Yadda za ki tsaftace soyayyarki ba tare da kin cutu ba

Kyakkyawa

Shahararren malamin nan na Tsangayar Tonga, wato Malam Abdul Tonga ya bada bayanai akan wadansu hanyoyi da mace za ta bi domin tsaftace soyayyarta ba tare da ta cutu ba.

  1. Kada ki saka saurayi a ranki a farkon soyayyar ku.
  2. Kada Kiyi sauri sake wa saurayi soyayyar ki ba tare da kun samu fahimtar  matsayin soyayyar taku ba.
  3. Kada ki kallafa soyayyar saurayi ba tare da ya gabatar da kansa a gaban ma gabata ba.
  4. Kada ki zake a soyayyar babu lokacin da aka tsayar na yin aure.
  5. Kada ki nunawa saurayinki bazaki iya rayuwa ba idan baki aureshi ba.
  6. Kada ki nunawa saurayinki kinfi sonshi da kanki
  7. Kada ki nunawa saurayi kina iya yin komai akan soyayyarsa
  8. Kada ki nunawa saurayi yafi kowa mahimmanci a wajenki
  9. Kada ki bari saurayi ya fahimci ki baki kula kowa sai ke koda kuwa hakan ne wanda hakan ya kuma dace.
  10. Kada ki kasa cusawa saurayinki shakkun zai iya rasa ki idan har bada gaske yake ba.

Akwai mai tambaya ko neman karin bayani?

Previous News Next News