Menene So? Shin Menene Soyayya

Menene So

Shi duk wanda ya fada cikin kogin soyayya, to, ya zama wajibi a tausaya masa domin ya bude wani sabon babi ne a rayuwarsa.

Yau, da yardar Allah za mu yi bayani akan menene so, ya yake, kuma ta yaya ake gane wani ko wata yana cikin yanayin soyayya.

A cikin dukkan cututtukan da Allah ya halitta musamman na zuciya, babu mai azabtarwar cutar ciwon so in har aka samu akasi.

Shi ko akasi ya fi kure, domin kure a kan gyara shi, amma akasi sai dai gyaran Allah.

Kalmar So

Ita kalmar so tana nufin a so wani abu, walau mutum, abin hawa, sutura, kudi, da sauransu.

A nan, abinda muke nufi da kalmar so shi ne son wani abu (ko ma wanne iri ne).

Menene So

"So shi ne ginshikin rayuwa, muna fara so ne tun ba mu san menene shi ba. Kafin a zo matakin so tsakanin sauraya da budurwa, muna fara so tun daga kan iyayenmu da 'yan'uwanmu da abokanmu."

Kazalika, darsuwa wani shauki game da wata ko wani ka iya zama so ko da kuwa so ne na dan lokaci.

Soyayya Rayuwa

Wani sashe ne wanda muka bude da zai rinka tattaunawa akan soyayya, rayuwar aure da zamantakewa, da kuma saduwar aure.

Previous News Next News