Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Kwacen Waya a matsayin fashi da makami

Ganduje
Gov. Ganduje

Majalisar tsaro ta jihar Kano ta ayyana kwacen waya a matsayin fashi da makami, kuma duk wani mutum ko kungiyar da aka kama da aikata laifin makamancin hakan to za a yi masa hukunci ne daidai da na ‘dan fashi da makami.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida mai barin gado, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.

Majalisar karkashin jagorancin gwamna mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje a yayin zamanta, ta bayyana cewa kwacen waya a ‘yan kwanakin nan ya yi tsamari ya kuma kai makura don haka yana bukatar daukar tsauraran matakai.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa majalisar ta amince da samar da wata tawaga ta musamman a cikin tsarin tsaro domin tunkarar matsalolin da ke faruwa a jihar.

“Kwamishanan ya kara da cewa majalisar a yayin da take tattaunawa kan rantsar da sabon gwamnan ta ce an dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an gudanar da bukukuwan lami lafiya tare da gargadin cewa miyagu da za su yi amfani da wannan dama wajen haddasa tashin hankali da sunan biki da su guji yin hakan. ''in ji sanarwar.

"Ba za a amince da lalata kadarori na jama'a, mutum ko 'yan adawa ba saboda an dauki isassun matakan maganin duk wadanda suka zo da wannan dabi’a."

Ya ce a yayin taron, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada bukatar mika mulki cikin kwanciyar hankali a jihar, tare da yin kira da a gudanar da bikin lami lafiya. 

Ya godewa jami’an tsaro a jihar bisa dukkan hadin kan da suka ba shi a tsawon mulkin sa, ya kuma bukace su da su guji hasala cikin sauri.

Taron ya samu halartar kusan dukkan shugabannin hukumomin tsaro da sauran mambobin majalisar.

Previous News Next News