Tarihin Rayuwar Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon (Cikakke)

Hadiza Aliyu Gabon
Hadiza Aliyu Gabon


Babu wani matashin Bahaushe da ke zaune a Arewacin Najeriya kai har ma da kudanci, da sauran kasashen yammacin Afrika wanda bai san wannan jaruma ba.

Sakamakon ta jima a masana’antar shirya finafinai da Kannywood ana damawa da ita.

A kalla, ta shafe sama da shekaru 10 tana fitowa a cikin finafinan Hausa.

Sannan ta fito a cikin finafinai masu tarin yawa, tun daga kan cikakkun finafinai (movies) zuwa shirye-shirye masu dogon zango (series), zuwa shirinta na kankin kanta (Gabon’s Talk Show).

Bugu-da-kari, mafi akasarin jaruman Kannywood asalinsu ba ‘yan Kano ba ne, amma dalilin jarumtakarsu yanzu basu da wani gari sama da Kano, matattarar Kannywod.

A yau, za mu kawo muku cikakken tarihin jaruma Hadiza Aliyu Gabon (Tani a shirin Gidan Badamasi).

Wacece Hadiza Gabon

Hadiza Aliyu dai shahararriyar jaruma ce a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood wacce ke da babban reshenta a jihar Kano, Najeriya. An kuma fi saninta da suna Hadiza Gabon.

Ita ce wacce ta kafa Hag Foundation, tana aikin jin kai da taimakon marasa galihu lokaci-zuwa-lokaci.

Kazalika, jakadiya ce ta wadansu manyan kamfanunuwa ciki har da MTN Nigeria, da Indomie’

Haka kuma ita ke shirya shirin da ake tambayar ka-ci-uwaka ga fitattun mutane da manyan jarumai, wato Gabon Talk Show.

Salsala

Hadiza dai ‘ya ce ga Malam Aliyu, shi ko mutumin Libreville ne da ke jamhuriyar Gabon.

Mahaifiyarta wacce aka sakaya sunanta, bafulatanar jihar Adamawa, Najeriya ce.

Haihuwa

An haifi Hadiza Aliyu a ranar 1 ga watan yuni, 1989 a garin Libreville da ke jamhuriyar Gabon.

Yanzu haka, a shekarar 2023, tana da shekara 34 cif a duniya.

Kamar yadda muka zayyano a baya, an haifi Hadiza a Libreville, sai dai ta dawo Najeriya sakamakon wadansu dalilai. 

Daga cikin dalilan akwai; fara sana’ar fim da kuma kara karatu.

Ilimi

Hadiza Aliyu ta yi makarantar firamare da sakandire a kasarta ta haihuwa, sannan ta rubutu jarabawar A-Level (mai kama da WAEC ko NECO) da muradin son zama lauya.

A jami’a a can kasar Gabon ta zabi lauyanci a matsayin kwas din da za ta karanta, ta kuma fara karatun sai dai wadansu kalubalalluka da suka dabaibaye karatun su suka sa dole ta aje karatun ba tare da ta kammala ba.

Bayan ta dakata ta karatun jami’a, sai ta shiga wata makarantar ta yi diploma a harshen Faransanci.

Sannan daga baya, sai ta zama Malamar Faransanci a wata makaranta ta sirri (private school).

Iyali

Hadiza Aliyu na da diyarta daya wacce ta haifa. Amma a binciken da muka gudanar, har yanzu ba ta da aure.

Shahara

Jaruma na daya daga cikin shahararrun jarumai mata na Kannywood, kuma shahararta ta karade gida Najeriya da kasashen yammacin Afrika da dama irin su Nijar Kamaru, Chadi, Côte D'Ivoire, Benin, Togo da sauransu.

A baya tauraruwarta ta matukar haska lokacin da ake tsaka da ganiyar yin finafinan CD, cikin ikon Allah har yanzu sunanta bai disashe ba.

Sana’ar Fim

Ba ta dade da shigowa jihar Adamawa ba daga jamhuriyar Gabon jarumar ta shiga masana’antar Kannywood.

Dan’uwanta shi ne wanda ya rakata Kaduna daga Adamawa yayin da ta ke sha’awar shiga fim.

Sannan ta samu nasarar ganawa da fitaccen jarumin nan, Ali Nuhu Mohammed, ta kuma nemi taimakonsa don ya bata dama ta zama ‘yar fim.

A shekarar 2009, Ali Nuhu ya santa jarumar a fim dinta na farko, Artabu.

Da kuma taimakonsa shi da Aminu Shariff (Momo), ta samu shiga sosai a masana’antar, har ta kai matakin zama daya daga cikin manyan jarumai mata na Kannywood.

A yanzu haka, tana sahun gaba a cikin shahararrun jarumai mata na Kannywood.

Bugu-da-kari, sakamakon yadda kusan kowanne lokaci ta ke fitowa cikin sutura da al’adar Hausawa a cikin finafinan da ta ke, hakan ya sa mata da dama ke daukarta a matsayin abar koyi.

Finafinai

Daga shekarar 2009 zuwa yau, Hadiza Aliyu Gabon ta fito a cikin finafinai masu tarin yawa.

Daga cikinsu akwai;

  1. Artabu
  2. Basaja
  3. Indon Kauye
  4. Umarnin Uwa
  5. Hauwa Kulu da sauransu.

Akwai kuma finafinai masu dogon zango (Series) da ta fito, daga cikin na kwana-kwanan nan akwai;

  1. Gidan Badamasi
  2. Sai Na Auri Hadiza Gabon da sauransu.

Jakadanci

Jarumar ta yi jakadanci da kamfanunuwa da dama, wadansu har yanzu ita jakada ce, wasu kuma kwantiraginta ya kare.

Daga cikinsu akwai irin su Dangote Classic Seasoning, MTN Nigeria, Kamfanin Indomie da sauransu.

Taimako

Kamar yadda aka wallafa a Wikipedia, “A shekara ta 2016, Hadiza ta kafa ƙungiyar agaji mai suna HAG Foundation Da nufin inganta rayuwar talakawa ta hanyar samar da taimako a bangarorin ilimi da kiwon lafiya gami da wadatar abinci. Ta zama daya daga cikin ‘yan wasa mata na farko a tarihin Kannywood da ta gabatar da irin wannan taimakon jin kai.

“A watan Maris na shekara ta 2016, ta ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke cikin jihar Kano inda ta ba da gudummawar kayayyakin abinci, kayan masaka da sauran kayan masarufi da mazauna sansanin suke bukata saboda rikicin arewacin Najeriya.

Lamban Yabo

Hadiza Aliyu Gabon ta samu lambobin girmamawa da kyaututtukan girmamawa da yawa.

Previous News Next News