Bincike: Asirin masu son raba kan Al’ummar Hausawa da Fulani ya fara Tonuwa

Munafukai

Sun ƙirƙiri shafi da sunan Fulani suna cin mutuncin Hausawa kuma sun ƙirƙiri shafuka da Hausa suna cin zarafin Fulani

A yau insha Allahu zan fara bayyana sunaye da fuskoki da akawun da lambobin wayar wasu daga cikinsu da shafukansu ta tashoshinsu. Ku yi haƙuri, rubutun zai ɗan yi tsayi.

Daga cikin hanyoyin da suka ɗauka don haddasa fitina a tsakanin Musulmi, sun raba aikin gida biyu. Fuska ɗaya tana yi da sunan kishin Hausa, ɗaya fuskar kuma da sunan kishin Fulatanci.

Sun buɗe shafuka biyu, ɗaya da sunan kishin Hausawa, kuma ba shi da aiki sai cin mutuncin Fulani da yi musu ƙazafi. 

Ɗayan kuma sun buɗe shi da sunan kishin Fulani, kuma ba shi da aiki sai cin mutuncin Hausawa da yi musu ƙazafi. Dukkan shafukan su na ƙirƙirar tarihin ƙarya da bai taɓa faruwa a wannan duniyar ba, masu sosa rai don su ruɗi mabiyansu.

 Da kuma umartar mabiyansu a kaikace da su tashi suyi tsayin daka wajen kawo ƙarshen junansu.

Ga shafukan guda biyu (na Hausawa da na Fulani):

__ An ƙirƙire shi a watan Yuli, 2021. An canza masa suna sau biyu.

__ Yana da Admin mutum biyu.

__ An ƙirƙire shi a watan Agusta, 2021 - wata guda bayan buɗe Gimbiyar Hausa. An canza masa suna sau ɗaya.

__ Yana da Admin mutum biyar.

Alaƙar da ke Tsakanin Shafukan Biyu

Da shafin da aka ce na Kishin Hausawa ne da kuma wanda aka ce na kishin Fulani ne, duka sun yi tarayya wajen bibiyar wasu shafuka na Kiristanci da kuma wasu ɗaiɗaikun mutane. 

Wannan wanne irin arashi ne? Ta yaya shafuka biyu masu yaƙi da juna suke yin tarayya wajen bibiyar wasu shafuka, da ɗaiɗaikun mutane?

Ga shafukan da shafuka biyun suka yi tarayya wajen bibiya:

 1.  Waazin Kalmar Yesu Almasihu 
 2. Shafiu M Bello
 3. Evang Danfulani Foundation
 4. Yesu Musulmi Ne 
 5. Basharu Altine Guyawa Isa 
 6. Jarumin Mazan Wakan Almasihu 
 7. Yesu ne Karfina 

Sai dai sun fara janye wa daga bibiyar wasu shafukan, cikin kwanakinnan, saboda sun gano muna bibiyar motsin su.

Mu ɗan yi Batu a kan Shafiu M Bello

Shi wannan mutumi mai Shafiu M Bello shafin Gimbiyar Hausa yana bibiyar sa, haka kuma shafin Voice of Fulani ma yana bibiyar sa. Shafiu M Bello dai sananne ne cikin masu kira kodayaushe zuwa rabuwar kai a tsakanin al'ummar Hausa da Fulani. Idan aka duba furofayil ɗinsa za a ga rubuce-rubucen da yake.

Ina so mu gane bambanci tsakanin kai kana bibiyar shafi da kuma shafin yana bibiyar ka. Ba kasafai shafi yake bibiyar mutum ba. Don haka wannan abu ne da ba saba gani ba.

 Musamman kuma har ayi arashin samun shafuka har biyu masu yaƙar jina suna bibiyar mutum ɗaya tilo, wanda ba ya daga cikin shahararrun al'umma.

Shi wannan mutumi kuma har yanzu, shi kaɗai ne a matsayin abokin a wani shafi Mai suna Kaltum Jitami, wanda muke kyautata zato cewa shi ne shafin matar da take amfani da sunan "Gimbiyar Hausa" ko "Jakadiyar Hausa" kuma ta buɗe wannan shafi da take da'awar haddasa fitina da zagi da yin ƙazafi ga Dan Fodio. 

Da Tuzurura mutane don su riƙa cin mutuncin duk wani Bafulatani, musamman shahararru irin su Dan Fodio da zuri'arsa, Sarakunan Arewa na Fulani, Muhammadu Sunusi, Sheikh Ɗahiru Bauchi, Sultan, Sheikh Pantami, Sheikh Lawan Trimph, Rabi'u Musa Kwankwaso, kamar yadda take ambatar sunayensu a cikin muryoyin da take yaɗawa a guruf guruf ɗin su na WhatsApp, shafukansu na facebook, tasharsu ta YouTube, da website ɗinsu.

A iya bincikenmu ga abubuwan da muka fahimta game da wannan mata:

 1.  Sunanta: Kaltoom Alumbe Jitami 
 2. Lambar wayarta: . Tana amfani da saƙandamin sunanta suna "KJ" a Whatsapp. Wato Kaltoom Jitami.
 3. Furofayil ɗin facebook ɗinta: https://www.facebook.com/kalthoom.jitami.5
 4. Website ɗinta: www.hausatoday.com kuma muna kyautata zato tana da alaƙa da shafin www.mutunci.com
 5. Fuskarta: binciken da muka yi ta hanyoyin intanet, wannan hoton da muka makala na mace mai ƙaramin hijabi, sanye da tabarau shi yake ta maimaituwa.
 6.  Asalinta: Jahar Jigawa
 7. Inda take zaune: ta yi zaman Sudan mai tsawo, amma yanzu tana Najeriya.

Tambayoyi:

 1. Me ya sa shafuka masu gaba da juna suke bin juna?
 2. Me ya sa shafuka masu gaba da suke bin wani mutum ɗaya mai suna Shafiu M Bello wanda shi kaɗai ne friend na akawun ɗin shugabar kira zuwa ga rabuwar kai? Menene alaƙarsa da su? - wataƙila idan wani ya tambaye shi zai ba da bayani.
 3. Me ya sa shafuka biyu masu gaba da juna suka yi tarayya wajen bibiyar shafuka iri ɗaya?
 4. Me ya sa duk shafukan suke da tsari iri ɗaya? Dukkansu ba su da aiki sai cin mutumci da ƙazafi ga ƙabilar da suke ikirari suna yaƙa. Za ka iya haɓɓaka wata ƙungiyar ƙabila ba tare da ka yi kira ga a muzanta wata ba.
 5. Me ya sa shafukan suka yi tarayya wajen sha'awar bibiyar shafukan da'awar Kiristanci? Duk da yake suna bibiyar wasu shafukan dabam.

Za mu ɗan tsaya saboda taƙaitawa.

Previous News Next News