Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya kaddamar da tsarin ilimi kyauta sakamakon cire tallafin man fetur

Agbu Kefas da Dalibai


Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya kaddamar da tsarin ilimi kyauta tun daga firamare har zuwa sakandare a jiharsa.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara makarantar firamare ta Ebenezer da ke Wukari a ranar Juma’a.

A cewarsa, daga zangon karatu na gaba, makarantun firamare da sakandare a jihar Taraba za su kasance kyauta (an daina biyan kudin makaranta).

Ya kuma jaddda cewa hakkin gwamnati ne ta dauki nauyin dawainiyar makaranta baki daya, don haka bai kamata dalibai su rika biyan wadansu kudade ba.

Also Read: Gwamna Kefas yayi sha alkawarin magance matsalar rashin tsaro a Taraba

Ya ce baya ga cika alkawarin yakin neman zabe, wahalhalun da aka shiga dalilin cire tallafin man fetur ya sa daukar matakin ya zama wajibi.

A baya dai gwamnan ya rage kudaden shiga jami’o’i da kashi 50 cikin 100 domin rage wahalhalun da kasar ke ciki.

Da yawa daga cikin daliban Jami’ar sun bayyana farin cikin su da wannan ci gaban da aka samu, inda suka ce rage kudaden zai kara inganta rayuwarsu.

Previous News Next News