen Kasuwar Shanu da ke Lokpanta a kan babbar hanyar Enugu zuwa Port Harcourt, titin Uturu-Okigwe, titin Ihube-Isuochi. Junction ABSU-Akara Road; Titin Uturu-Afikpo, titin Umuaku-Umunze da titin Awgu-Ishiagu da kewaye inda masu garkuwa da mutane suka komar mafakarsu.

Majalisar ta umurci babban hafsan sojin kasa, Sufeto Janar na ‘yan sanda da kuma kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya da su kafa wata tawagar hadin gwiwa da za ta rika aikin sintiri a gonaki da dazuzzuka domin kakkabe masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da duk wani mai aikata laifuka a kowane bangare na kananan hukumomin Isuikwuato da Umunneochi na jihar Abia.

Previous News Next News