Shin Mutum na da bukatar gyara (Shan maganin karfin maza) don zai yi aure? Binciken Masana

Daga Dr. Ibrahim Y. Yusuf

Daga cikin abinda kesa rubutuna game da lafiya zamantowa na daban shine; idan zan bayani game da lafiya bawai journals din mu na medicine kurum zan hausantar ma dasu kai tsaye ba.., A'ah ina haɗa bayanin ne da abinda yake faruwa a zahiri, wanda nagani da idona cikin al'ummar mu' game da larurar dana ɗauko bayaninta, Infact wasu marasa lafiyar nine likitan dake basu kulawa da kaina....

Wanda daga nan ne kuma sai na qara da sauran bayanan da suka fito daga sauran masana. Wanda inka tafi akan kai A'a ga abinda ka gani a Google wannan kai ta shafa. 

Zan so naja hankalin mu game da wani muhimmin al'amari dake faruwa na baiwa Samari ko Matasa da aurensu yazo dab shawarar shan maganin karfin Maza. Zanyi jan hankalin ne ganin yadda abin ya kai ga fara jawoma matasan mu mutuwar tsaye, wanda kuma aqalla na sami cases huɗu kenan cikin wata guda kan matsalar, wanda na tabbatar a sauran asibitocin mu na Nigeria suma suna samun masu matsalar dakan je musu. 

Masu cikakken hankali tare da nazartar al'amura cikin mu a yau zasu iya gane ko rubutu ne a media inya zamto an sirka yasashshen zance ko Batsa ciki yafi jan hankalin mutane, anfi tururuwa kansa.

Wannan ke nuna irin yadda mutane suke baiwa al'amarin sha'awa muhimmanci a yau. Wanda abin har ya wuce mizanin lafiyayyen hankali.

A kwanakin da suka gabata mun sami wani mara lafiya da aka kawo asibiti ta emergency da wata matsala da muke cewa "FRIYAFIZIM" Wato miƙewar alƙalami yaƙi kwanciya, komi irin ƙoƙarin ganin ya kwanta ɗin da za ai kuwa bazai ba, kuma in aka matsa ma tsab zai karye. 

Shi namiji gabansa bai miƙewa tsaye cak ya sami erection face sai idan jini ya kwaronyo ya cika jijiyoyin azzakarin. Wanda idan jinin ya cika jijiyoyin taf shine gaban zai miƙe tsaye cir ai abinda za ai, shi kuma wannan jinin yana shiga ne ta jijiyar ATIRI (artery) tare da fita ta cikin jijiyar Ben (Vein) a guje batare da jinkiri ba, continuous circulation.

Toh amma idan ya zamto jinin ya shiga ATIRI amma hanya ta kulle ya kasa yin gaba ko baya zuwa Vein balle ya fita to shine azzakari zai kasance tsaye cak, ya ɗau ɗumi, ko me mutum zai abin bazai taɓa kwanciya ba wato friyafizim [Priapism] kenan da nace.

Wanda shi dama maganin ƙarin karfin maza aikin da yake yi shine buɗe jijiyoyin jinin azzakari su tale, su cika dam da jini don ya zamto ansami erection tare da qarawa zuciya gudu.

Babbar damuwar kamar yadda na faɗa a baya ita ce; a yau zaka sami matasa zarar mutum zai aure to daga cikin abokai zaka ga wasu na kokarin bashi shawara tare da son gamsar dashi cewa lallai fa yana bukatar shan maganin ƙara kuzari wajen jima'i... Saboda da yawa sun jahilci al'amarin jima'i, wasu ma. Basu da auren ma, ko su riƙa nuna cewa mutum bazai yi mutunci gun Matarsa ba inba wannan.

A gaskiya wannan muguwar shawara ce kuma ina ƙalubalantar duk me dora mutane kan irin wannan muguwar shawarar da sunan taimako, kuma ya dace mutum yaji tsoron Allah koda kudi zamu nema to kada mu zamto masu saka rayuwar mutane cikin hatsari ta yadda kudin kurum muke hange, domin abin na neman zama kamar wani normal alhalin IS NOT Normal.

Domin da magana ta fatar baki kacal kana iya dora mutum kan abinda zai iya halaka wanda in shi bai gane ya dauki mataki ba toh zaku haɗu a gaban ubangiji. 

Shi wannan patient din nawa irin tsutsayin da ya haɗu dashi kenan bayan da ya biyewa gurguwar shawarar abokai, suka samo masa tare da sanya shi shan maganin a daren ranar daurin aurensa, inda karshe ya sami firiyafizm, gabansa ya kasance miƙe yaqi kwanciya tsawon awonni ashirin da biyu, kuma yaqi tunanin zuwa asibiti farko, ya je ya sami wanda ya bashi shawarar akan abinda ya faru amma sam sun rasa ma tayama zasu taimaka masa, domin iya abinda suka sani shine in ansha za'a sami mikewa gaba ko anyi release zai saɓi zarce Amma me ka iya biyo baya sam basu san komi ba.

Kurum nuna masa ya koma ga iyali suke ai Normal ne sha'awar sa ce bata karye ba, alhalin duk ya gama yiwa yar mutane rauni, tun ana abu na daɗi ya koma azaba, haka ya zauna tun alƙalamin bai fara zafi ba har ya fara... Wanda saida ya fara fita hayyacinsa, yaji ba sarki sai Allah sannan ya nemi san uwansa aka kawo asibiti a jigace.

Nan mukai tambayoyin da suka dace don sanin makamar fara aiki, a gaggauce muka fara ƙokarin ganin yadda zamu taimake sa domin a awoyin da ya dauka munsan gaban na iya mutuwa, Tunda gashi ya fara fita daga hayyacinsa saboda azaba.

Kai tsaye muka zira allurai jiki muka fara kokarin zuqe jinin da ya zamto trapped cikin azzakarin, tare da flushing da ruwa sama da liter 1 da rabi, da sauran allurai, wanda bayan shafe kusan awa guda, muka fara samun nasarar kwantar da ita, saide bayan baifi minti 20 ba da gama wannan wahalar abar ta qara mikewa tsaye wato Recurrent stuttering priapism... A nan ne fa ya zamto bamu da zaɓi sama da musa wuƙar mu ta fiɗa "surgical blades" mu lumata ciki kan kaciyarsa don samun kwaranyowar jini sosai, haka mukai ta fama kafin Allah ya bamu sa'ar kwantar da ita, wajen sama da awa 2 muna aikin abu guda.

Wannan shine link na video irin yadda muke ɓulatan a aikace.

WATCH VIDEO HERE (GOOGLE DRIVE)

______________________________________

In taƙaice muku de dalilin wannan illar da yai ma kansa da tsawon lokacin da ya dauka kafin zuwa ga likita rashin jinin dake circulation yasa tsokokin azzakarin sun lalace, ya gamu da Probable permanent Erectile dysfunction, Wato gabansa bazai kuma tashi ba koda yaji sha'awa ballantana ma sha'awar ita kanta ta taɓu. 

Abu daya ne ya rage shima sai in yana da gata ko hali shine; ai aiki asa masa penile implant "Wato dashen robobi cikin azzakari", robobi masu kamar rehu da inyaso jima'i zai riƙa matsatsu kamar irin yadda ake matsa robar jikin abun awon hawan jinin nan "spygmanometer" da ake matsawa yake qara tsamke hannu, inyaso in angama jima'in sai ya kwance kan robar iskar ta fita' gaban ya kwanta.

Saide ko shi wannan ɗin yana bukatar kusan Naira Milyan 5 zuwa 10 koda a Nigeria za ai aikin, kuma ba tabbas ma in anyi adace. Sannan ko andace bazade ka taɓa kwatantashi da natural erection ba.

Wannan shine yadda sauraron kowanne irin taci barkatai din shawarwari kan kai mutum ya barosa. Yanzu amaryar da shi yaso birgewa shin zata iya haƙuri ta rayu dashi ahaka kuwa? Wannan can zasu warware ta, amma da kamar wuya de kam. 

Don haka kamar yadda nake faɗa muji tsoron Allah, mu sani in wani fa yai rawa an watsa kudi wani inyai duka zai ci. Eh Mun yadda muna iya zamowa mutane baki daya... To amma fa ginin halittar jikin mu na kowa ya bambanta da juna, kamar yadda kakannin mu da kalar surar mu suka bambanta dana juna. 

Baka bukatar shan komi don kurum zakai Aure! Bai dace mu zamo birkitattu marasa lissafi ba. Ko zinace-zinace ka saba yi kake zaton kana da matsala yana da kyau ka fahimci jima'i da Macen da aure ne tsakaninku yasha bamban da wacce ita kuɗi ne tsakaninku. Ka lura da cin fruits, tsafta, wanka, wanki, shafa turare, iya magana, da kyautata mu'amala shikenan kurum. 

Duk wata matsala da zaka ga alamun kamar kana da ita a sanda kai sabon aure kurum ka kau da kai ka bata lokaci, ba matsala bace har sai kaga kun shafe watanni 6 cir batare da abin ya kau ba.... sannan ne zaka iya tabbatar da matsala, inba haka ba koda saurin inzali bai amsa cewa akwai sa har sai kai wata 6 kana jima'i batare da jin ka gamsu ba.

Amma daga lokacin da ya zamto kuna gamsuwa to ko minti 2 kake sunansa jima'i kuma lfy kake, ba sharadi bane duk jima'i sai an shafe tsawon mintoci masu yawa, ba yadda yake a finafinan Batsa ba yake a zahiri.

Kuma in kana tunanin matsala fara zuwa babban asibiti Urology center, Teaching hospital, FMC, ko Specialist hospital tukun kaga likita, bawai garzayawa ga masu magungunan gargajiya ko Islamic Chemist ba, asibiti ne matakin farko basai abu ya lalace ka doso mu ba.

Allah yasa saƙon ya isa.

Previous News Next News