Yadda Zaka Rage Girman Tumbi Da Teba Cikin Sati Daya (Mace ko Namiji)

Rage Tumbi

To kamar yadda muka saba barkanku da zuwa wannan shafi namu na seeyblog, shafin dake kawo muku sabbin labarai, bayanai, fadakarwa, ilimantarwa, nishadantarwa da sauransu.

Yau da izini mai duka za mu yi bayani ne kan yadda mutum zai rage girman ciki ko ince tumbi ko na ce tebar ciki wanda mata da maza da dama na fama da wannan matsalar.

{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}

Na tabbata da dama suns ha gwada wasu hanyoyi mabanbanta amma hakan bai kawo musu komai ba, amma dai izin ubangiji wannan hamya mai sauki ce kuma ana samun waraka da yardar mai duka.

Kayan Hadin Maganin Da Zaku Nema

Kana /kina fama da tebar ciki to wannan ya kwana gidan sauki zaku iya dawowa madaidaita cikin kankanin lokaci da yardar mai sama.

 1. Farko mutum ya tanadi lemon coca-cola guda daya
 2. Sannan sai mutum ya nemi cocumber guda daya itama
 3. Ya kara neman ginger wacce take zuwa a roba din nan itama ya ajiye koda bata wuce cokali biyar ba haka
 4. Sannan sai mutum ya nemi lemon zaki guda daya wanda ya nuna sosai yayi yellow din nan
 5. Sannan sai mutum ya nemi lemon tsami ma anfi son mutum ya nemi me ruwa a lemon tsamin ma guda daya
 6. Bayan mutum ya nemi lemon tsami  Sannan sai mutum ya tanadi ruwa mai kyau ya adana a gefe

Sannan sai kuma bayanin yadda za'a hada wannan mahadai domin hada wannan maganin rage tumbi cikin sauki.

Bayan ka tanadi abinda ake bukata da na lissafo a sama sannan saiku karanta bayanin kasa domin hada naku maganin cikin sauki ba tare da wata shan wahala ba.

Za Ku So Duba: Maganin Karin Kiba na Bature Dana Gargajiya

Kasancewar gaskiya a wajen hadin wannan magani mutum dole sai ya nemi kofi guda biyu bayan wanda ya ajiye ruwan daya debo mai kyau

Babban kofin daka nema shine na hada maganin karamin kuma nashan maganin fatan kowa ya gane.

Yadda Ake Hada Maganin

 • Bayan ka tattara abubuwan da na lissafo a sama sannan sai karanta yadda ake hada shi wagga magani cikin sauki
 • Farko dai zaka samu wuka mai kaifi sannan wacce bata da datti wadda zata iya yanka lemo da cocumber
 • Bayan ka tanadi wukarka sannn saika dauko wannan babban kofin naka ka ajiyeshi gabanka, sannan saika dauko robar coca-cola din daka sayo ka budeshi a hankali
 • Sai ka kiyasta iya rabin lemon sannan ka tsiyaya rabin lemon cikin dogon kofin daka ajiye gabanka yake facing naka
 • Bayan ka zuba rabn lemon coca-cola din nan naka a cikin kofin saika maida murfin robar lemon ka rufe
 • Sannan sai ka dauko wannan cocumber din taka sai ka aunata dai dai gida biyu ko uku, yadda dai kaga zata isheka amma zaifi kyau ka rabata gida biyu ko kuma ka yanka yar madaidaiciya da wukar nan taka kayi mata yanka madaidaita yadda za'a iya cinyewa
 • Bayan ka yanka cocumber naka a cikin kofin ka sannan sai ka dauko ginger dinka ka samu cokali shima kamar nashan tea ko kayi diba biyu idan cokalin shan tea ne idan kuma babban coki ne sai kayi one spoon ka zuba a cikin kofin
 • Kaga kenan ka hada coca-cola da yankakkiyar cocumber da ginger a cikin kofin naka gaba daya yauwa muje zuwa
 • Sai ka dauko lemon zakin daka sayo sannan saika yankashi gida biyu yadda za'a iya matse rabin cikin sauki, sannan sai ka matse bari daya ko kuma rabin lemon daka yanka gida biyi na zakin daka siya
 • A takaice dai ka yanka lemin zaki gida biyu ka matse rabi a ciki sannan a ajiye rabi a gefe
 • Yauwa ina lemon tsamin daka siyo shima sai ka yanka shi gida biyu ka matse rabi cikin kofin naka bayan kayi haka sannan saimu karasa matakin karshe.

Bayani Gwari-gwari

Ga dai bayanin a takaice idan mutum bai gane bayanin sama ba, farko a nemi lemon coca-cola a rabashi biyi a juye a dogon kofi a samu ginger a zuba cokali daya sannan a samu cocumber a yanka rabi a cikin kofin, kana a nemi lemon zaki a yanka rabinsa a matse ruwan a ciki sannan sai a nemi lemon tsami shima a yankashi gida biyu a matse rabin sa a ciki a yayyanka bawon a cikin hadin.

Bayan ka hada wannan hadin sannan saika dan jijjigashi yayi mix sosai sannan saika dauko ruwan daka tanada saika zuba a cikin wannan kofin hade haden da kayi bayan ka zuba sai ka dada jijjiga kofin yadda hadin zai dada mix sosai.

Sannan sai ka dauko karamin kofinka ka tsiyayi hadin kashanye.

Amma fa badan dadi ba ake sha domin idan da don dadi akeshan maganin babu yadda za'ayi tebar mutum ta ragu.

Kana iya shan maganin sau biyu a rana ko sau daya a rana.

Sannan idan kaga hadin ya kare saika hada wani cikin kwanaki kalilan zaka nemi tebar dake jikinka kaga babu ita ubangiji ya yaye Maka

Sai ka koma dan motsa jiki, ga mata kuma sai suyi zamansu komai normal ne.

Fatan wannan yana da amfani ga kowa da kowa sannan wannan hadin na gaske ne babu karya cikinsa.

Fatan kowa ya gane.

Kammalawa

Na tsamo wannan sahihin maganin rage tumbi ne daga cikin acib din wani tsohon shafina wanda na wallafa a shekarar 2019. Ina fatan kun amfana da wannan magani kuma kun ji dadinsa.

Ina kuma so ku sani, kofa a bude take, za ku iya yin sharhi a kan wannan rubutu nawa.

Allah ka kara wa Annabi Daraja. 

Previous News Next News