Majalisar dokokin jihar Kogi ta wanke 'yan majalissu 9 daga zargin ta’addanci

Kogi House of Assembly
Kogi House of Assembly


Majalisar dokokin jihar Kogi ta wanke wasu ‘yan majalisa tara da ake zargi da alaka da ta’addanci tare da yi musu maraba da komawa majalisar.

Aranar 24 ga Maris 2023, Majalisar Dokokin Jihar ta sanar da dakatar da Olusola Kilani (Ijumu), Bello Hassan (Ajaokuta), Muhammed Lawi Ahmed (Okene I), Moses Akande (Ogori/Magongo), Aderonke Aro (Yagba West) , Daniyan Ranyi (Bassa), Atule Igbunu (Ibaji), Atachaji Musa (Idah) and Muktar Bajeh (Okehi).

Dakatar da su ya biyo bayan wata wasika da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya karanta a gidan, inda ya ce ‘yan majalisar sun aikata ta’addanci ne bisa rahotannin tsaro.

An wanke ‘yan majalisar ne a wata sanarwa da aka fitar a zauren majalisar dokokin jihar yayin zaman majalisar na ranar Laraba.

Ana sa ran mambobin za su ci gaba da aiki nan take.

A nasa jawabin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ijumu Kilani, ya bayyana jin dadinsa da cewa an wanke shi, yana mai cewa mutuncin sa na nan daram, kuma ba shi da wata matsala, kuma zai ci gaba da kokarin ganin jihar ta samu ci gaba mai dorewa.

Previous News Next News