Yadda Ake Tsara Budurwa da Sace Zuciyarta

Budurwa
Budurwa

Babu shakka mace na da wuyar sha’ani muddin ba a gano lagonta ba, amma daga lokacin da aka gano lagonta shi kenan sai kuma a fahimci ai saukin sha’ani gareta.

Haka su ma maza da dama daga cikinsu akwai su da wuyar lamari da ganewa.

Akwai tarin hanyoyin da ake bi wurin tsara budurwa, za ma ta iya yiwuwa ka san mafi akasarinsu, kawai dai ba ka taba gwadawa ba ne, ko kuma kana shakkar gwadawa.

{tocify} $title{Table of Contents}

Zamani ya zo da wani irin juyin-juya-hali ta kowacce irin fuska, abin kuma har cikin soyayya ya shiga ciki.

Wadansu mutanen har yanzu sun yi matukar amanna da cewa, soyayya ta gaskiya (wacce ba don kudi ake yinta ba) har yanzu tana raye a ban kasa.

Yayin da kaso mafi yawa cikin mutane ke ganin soyayya ta tsakani da Allah yanzu sai daidaiku ke dacewa da ita, amma muddin kana da wuri to ka fi masu wuraren zuwa dace.

Ba zan yi mamaki ba, in har kowanne tsagi na wadannan nau’ikan mutane ya tsaya a matsayarsa.

Domin kowa da ra’ayinsa, kuma mu ganau ne a fannin soyayya ba jiyau ba.

Wacece Budurwa

“Budurwa ita ce yarinya mace wadda ta haura shekara 15, nonuwa suka fara dinko kai daga kirjinta ko suka rika suka fito, kuma ba ta taba aure ba, ba kuma ta san namiji ba (in ma ta sanshi a waje, muddin ba ta taba aure ba, a iya kiranta budurwa).” 

Shin Akwai So na Gaskiya Har Yanzu

Kwarai da gaske soyayya ta gaskiya wacce ake yinta tsakanin ruhi-da-ruhi har yanzu akwai ta.

Sai dai daidaiku ne daga cikin mutane ke yin dace da samun irin wannan soyayyar.

Kuma tana matukar wahalar da masu yinta.

Yadda Ake Tsara Budurwa

A nawa tunanin, tsari da kuma sace zuciyar budurwa kusan abu daya suke nufi. 

Amma, shi tsara budurwa na bukatar iya kalaman soyayya masu matukar ratsa zuciya, da kuma dakewar zuciyar iya tunkarar wacce ake so.

In har da hali, ka hada da ‘yar karya-karya ba laifi ba ne, ka bayyana wa mace irin son da ka ke mata cikin tausasa murya.

Saboda kana son mace, kada ka tsaya ta rinka wankarka, ko kuma ta mayar da kai garan kauye wanda bai san me ya ke yi ba.

Also Read: Yadda Zaki Yi Dace Auren Namiji Mai Kudi Ko Matsayi

Ka rinka kyautata mata, domin zuciya na son mai kyautata mata, kuma ka kasance cikin tsafta a kowanne lokaci.

Har ila yau, tsara budurwa ba ya wahala in dai ka yi nasarar yi mata magana ta tsaya ta saurareka muddin kana da bakin maganar.

Tsari fa ko a ina ne, ba a iya fagen soyayya ba, zance ne daki-daki mai ma’ana.

Don haka, sai ka tanadi kalamai na musamman domin tsara wacce ka ke so.

Yadda Ake Sace Zuciyar Budurwa

Kai fa ba barawo ba ne, saboda haka ba na tunanin akwai wata hanya wacce za ka sace wa budurwa zuciya.

Illa iyaka dai, za ta fada kogin soyayyarka in har ka yi iya iyawarka wurin bin wadannan hanyoyin guda takwas da zan jero maka yanzu.

Tsari

A nan tsarin da nake nufi shi ne; tsari na sanin ciwon kai, sanin ya kamata, rashin kan gado da kuma tsarin rayuwa mai kyau ba na magana ba.

Mace na son yin mu’amala da namiji wanda ya ke mai tsari, komai nasa a tsare.

Hakika, da za ka yi kokari ka fara tsara rayuwarka, da mu’amalaka (da maza da mata) lallai ko da duk wacce ta yi nasarar samun soyayyarka ta matukar dace.

Kyau da Kwalliya

Kamar yadda yatsunmu ba su kasance daya ba, to haka kyawunmu, dirinmu da zubin halittarmu ba su zama daya ba.

Wadansu matan na son yin soyayya ko tsayawa da saurayi ‘dan gayu, kyakkyawa (daidai gwargwado har ma da fiye da haka) wanda ya san wanka da kwalliya.

Shi yasa sau tari za ka ga mata na yin soyayya da saurayi. Ka rasa me yasa, in ka yi duba da kyau, za ka ga ko dai yana da tsari, ko yana da kyau ga iya kwalliya kamar dawisu.

So dai kowa ya sani makaho ne, abinda ya yi maka, sai ka ga bai yi mini ba.

Kalamai

Yana da matukar muhimmanci namiji ya iya kalaman soyayya masu zafi, wadanda za su rinka kwantarwa da mace hankali, su sanyaya mata rai, su kuma sanya kaunarka cikin zuciyarta.

Akwai samari da dama wadanda dalilin rashin iya kalamai masu dadi ya sanya suka rasa soyayyarsu (wani ya musu kwace).

Shi yasa ya kamata ka iya kalaman soyayya, ka nakalcesu yadda ya kamata.

Kulawa da Kirki

Zuciya na son mai kyautata mata, don haka yana da matukar amfani ka rinka kulawa da budurwarka yadda yakamata.

Ka rinka yi mata abubuwa wadanda za su rinka sa yana ganin kirkinka.

Kulawa ta hadar da takaita chat ta WhatApp da Call, ku rinka haduwa da yammaci kuna zantawa baki-da-baki.

Kana yi mata murmushi mai cike da alkawari da kauna, ita ma tana yi maka.

Sakamakon haka za ta rinka ganin kana kulawa da ita kwarai da gaske, madadin ka uzzura mata da chat a WhatsApp.

Barkwanci

In da son samu ne, kada ka rinka yi wa budurwarka barkwanci kadai yayin da kuke yi waya ko chat.

Duk lokacin da ka je wurinta domin ku yi hirar soyayya, ka rinka ‘dan takalarta da barkwanci, kuna yin raha.

Hakan na matukar kara dankon soyayya.

Kyautatawa

Kyautatawa na nufin yin kyauta. 

Akwai mazan da Allah ya halitta da muguwar kiwatacciyar rowa na Innalillahi.

Haka kuma akwai matan da su ma halinsu daya da mazan wurin rowa, da kwadayin tsiya.

Ya kamata, kai a matsayinka na namiji ka rinka yawan kyautatawa budurwarka akai-akai.

Kamar su kyautar kudi in ka samu dama, da ‘yan abubuwa dai haka. Kai duk abinda ka san zai sanya farin ciki muddin ka siyo mata shi ko kuma ka bata shi, to ka yi, saboda soyayyarka ta kara damke zuciyarta.

Ke kuma, saboda ya saba baki, hakan ba shi zai sa ki matse hannunki gam ba, sai dai ki karba amma ba ki bayarwa ba.

Ki rinka yi wa saurayinki ‘yan kananun kyaututtuka, hakan zai sanyan ya ji a ransa cewa, eh lallai kina kaunarsa kuma ke din ta daban ce.

Previous News Next News