Hanyoyin da za ka sa Masoyiyarka ta shaku da kai

Budurwa

Shin kana daga cikin jerin mazajen (samari da masu aure) da suke son ababen kaunarsu ko abokan zamansu su shaku da su?

In ko haka ne, to lallai kada ka wuce karatun malamin tsangayar tonga na yau.

Cikin sauki zaka iya mamaye zuciyar mace da wadannan abunuwan kamar haka:

Ka Zama Mai Saukin Kai

Mace tana saurin shakuwa da namiji mai saukin kai wanda bai nuna mata isa bare gadara.

Namijin da zata iya ce masa miko mini wannan ko dauko mini wancan cikin girmamawa kuma ya mata.

Mace yanzun na zata saki jiki da namiji muddin ta fahimci bai mata gyara cikin zafin kai ko kaskanci.

Shawara da Ita

Idan har kana shawara da mace musamman kan wasu abubuwan ka da basu shafeta ba. Nan da nan mace zata shaku da kai.

Ita mace a kullum tana son ganin namiji ya maidata mutum. Shigo da ita cikin shawaran ka tana budurwar ka ko matarka abune da yake sata taji tana matukar sonka da bata son rabuwa da kai.

Recommended Reading: Wasu Kalmomi Guda 12 Da Basu Dace Ki Furtawa Mijinki Su Ba

Yi kokarin ka rika shawara da matarka ko wacce zaka aura koda ba zaka yi amfani da shi ba. Ko kuma ba komai kake so ta sani ba. Kada ka watsar da ita can kamar mara amfani ko mara tunanin da za a iya shawartawa da ita.

Yawan Yaba Mata

Wani abu da namiji yake saurin shakuwa da mace shine ya yawaita yaba mata.

Idan tayi abun kwarai yaba mata. Idan tayi kuskure yi mata gyara cikin girmamawa. Idan tayi kwalliya nuna mata tafi duk wata mace kyau. Yaba takunta yadda take tafiya. Idan tayi girki ko ta miko maka ruwa yaba mata.

A duk lokacinda zata yiwa wani namijin da bai saba yaba mata ba wani abun, kawai kaine zaka fado mata a ranta.

Mata tamkar yara kananan suke. Idan Ka yabeta akan wani abunda tayi a yau, gobe so take ta maka wannan abun fiye dana jiya. Yana da kyau maza mu koyi yaba matayen mu idan sunyi bun kwarai domin yakan sa shakuwa ga masoya ko ma'aurata.

Bata Lokaci

Idan kana samun lokaci kuna zama da wacce zaka aura ko matar sa kake aure. Cikin sauki zaka makale mata a rai.

Samun lokacin zama ko hira da mace na sa a kullum tana bege da son mai mata hakan. Kada ka dauka yawan kiranta a waya ko sakonnin text zasu iya maye gurbin samun lokaci Ku zauna kuna hiran duniya.

Gamsar Da Ita

Akwai matan da sun gwammace zama ba aure idan suka rabu da mazansu ta mutuwar aure ko na fitar rai basu sake wani auren ba.

Akwai matan da suke auren maza basu duka amma suna manne dasu. Wasu ko abincin kirki basu samu amma ba isa a fadi aibun miji ba. Wannan duk ba komai ya jawo hakan ba sai yadda take samun gamsuwa daga wajen mijinta. Wanda a mahanganta babu wani na mijin da zai iya gamsar da ita idan ba shi ba. Don haka bazata yi gangacin rabuwa da shi ba.

Gamsar da mace shine abu mafi tasiri wajen shakuwa da mace.

Ga mazan da suke soyaya basu kai ga aure ba kuma. Iya zancenka da sanin lugga da kalmomin soyaya wajen yaba mace nasa mace ta shaku da kai.

Da fatan maza zasu rike wadannan darusan domin samun damar shakuwa da Masoyan su. 

Previous News Next News